Labarai

Yariman Saudiyya ya yi alƙawarin tallafa wa canjin da Tinubu ke yi a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Yariman Saudiyya kuma Firaministan ƙasar, Muhammad bin Salman bin Abdul'aziz Al Sa'ud ya tabbatar da cewa zai tallafa wa Nijeriya a ƙoƙarinta na gyare-gyaren harkokin tattali. Hakan na zuwa ne a lokacin da Yariman da Shugaba Bola Tinubu suka haɗu a Riyadh dake Saudiyya a yayin taron ƙasashen Musulmai Larabawa. Manyan ƙasashen biyu sun tattauna kan ɓangarorin haɗaka da suka haɗa da mai, gas, noma da ababen rayuwa da kuma samar da Majalisar Kasuwanci ta Saudi-Nijeraya wanda za a zuba aƙalla Dala biliyan 5. A shekarar 2022 ne kamfanin noma da kiwo na Saudiyya (SALIC) ya…
Read More

Dakarun tsaro sun tarfa Bello Turji a wata musayar wuta

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaro da mafarauta sun yi arangama da jagoran ƴan bindiga, Bello Turji a garin Gatawa dake ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato yayin da suka tarfa shi a bayan waɗansu duwatsu. A safiyar ranar Talata da misalin ƙarfe 6 na safe ne aka samu rahotonni da dama daga garin waɗanda suka ce an samu musayar wuta a tsakanin dakarun da ƴan bindiga. Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa, ƴan bindigar sun yi yunƙurin shiga garin ne inda sojoji da mafarauta suka dakatar da su. Ya ce, babu cikakken bayani game da sakamakon artabun, amma…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: An rantsar da Okpebholo na APC a matsayin sabon gwamnan Edo

Daga BELLO A. BABAJI An rantsar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Edo a wani yanayi na kafa tarihi, a Benin babban birnin jihar. An gudanar da taron rantsarwar ne a ranar Talata, a filin wasa na Samuel Ogbemudia dake cikin birnin. Hakan na zuwa ne watanni biyu bayan jam'iyyar APC ta lashe zaɓen gwamna a jihar. Okpebholo ya kama karagar mulki ne inda zai kasance tare da abokin tafiyarsa, wato Dennis Idahosa. Gwamna mai barin gado, Godwin Obaseki ya jagoranci jihar har sau biyu inda wa'adinsa na ƙarshe ya kare a yau, 12 ga watan Nuwamba, 2024.
Read More

Kisan ƙare dangi Isra’ila ke yi a Gaza – Yariman Saudiyya

Daga BELLO A. BABAJI Yariman ƙasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman ya yi alla-wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa a Gaza, inda ya kwatanta hakan da 'kisan kare dangi'. Ana ganin wannan dai shi ne suka mafi zafi da wani jami'in gwamnatin Saudiyya ya yi tun fara yaƙin na Gaza a shekarar da ta gabata. Da ya ke magana a taron ƙoli na ƙasashen Musulmai da Larabawa, Yariman ya soki Isra'ila kan hare-haren da ta kai a ƙasashen Lebanon da Iran. BBC Hausa ta ruwaito cewa, Isra'ilar ta musanta cewa dakarunta na aikata kisan ƙare dangi…
Read More

Tinubu ya nemi a samar da mafita ta difulomasiyya ga yaƙin Isra’ila da Palestine, inji Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi a samar da hanyoyin difulomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila da Palestine a taron haɗaka na ƙasashen Larabawa, a Riyadh da ke ƙasar Saudiyya. Ministan Labarai da Wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ya bayyana hakan wa manema labarai na Fadar shugaban ƙasa, a Riyadh. Ya ce, Shugaba Tinubu na neman a samu hanya ta lumana da bin tsarin difulomasiyya wajen dakatar da yaƙin da ke faruwa tsakanin ƙasashen biyu. Ministan, ya ce Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen yaƙin, ya na mai…
Read More
Yan ta’adda na neman sasanci da gwamnatin Katsina

