Labarai

Manchester United ta tabbatar da Amorim a matsayin sabon kocinta

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da naɗa Ruben Amorim a matsayin sabon mai horar da ƴan wasanta maza gabannin kammala cike ƙa'idar shiga ƙasa. Manchester United ta bayyana haka ne ta kafofinta na sada zumunta a ranar Juma'a, 1 ga watan Oktoba, 2024. Ta ce, zai kasance tare da ita har zuwa watan Yunin 2027 da zaɓin tsawaita zamansa na shekara ɗaya. Da zarar ya kammala sauke nauyin da ke kansa na ƙungiyar da ya ke wa aiki a yanzu, zai je Manchester United a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Read More

An tashi a zaman Gwamnatin Tarayya da ma’aikatan jami’o’i ba a cimma matsaya ba

Daga BELLO A. BABAJI Zaman da aka gudanar tsakanin Gwamnatin Tarayya da kwamitin haɗaka na ƙungiyoyin jami'o'i (NASU da SSANU) a ranar Alhamis ya ƙare ba tare an cimma matsaya ba. Tsohon Ƙaramin Ministan Ilimi, Dakta Yusuf Sununu ya jagoranci zaman a Ma'aikatar Ilimi wanda an shirya shi ne don tattauna batun yajin aikin da ƙungiyoyin ke yi. Babban Sakataren Ma'aikatar, Nasir Gwarzo na daga cikin wanɗanda suka halarci zaman. A ranar Litinin ne ƙungiyoyin suka shiga yajin aiki mara iyaka sakamakon albashinsu na watanni huɗu da aka riƙe, wanda a saboda haka ne harkokin jami'o'i suka ja baya a…
Read More

Ya kamata manema labarai su fahimci shirin Tinubu ga Nijeriya – Ministan Labarai

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Labarai, Mohammed Idris ya ce gwamnati da gidajen jaridu ba abokanan hamayya bane face takwarori ga harkokin gina ƙasa. Ministan ya faɗi haka ne a lokacin da hukumar gudanarwa ta jaridar Guardian ta kai masa ziyara ofishinsa a ranar Alhamis. Ya ce, samar da ci-gaba wa ƙasa aiki ne na kama-kama tsakanin ɓangarori, ya na mai cewa a matsayin ƴan jarida na masu lura da lamuran al'umma, akwai buƙatar su ƙara ƙaimi wajen kare martabar demokraɗiyyar Nijeriya da tabbatar da haɗin-kai da zaman lafiya acikin al'umma waɗanda za su su taimaka wajen samun riba wa…
Read More

Tinubu ya gaji ayyukan titina 2,000 yayin da ya soke 10 – Ministan Ayyuka

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi ya ce aƙalla ayyuka 2,000 da ba a kammala ba gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gada, waɗanda ke zuƙar Tiriliyoyin nairori daga asusun ƙasa. Ministan ya ce Ma'aikatarsu ba ta shakkar ɗaukar manyan matakan inda a halin yanzu an soke kwangiloli goma na wasu kamfanoni. Mista Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani zama da masu-ruwa-da-tsaki Jihar Ondo kan haɗe wani ɓangare na babbar hanya mai tsawon kilomita 63 ta Legas zuwa Calabar. Ya ce, samun Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaba, kyauta ce ga al'ummar Nijeriya, ya…
Read More

Majalisar Zartarwa ta nemi a janye ƙudirin neman yi wa haraji kwaskwarima

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Zartarwa kan Tattali (NEC) ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ta nemi a janye ƙudirin da ke neman yi wa haraji kwaskwarima, wanda aka gabatar a Majalisa. Acikin mambobin NEC akwai gwamnoni inda ɗaya daga cikin su wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Oyo, Sheyi Makinde ya bayyana wa manema labarai cewa an samu cecekuce ne kan ƙudirin wanda hakan ya sa suka ga dacewar a janye shi tare da sanya masu-ruwa-da-tsaki acikin lamarin. Hakan na zuwa ne yayin ake tafka muhawara kan harajin VAT wanda a mafiya yawancin jihohin Arewacin Nijeriya da ake…
Read More
Ya kamata a rarraba hanyar wutar lantarki – Shettima

