08
Nov
Daga JAMEEL GULMA a Kebbi A cikin shirinta na yaƙi da cututtuka da ke yaɗuwa tsakanin jama'a, uwargidan gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir (Nasare) ta ƙaddamar da cibiyoyin gwaje-gwajen cututtukan hawan jini da ciwon siga ga marasa lafiya maza da mata marasa galihu a jihar Kebbi. An ƙaddamar da shirin a garin mai taken "Ka San Lambarka Kuma Ka Kiyaye" a Gwadangaji da ke ƙaramar hukumar mulki ta Birnin Kebbi inda Hajiya Zainab ta bayyana cewa ana hasashen yi wa mutane milliyan goma faɗin ƙasar nan. Da ta ke jawabi a madadin Uwargidan gwamnan Kebbi Hajiya Zainab, shugabar ma'aikatan…