Yan ta’adda na neman sasanci da gwamnatin Katsina

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ganin yadda jami'an tsaro suka zafafa hare hare a maɓoyan 'yan ta'adda a Jihar Katsina,yanzu yan ta'addan sun fara neman hanyar sasanci da gwamnatin jihar. Gwamnan Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a wajen bikin yaye jami'an community watch corps su 550 kashi na biyu da suka kammala samun horo a Katsina. "Jami'an tsaron sun kashe ɗaruruwan 'yan ta'addan da jagororin su, sauran da suka rage na neman sasanci da gwamnatin" inji gwamnan. Ya ƙara da cewa yanzu ɗaruruwan mutanen da 'yan bindigan suka sace an kuɓutar da su,da yanzu haka suna tare da…
Read More
Majalisar dokoki ta buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a garin Yashe da Daɗin Kowa

Majalisar dokoki ta buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a garin Yashe da Daɗin Kowa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar dokoki a jihar Katsina ta amince da ƙudurin tunatarwar na gina magudanun ruwa a mazabar Yashe a karamar hukumar Kusada, tare da gina gada a ƙauyen Daɗin Kowa a ƙaramar hukumar. Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kusada, Hon. Gali Garba ya gabatar da ƙudirin na tunatarwa ga ɓangaren zartarwa na gina magudanan ruwa a mazabar Yashe a ƙaramar hukumar Kusada. Ɗan majalisar ya bayyana cewa samar da wannan hanyoyin ruwa a garin zai taimaka wajen hana zaizayar ƙasa da garin yake fama dashi. Ƙudirin na biyu, ƙudiri ne da ɗan majalisa mai wakiltar…
Read More
Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa – da Musulmi a birnin Riyadh, Saudi Arabiya

Fassarar jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa – da Musulmi a birnin Riyadh, Saudi Arabiya

. 11 ga watan Nuwamba, 2024 Bari in fara da miƙa godiyata ga Mai Martaba Sarki Salman Bin Abdul-Aziz Al-Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu, da ya shirya wannan gagarumin taro. Tare da tsantsar girmama nauyin aiki da ya rataya akai na na tsaya a gabanku a yau yayin da muke ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin Falasɗinu da tabbatar da maslahar samar da ƙasashe biyu. Wannan manufar tana da matuƙar mahimmanci kuma al’amari ne na gaggawa. Rikicin Falasɗinu ya daɗe yana ci gaba da jawo wahalhalu marasa adadi ga mutane da dama. A matsayinmu na wakilan al'umma masu darajanta…
Read More

Ƙungiyoyin Islama sun shiga sahun masu nazari kan gyaran haraji

Daga BELLO A. BABAJI Wata tawagar haɗaka ta ƙungiyoyin addinin Islama ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar haɗin kan al'ummar musulmi (IFUU) ta shirya tattaunawa game da ƙudirorin gyaran haraji da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙirƙiro. A ranar Laraba ne za a gudanar da zaman inda tawagar ta ce tsarin gwamnati na neman kwaskwarima wa haraji abu ne da ke da buƙatar neman shawarwari daga masu-ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi da kuma al'umma kafin zartar da shi a matsayin doka. A ranar 3 ga watan Satumba ne Tinubu ya miƙa ƙudirorin neman gyaran haraji ga Majalisa domin dubawa. Cikin wani jawabi da ke…
Read More

Yadda gwamnan Zamfara ya inganta harkokin kiwon lafiya a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Biyo bayan taɓarɓarewar harkar kiwon lafiya a Zamfara a shekarun baya, Gwamna Dauda Lawal ya shelanta dokar ta-ɓaci a ɓangaren jim-kaɗan da kama mulki a jihar. A ƙoƙarinsa na inganta harkar lafiya, gwamnan ya fara ne a gyare-gyaren asibitoci da zamanantar da su da sanya kayayyakin aiki na zamani da kuma gina waɗansu asibitocin. Acikin shekara guda ne rashin kula da asibitocin suka yi fama da shi ya zama tarihi inda aka ƙawata gine-ginensu da samar musu da ƙwararrun ma'aikata don amfanin al'umma a jihar.
Read More