Labarai

An yi manyan sauye-sauyen muƙamai Kamfanin NNPCL

An yi manyan sauye-sauyen muƙamai Kamfanin NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya sanar da sauye-sauye ga hukumarsa da manyan jami’anta, tare da sauke Umar Ajiya da Oritsemeyiwa Eyesan daga muƙamansu na babban jami’in kuɗi. A madadinsu, NNPCL ya naɗa Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban zartarwa na Downstream da Udobong Ntia a matsayin EɓC (Upstream). Haka nan, Adedapo Segun, wanda ya kasance EVP (Downstream) an naɗa shi babban jami’in kuɗi. A cikin wata sanarwa da hukumar ta NNPC ta fitar a daren Larabar da ta gabata, ta ce naɗe-naɗen na da nufin inganta harkokin tafiyar da harkokin kamfanoni…
Read More
Tinubu ya naɗa hadimin Atiku a 2023 a matsayin mashawarcinsa kan sadarwa

Tinubu ya naɗa hadimin Atiku a 2023 a matsayin mashawarcinsa kan sadarwa

Daga USMAN KAROFI Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Daniel Bwala a matsayin mai ba shi Shawara na musamman kan harkokin watsa labarai da sadarwa na fadar gwamnati kamar yadda sanarwar da Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana. Bwala, wanda ya taba zama hadimi ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya goyi bayan Atikun a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda Atiku ya faɗi a hannun Tinubu. Bayan zaɓen, Bwala ya canza sheka zuwa ga goyon bayan Tinubu matakin da ya jawo cece-kuce dayawa. Onanuga ya kuma tabbatar da naɗa…
Read More

Sojojin sama sun hallaka ƴan bindiga 15 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi nasarar hallaka ƴan bindiga 15 a wani hari ta sama da ta kai wa dabar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Safana dake Jihar Katsina. Zagazola Makama, wanda masani ne kan aikace-aikacen ƴan ta'adda, ya ce sojojin sun ƙaddamar da harin ne a wata maɓoyar ƴan bindinga dake ƙauyen Tsaskiya. Makama ya kuma ce rundunar sojin 'Fansar Yamma' ce ta yi luguden wutar da nufin tarwatsa wasu manyan sansanonin ɓarayin daji dake yankin. Wasu bayanan sirrri daga majiyar sojin, ta bayyana cewa, "rundunar sojin sama ta samu nasarar hallaka…
Read More

Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun kiwon lafiya 14 kan rashin cika ƙa’idoji

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Makarantun kiwon lafiya 14 masu zaman kansu Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rufe su bisa rashin cika ƙa'idoji yayin da wasu 7 kuma aka umarci da su yi wasu gyare-gyare. An kuma bai wa wasu makarantu 8 izinin cigaba da aikin su. Mai bai wa gwamna shawara kan makarantun kiwon lafiya Hon. Umar Mamuda ya sanar da hakan a hira da manema labarai a ofishinsa. Ya ce wannan mataki da gwamnati ɗauka ya biyo bayan sakamakon da kwamitin binciken da gwamnatin ta kafa ya fitar ga harkokin gudanarwar waɗannan makarantu masu zaman kansu. Kwamitin…
Read More

Jami’an CWC sun kama jami’in kiwon lafiya mai yi wa ƴan ta’adda magani a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'an tsaron al'umma na community watch corps (CWC), sun kama wani malamin asibiti mai sun Rabe Mamman da laifin kula da lafiyar ƴan ta'adda a ƙaramar hukumar Batsari dake Jihar Katsina. A yayin wata hira da jami'an CWC da manema labarai, jami'in ya tabbatar da zargin da ake masa. Ya ce akwai lokacin da ya taɓa yi wa wani ƙasurgumin ɗan ta'adda mai suna Abu Raɗɗe magani a rauni da ya samu sakamakon artabu da ya yi da mutanen ƙauyen Kirtawa. "An taɓa kira na ƙauyen Baranda inda na yi wa shi babban ɗan bindiga,…
Read More
Jakadan Falasɗinawa ya buƙaci duniya ta tabbatar da kare haƙƙin bil’adama a Gaza

