30
Oct
Daga ABDULLAHIMUHAMMAD a Katsina Jami'ar Gwamnatin Tarayya FUDMA da ke Dutsinma a Jihar Katsina zata yi bikin yaye ɗalibai a karo na tara inda za ta karrama uwargidan shugaban ƙasa da wasu fitattun mutane su uku. Mataimakin jami'ar Farfesa Armaya'u Hamisu Bichi ya faɗi haka a hira da manema labarai da yayi a ɗakin taro na jami'ar. Yace uwargidan shugaban ƙasan ta taka rawar gani wajen ilimin ɗalibai mata a jami'ar. Farfesa Bichi ya bayyana cewa a lokacin da ƴan bindiga suka sace wasu ɗalibai mata na jami'ar, ta taka rawa gaya wajen kuɓutar da su . "Bayan kuɓutar da…