Ya kamata a rarraba hanyar wutar lantarki – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana buƙatar raba hanyar samar da wutar lantarki a Nijeriya don magance matsalar rushewar rumbun lantarki ta ƙasa da ake fama da ita. A taron majalisar tattalin Alarziki ta Ƙasa karo na 145 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Shettima ya yi bayani kan matakan da za a ɗauka wajen raba hanyoyin samar da wutar, wanda ya haɗa da samar da ƙananan hanyoyin samar da wuta da kuma amfani da makamashi mai sabuntawa kamar hasken rana. Ya kuma jaddada buƙatar gaggawa wajen aiwatar da tsarin ayyukan makamashi na Nijeriya (NESIP),…
Read More

Akwai waɗanda suka tara biliyan N9 don haddasa tarzoma lokacin zanga-zanga – ‘Yan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Kakakin rundunar ƴan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya ce kimanin Naira biliyan 9 aka tara don haddasa tashin-tashina a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta. Adejobi ya bayyana hakan ne a yayin taron 'Civil Space Guard' da aka gudanar a Cibiyar aikin jaridar zurfafa bincike ta Wole Soyinka (WSCIJ) da haɗin-gwiwar Masarautar ƙasar Netherlands. An gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwar ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024, wanda al'ummomin jihohin Nijeriya da dama suka tsunduma aciki. An gudanar da zanga-zangar a kudancin Nijeriya cikin lumana yayin da lamarin a…
Read More

Majalisar Dattawa ta fara binciken zagon-ƙasa ga fannin fetur a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattijai ta shirya ƙwarya-ƙwaryar kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin yin zagon-ƙasa wa ɓangaren man fetur a Nijeriya. Mataimakin shugaban Majalisar, Barau Jibrin ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar bayan da shugaban kwamitin, Opeyemi Bamidele ya ɗauki nauyin ƙudirin wanda ke neman Majalisar da ta Wakilai da su gudanar da binciken ɓangaren man. Shugaban kwamitin ya ce Majalisar Wakilai ta gudanar muhawara akan batun wanda ita ma ta shirya kwamitin da zai yi bincike akan lamarin. Ya kuma nemi su haɗa hannu tare da sanya wa kwamitin suna kwamitin haɗin-gwiwa na…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 25 ne suka samu tallafin gwamnati na N25,000

‘Yan Nijeriya miliyan 25 ne suka samu tallafin gwamnati na N25,000

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ’yan Nijeriya miliyan 25 sun karɓi tallafin kuɗi na ₦25,000 da aka keɓe don rage raɗaɗin talauci. Ministan Kuɗi kuma Mlministan tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai bayan taron majalisar tattalin arziki ta Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta. Edun ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ɗaukar matakan tallafa wa ’yan Najeriya don rage wa mutane raɗaɗin da cire tallafin man fetur da wasu tsare-tsaren gwamnati ke haifarwa. A cewarsa, iyalai miliyan biyar ne suka amfana daga wannan shirin kai…
Read More
Uwargidan Gwamnan Kebbi ta ƙaddamar da cibiyar maganin ciwon Tari a Argungu 

Uwargidan Gwamnan Kebbi ta ƙaddamar da cibiyar maganin ciwon Tari a Argungu 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Uwargidan gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir ta buɗe wata cibiya don bayar da maganin ciwon tarin TB kyauta a garin Argungu. Da ta ke buɗe cibiyar a wani sashe na babbar asibitin garin Argungu, Hajiya Zainab Nasir ta bayyana cewa yanzu an samo maganin ciwon tarin TB mai inganci ba kamar irin waɗanda cutar ke bijirewa ba.  Ana rasa rayuka da dama sanadiyyar ciwon da ake iya magancewa saboda halin ko-oho da mutanen da ke ɗauke da cututtukan ke nunawa wanda da sun dage da shan magani za su iya warkewa. Ta ƙara da…
Read More