15
Nov
Daga GAMBO ISAH Shugaban ƙungiyar NURTW a Tashar Kano da ke Maidugiri a Jihar Borno, Alhaji Ahmadu Yau, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridun Blueprint a Abuja, ya yaba da ɗimbin nasarorin da Maigirma Gwamnan Jihar Borno ya samu da kuma salon shugabanci a fannin gina hanyoyi, tsarin kiwon lafiya, samar da kayan aiki ga jami'an tsaron soji, 'yan sanda da JTF a dukkan ƙananan hukumomi 27 da ke faɗin jihar, da dai sauransu. Ahmadu Ya'u ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Zulum bisa jajircewarsa wajen ƙarfafa wa ’yan jihar da kuma mambobin ƙungiyarsa…
