01
Nov
Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta cafke wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Nuhu Haruna daga ƙaramar Hukumar Dutsinma bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa. Kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina ASP Abubakar Sadiƙ ne ya gabatar da yaron a gaban manema labarai tare da wasu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai a jihar. Kakakin rundunar, wanda ya gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar ya bayyana cewa, an kama Haruna ne biyo bayan wata hatsaniya da suka yi da abokiyar zaman mahaifiyarsa Rabi Haruna…
