13
Nov
Wata tankar mai ɗauke da man fetur ta kama da wuta a kan iyakar Jigawa da Kano, lamarin da ya jefa tsoro a zukatan mutanen da ke wajen. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara ta tarayya a Jihar Jigawa, Aliyu M. A ya tabbatar da faruwar wannan lamari ga manema labarai a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamba, 2024. A cewar Aliyu, “A ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024, da misalin ƙarfe 10:43 na safe, hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa daga dagacin Kuho, Zubairu Ahmad, kan hatsarin tankar da ya faru a Tsaida, Kwanar Kalle, kusa…
