30
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sandan Jihar Imo sun yi nasarar kama wata ƴar shekara 17 mai suna Jesse Chidiebere wadda ɗaliba ce a Jami'ar jihar, IMSU wacce ta yi ƙaryar garkuwa da kuma mutuwa. Henry Okoye, wanda shi ne Kakakin rundunar ƴan sandan, ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa sun samu rahoton zargin ɓacewar yarinyar a ranar Asabar da ta gabata. Chidiebere ta bayyana wani saƙo ta wattsapp da ke nuna cewa an yi garkuwa da ita kuma an kashe ta wanda hakan ya sa iyalanta suka garzaya ofishin ƴan sandan don isar da rahoto. Daga nan…
