02
Nov
Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda ta ce duk wanda ya haura shekara 7 ya cancanci a maka shi kotu. Kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi ya faɗi hakan a ranar Juma'a yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels' inda ya bayyana hukuncin doka da ya bada damar kai wanda ya haura shekara bakwai kotu tare da bin hanyoyin da dokar ta tsara. Kakakin ya bayyana hakan ne yayin da ake tsaka da cecekuce game da batun kama wasu yara da ake zargin su da hannu a laifukan haddasa tashin-tashina a lokacin da aka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a…
