04
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Ƴar takarar kujerar shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris ta gabatar da yaƙin neman zaɓe a karo na ƙarshe, kwanaki uku kafin zaɓen ƙasar. Harris ta halarci wani shirin barƙonci ne na wani gidan telebijin a karon farko wanda an ɗauki shekaru da dama ana yi inda ƴan takarar shugaban ƙasa su kan shiga cikin shirin sakamakon shaharsa. Haka ma Tsohon shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Donald Trump ya kammala nasa yaƙin neman zaɓen inda tuni aka fara hasashen sakamakon zaɓen. A halin yanzu jihohi bakwai ne ake ganin fafatawa za ta yi ƙarfi tsakanin…
