02
Nov
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce za a daina samun dogayen layuka a gidajen mai muddin dillalan mai suka fara sayen mai a matatarsa. Dangote ya bayyana haka ne bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a ranar Talata. Hamshaƙin attajirin na Afrika ya kuma buaaci babban kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL, da kuma ’yan kasuwa a faɗin ƙasar da su daina shigo da mai daga waje. Ya ƙara da cewa, matatarsa ita ce mafita ga batun dogayen layuka da ake samu a gidajen mai da ke faɗin ƙasar. "Kiyasin da na yi…
