01
Nov
Daga JAMEEL GULMA a Kebbi Bayanai daga yankin ƙaramar Hukumar mulki ta Danko/Wasagu da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa waɗansu mahara sun yi awon gaba da kimanin mutane goma sha shida daga garin Bena da kuma waɗansu ƙauyuka da ke kusa da garin ranar Talatar da ta gabata. Malam Lauwali Umar, Sakataren kwamitin tsaro na ƙaramar hukumar mulkin me ya bayyana haka ranar Laraba kwana ɗaya da faruwar lamarin. Ya ce waɗansu mutane ɗauke da makamai da ake sa ran masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne suka kaiwa manoma farmaki yayin da su ke aiki a…
