29
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce za a gyara wutar lantarkin da ta lalace a jihohi 17 na Arewacin Nijeriya sakamakon tsaiko da aka samu a tashar lantarki na Shiroro-Kaduna. Ministan Wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bada tabbacin hakan wa manema labarai jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a Fadar shugaban ƙasa. Ya ce an samu ɗaukewar lantarki ne Arewa sakamakon lalacewa da tashar ta Shiroro-Kaduna ta yi wadda ita ce babbar tashar da ke samar wa yankin wutar lantarki. Adelabu ya ce za a ɗauki tsawon kwanaki uku zuwa biyar ana gyara ta don…
