Labarai

An fara kaɗa kuri’a a Amurka don zaɓen sabon shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI A yau Talata ne ake gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Amurka inda al'umma ke fatan samu sabon Shugaba tsakanin Donald Trump da Kamala Harris. Harris ita ce ƴar takarar jam'iyyar Democrats bayan da shugaban ƙasar, Joe Biden ya janye daga tsayawa takarar, wadda ta kasance mai neman a bada ƴancin zubar da ciki da neman a sauƙaƙe farashin kayan abincin da na gidaje ga ma'aikata. Trump kuma a nasa ɓangaren ya yi alƙawarin rufe kan iyaka da kuma rage kuɗin haraji da kaso mai tsoka. Tsohon shugaban ƙasar ya kuma tsallake harin mutuwa har sau biyu…
Read More

EFCC ta kama tsohon abokin takarar Atiku, Okowa kan zargin badaƙala

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da tsohon Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa kan zargin sauya akalar Naira Tiriliyon 1.3 daga asusun Gwamnatin Tarayya waɗanda ke wakiltar kaso 13 na kuɗin asusun daga 2015 zuwa 2023. A ranar Litinin ne aka kama tsohon gwamnan, a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas a lokacin da ya amsa gayyatar hukumar a offishinta dake birnin kan al'amarin. Ana zargin Okowa ne da ƙin bada asusun da aka ware don sanya kuɗaɗen, sannan da kuma wasu biliyan 40 na hannun jarin da ya mallaka a ɓangaren gas na 'UTM Floating Liquefied…
Read More
Dujiman Katsina ya jinjina wa hukumar Civil Defence a Katsina

Dujiman Katsina ya jinjina wa hukumar Civil Defence a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin hukumomin tsaron cikin gida na majalisar wakilai Hon Abdullahi Aliyu ya yabawa babban kwamanda na hukumar Civil Defence ta ƙasa Abubakar Audi bisa ƙoƙarin da yayi na sake fasalin hukumar. Ɗan majalisar wakilan ya yi wannan yabon ne a Katsina yayin da yake liƙa wa shugaban sashin koda ta kwana na hukumar a Katsina CS Jibiril Usman. Hon Abdullahi Aliyu kuma Dujiman Katsina ya ƙara bayyana cewa sabbin tsare tsare da kwamandan ya fito da shi zai taimaka gaya wajen kare muhimman kadarorin gwamnati da magance masu ma gwamnati zangon ƙasa. Ya kuma…
Read More
Kotu ta wanke tsohon Alƙalin Alƙalai na Nijeriya, Onnoghen

Kotu ta wanke tsohon Alƙalin Alƙalai na Nijeriya, Onnoghen

Daga USMAN KAROFI Kotun ɗaukaka ƙara ta wanke tsohon Alƙalin Alƙalai na Nijeriya, Justice Walter Onnoghen a kan tsige shi a kan muƙamin sa mai cike da cece-kuce a shekarar 2019. Shugaban ƙasa na wancan lokacin Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen ne kwanaki kaɗan kafin zaɓen 2019, inda Tanko Muhammad ya maye gurbin sa a matsayin muƙaddashi. Wannan lamari dai ya jawo cece-kuce inda ƙungiyar lauyoyin ƙasa a lokacin su kayi Allah wadai da lamarin. Lamarin ya ja hankali ne domin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan Onnoghen ya bayyana alƙalan da zasu jagoranci ƙararrakin zaɓen na wannan shekarar.…
Read More

Zanga-zanga: Tinubu ya umarci a gaggauta sakin yara marasa galihu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gaggauta sake baki ɗaya yaran da aka tsare waɗanda ke fuskantar hukuncin kotun kan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta. Wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, ya ce Shugaba Tinubu ya kuma umarci Ministan Jin-ƙai da ya tabbatar da bai wa yaran kulawar da ta dace. Ministan Labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan wa manema labarai a Fadar shugaban ƙasa dake Abuja. Shugaban ƙasar ya kuma ce a binciki baki ɗaya hukumomin da ke da hannu akan kamawa tsarewa da kuma binciken yaran, ya na…
Read More
Mazauna da masu sana’ar POS a Kano sun koka kan Ƙarancin Kuɗi

Mazauna da masu sana’ar POS a Kano sun koka kan Ƙarancin Kuɗi

Daga USMAN KAROFI Mazauna Kano da masu gudanar sana’ar POS sun koka kan Ƙarancin Kuɗi da ke addabar jihar, wanda ke shafar kasuwanci da rayuwar jama'a. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa matsalar Ƙarancin Kuɗi na ƙara tsananta, inda ake fuskantar barazana ga kasuwanci da rayuwar al'umma a kullum. Wani mazaunin Kano, Halliru Aƙilu, ya ce, “Wallahi, a yanzu akwai Ƙarancin Kuɗi sosai. Ni ban saba fita da kudi a hannu ba, abin da nake yi shi ne neman inda zan samu su idan na fita. Amma yanzu yana da wahala. Idan ka je wajen POS, sai ka samu ba…
Read More

Zamfara ta zama jiha mafi bunƙasa ta fuskar tara haraji

Daga BELLO A. BABAJI Jihar Zamfara ta zama wacce ke kan gaba a Nijeriya wajen tara haraji a bisa nazarin 'State's performance', bayan fitar da wani rahoton harajin jihohi da aka yi wa laƙabi da BudgIT's State of States Report 2024. Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa hauhawar da ɓangaren tara harajin jihar ya yi da kaso 240.44 ya faru ne sakamakon ƙin dogara da Kwamitin Kasafin Asusu na Ƙasa (FAAC) kaɗai da jihar ta yi. Rahoton, cikin nazarinsa na shekara, ya duba aikin harajin baki ɗaya jihohi 36 na Nijeriya, inda Zamfara daga mataki na 36…
Read More
Ma’aikatan  Abuja sun ajiye motocinsu sakamakon tashin farashin fetur

Ma’aikatan Abuja sun ajiye motocinsu sakamakon tashin farashin fetur

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Akasarain ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a Babban Birnin Tarayya Abuja sun fara tafiyar ƙafa ko bin motocin haya sakamakon tsananin tsadar man fetur, kamar yadda wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya gudanar ya nuna. Wasu ma’aikata da dama sun shaida wa NAN cewa, canja salon rayuwar na taimaka musu wajen shawo kan matsalar kuɗi, saboda albashinsu ba zai iya tafiya daidai da ƙarin kuɗin man fetur ba. Wata mata mai suna Elizabeth Ekwere, ma’aikaciyar gwamnati, ta ce ta daina amfani da motarta ne saboda maƙudan kuɗaɗen da take kashewa wajen saka man fetur, wanda…
Read More
Nijeriya na asarar Dala biliyan 26 duk shekara saboda ƙarancin lantarki

Nijeriya na asarar Dala biliyan 26 duk shekara saboda ƙarancin lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Nijeriya na asarar dala biliyan 26 a duk shekara sakamakon ƙarancin wutar lantarki.  Wannan na ƙunshe ne cikin wani sabon rahoton kasuwanci na Afirka da aka fitar.  Sai dai ya ce asarar ba ta shafi kuɗaɗen da ake kashewa kan na'urorin samar da wutar lantarki ba.  Rahoton ya ce 'yan kasuwa suna kashe kusan dala biliyan 22 a duk shekara kan fetur don magance tasirin ƙarancin wutar lantarki. Wannan yana ƙara taɓarɓara al'amura. Ya bayyana samar da wutar lantarki a matsayin babban ƙalubale ga harkokin kasuwanci a Nijeriya da ma nahiyar Afirka baki ɗaya. Rahoton na…
Read More