11
Nov
Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayar da umarnin yajin aikin sai baba ta gani a duk jihohin da har yanzu ba su fara aiwatar da sabon albashi ba, daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024. Wannan umarni yana cikin matsayar da ƙungiyar ta cimma a taron majalisar gudanarwa na ƙungiyar(NEC) da suka yi a ƙarshen mako. A cewar ƙungiyar, rashin bin doka da jinkirin aiwatar da sabon albashi ya zama abin damuwa ga ma’aikata da ke fama da tsadar rayuwa mai tsanani. Ƙungiyar ta NEC ta bayyana cewa, wannan gazawa da wasu gwamnatocin jihohi suka yi…