Jakadan Falasɗinawa ya buƙaci duniya ta tabbatar da kare haƙƙin bil’adama a Gaza

Daga USMAN KAROFI Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya bayyana damuwarsa kan cigaba da kashe-kashen da ake yi a Gaza tare da kiran a kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila. Yana mai cewa lokaci ya yi da ƙasashen duniya za su ɗauki matakin kawo ƙarshen “yunƙurin kisan ƙare dangi da kuma tsangwamar da aka daɗe ana yi wa al’ummar Falasɗinu. Bisa ƙididdigar da aka fitar a kan rikicin Gaza, fiye da kwanaki 405 na takurawa da kashe-kashen da Isra'ila ke yi tare da goyon bayan Amurka, mutane 43,603 na Falasɗinawa ne aka kashe, yayin da aka jikkata mutane 102,929…
Read More
Arewa za ta sake shiga duhu bayan ‘yan bindiga sun sake lalata tashar wuta a Kogi

Arewa za ta sake shiga duhu bayan ‘yan bindiga sun sake lalata tashar wuta a Kogi

Daga USMAN KAROFI Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya yi gargaɗin cewa ana iya fuskantar matsalar rashin wuta a ƙasar nan, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari tashar rarraba wuta a Obajana, Jihar Kogi. Babban manajan hulɗa da jama’a na TCN Ndidi Mbah, ta bayyana hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar , inda ta ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Talata. A cewar Mbah, rahotannin daga jami’an tsaro da ke wurin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, lamarin da ya sa jami’an…
Read More

Yadda ɗan majalisa ya baje miliyoyin nairori a gidansa duk da halin matsi da al’umma ke ciki

Daga BELLO A. BABAJI Wani ɗan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano mai suna Aliyu Sani Madaki ya janyo cecekuce acikin al'umma bayan da aka gansa cikin hotuna da bidiyo a ɗakinsa da wasu maƙudan kuɗaɗe a gabansa. Madaki, wanda ɗan jami'yyar NNPP ne da ke wakiltar mazaɓar Dala, an gan shi tare da wasu mutum biyu su na ƙirga kuɗaɗen waɗanda ana hasashen ba za su yi ƙasa da Naira miliyan 500 ba. Al'umma da dama musamman a halin matsin rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya na mamakin yadda ɗan majalisar ya mallaki tsabar kuɗi irin haka a…
Read More
‘Yan bindinga sun yi awon gaba da mutane sama da 30 bayan kashe wasu a Katsina

‘Yan bindinga sun yi awon gaba da mutane sama da 30 bayan kashe wasu a Katsina

' Daga UMAR GARBA a Katsina Wata dabar 'yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki a ƙauyukan Mai Ɗoriya da kuma Ɗan Alhaji a ƙaramar hukumar Batsari dake jihar Katsina. 'Yan bindingar sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu fiye da 30 a ƙauyukan biyu. Majiyarmmu ta bayyana cewa, an yi garkuwa da mutane 25 da suka haɗa da mata da ƙananan yara a unguwar Ɗan-Alhaji, yayin da wasu da dama suka samu raunukan harbin bindinga. A ƙauyen Maiɗoriya, ‘yan bindigar sun yi wa mutane biyu yankan rago tare da yin garkuwa da wasu mutum…
Read More

Nan ba da jimawa ba za mu gama da Lakurawa – Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen sabuwar kungiyar ƴan ta’adda ta Lakurawa a shiyyar Arewa-maso-Yamma nan ba da jimawa ba. Ribaɗu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen bikin babban taron Hukumar Kwastom na shekarar 2024 a ranar Laraba, a Abuja. Ribaɗu ya ce, "Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lakurawa daga ƙasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu. Boko Haram da suka addabi ƙasarmu a baya, yanzu…
Read More