02
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan daba da ake nema ruwa a jallo mai suna Inuwa Zakari wanda aka fi sani da Gundura. Wata sanarwa da mai magana da yawun 'yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kuma samu nasarar kama wasu ɓata-gari 14 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a samamen da suka yi ranakun 25 da 27 ga watan Oktoba. Kiyawa ya ce ɗan daban ya addabi al'ummar ƙwaryar birnin Kano saboda irin laifuka da yake aikatawa. "Ya kuma…
