Labarai

Gwamnonin Arewa sun gana da shugaban tsaro da sarakunan gargajiya kan lamarin rashin wuta da matsalar tsaro

Gwamnonin Arewa sun gana da shugaban tsaro da sarakunan gargajiya kan lamarin rashin wuta da matsalar tsaro

Gwamnonin Jihohin Arewa 19 sun gana da sarakunan gargajiya a Kaduna a ranar Litinin, don tattaunawa kan muhimman batutuwa da suka shafi yankin Arewa. Wannan taron, wanda ya zama wani ɓangare na ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin jihohin arewa don shiga tattaunawa da masu ruwa da tsaki, yana mai da hankali kan matsalolin tsaro, talauci, yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, da sauran ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin. Wannan ganawar, wadda Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya jagoranta kuma Gwamna Uba Sani na Kaduna ya karɓi baƙunci a gidan gwamnatin Kaduna, Sir Kashim Ibrahim House, ta samu halartar gwamnonin…
Read More

Kotu ta ɗage ƙarar PDP tsagin Mustapha Inuwa zuwa watam gobe a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Babban Kotun Tarayya a Jihar Katsina, ƙarƙashin Mai shari'a Abbas Bawale, ta ɗage ƙarar da PDP ɓangaren Mustapha Inuwa ya shigar wanda ke ƙalubalantar zaɓen shugabannin jam'iyyar da tsagin Sanata Lado Ɗanmarke ya gudanar a jihar. Lauya da ke tsaya wa ɓangaren Lado Ɗanmarke, Mista Isaac Nwachukwu ya ƙalubalanci hurumin kotun na sauraren ƙara da bangaren Mustapha Inuwa ya shigar. Ya ce, duk ƙorafe-ƙorafen su akan zaɓen fidda gwani ne na jam'iyyar ba zaɓen shugabanni wanda harka ce ta jam'iyya. A ɗaya ɓangaren kuma, lauyan su Mustapha Inuwa, Mustapha shiru Mahuta, ya nemi kotun da…
Read More
BIDIYO: Zan iya ɓatar da kai, wani ɗan majalisa yayin taƙaddama da direban Uber

BIDIYO: Zan iya ɓatar da kai, wani ɗan majalisa yayin taƙaddama da direban Uber

Wani ɗan majalisar Wakilai, Alex Mascot Ikwechegh, ya bayyana a cikin wani bidiyo yana cin zarafin direban Uber a gidansa da ke Maitama, Abuja. Ikwechegh, wanda ke wakiltar Aba ta Arewa da Kudu a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam'iyyar APGA, ya aikata wannan abin a lokacin da direban ya kawo wani saƙo amma ya ƙi shiga cikin gidan, ya nemi Ikwechegh ya fito ya karɓi kayan da kansa. A cikin bidiyon, ana iya ganin Ikwechegh ya fusata da faɗa da direban tare da yin barazana ga shi. Yana cewa, “Ka yi tunanin wannan ɓera, zan iya sa ɓatar da mutum…
Read More
Manchester United ta kori Erik ten Hag

Manchester United ta kori Erik ten Hag

Daga USMAN KAROFI Ta tabbata Manchester United ta kori Erik ten Hag a matsayin mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United. An naɗa shi a watan Afrilu na 2022, kuma ya taimaka wa ƙungiyar wajen lashe kofuna biyu na gida, wanda suka haɗa da Carabao Cup a shekarar 2023 da kuma FA Cup a shekarar 2024. Ƙungiyar ta bayyana godiyarta ga Erik bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake tare da su, tare da yi masa fatan alheri a nan gaba. Ruud van Nistelrooy zai ja ragamar ƙungiyar a matsayin mai horarwa na riƙon ƙwarya, tare…
Read More
Rayuwa na ƙara tsananta yayin da aka shiga kwanaki da yawa babu lantarki a Arewa

Rayuwa na ƙara tsananta yayin da aka shiga kwanaki da yawa babu lantarki a Arewa

Daga USMAN KAROFI Yankin Arewa na Nijeriya ya shiga rana ta takwas ba tare da wutar lantarki ba, wanda hakan ya haifar da cikas mai tsanani ga ayyukan yau da kullum da rayuwar jama’a. Rashin wutar ya samo asali ne daga matsalar wutar 330kV da ke tsakanin Benue da Enugu, da kuma layin Shiroro da Kaduna, wanda ya jefa yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da kuma wani sashi na Arewa maso Tsakiya cikin duhu. Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa layin wutar 330kV DC Ugwaji-Apir ya samu matsala, wanda ya jefa yankin Arewa gaba…
Read More
NASU da SSANU sun shiga yajin aikin sai baba ta gani

NASU da SSANU sun shiga yajin aikin sai baba ta gani

Kwamitin haɗin gwiwa, JAC, na ƙungiyoyin ma’aikatan da ba na koyarwa a jami’o’in, wanda ya haɗa da ƙungiyar ma’aikatan ilimi da haɗin gwiwa, NASU da ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya( SSANU) ta umurci mambobinta da su fara taron ƙasa baki ɗaya domin yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin kan rashin biyan albashin watanni huɗu da aka hana. A cewar shugabannin ƙungiyoyin biyu sun fara yajin aikin ne a daren Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024. Ƙungiyoyin dai na neman a biya su albashin watanni huɗu da aka hana su, a ƙara musu alawus alawus da kuma aiwatar da yarjejeniyar…
Read More

Za a gurfanar da sojan da ya kashe abokin aikinsa a kotun sojoji

Daga BELLO A. BABAJI Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce wani jami'in sojan ruwa da ke aiki a sansanin jami'an atisayen FANSAN YAMMA a yankin Ɗan-Sadau ya yi ta harbe-harbe wanda a sanadiyyar haka ne ya kashe ɗaya daga cikin abokanan aikinsa. Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 3 na yamma a ƙaramar hukumar Ɗan-Sadau dake Jihar Katsina. Ya ce, an kama jami'in mai suna L Seaman Akila A. inda aka karɓe masa bindiga da kuma tsare…
Read More

Daga ƙarshe Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan Ministar Jinƙai da aka dakatar

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da aka yi wa ministocin shugaban ƙasa garambawul a kwanaki kaɗan da suka gabata, Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya tabbatar da tsige Ministar Jinƙai, Betta Edu daga muƙaminta. Kakakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels', inda ya ce an maye gurbinta ne da wani ɗan Filato. Ya ce, Edu ba ta da gurbi yanzu acikin ministocin Shugaba Tinubu, ya na mai cewa ta yiwa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati (EFCC) ne ta bada bayanai akan ta da ke tabbatar da rashin…
Read More

Ka ja kunnen Wike ko mu ƙone tashoshin man Neja-Delta – Mayaƙan yankin ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar mayaƙan Nija-Delta sun yi barazanar ƙone tashoshin man da ke yankin matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya gaza ɗaukar mataki akan Ministan Abuja, Nyesom Wike. Mayaƙan sun yi gargaɗin ne kan zargin Wike da yunƙurin ƙasƙanta gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas. Kakakin ƙungiyar, Justin Alabraba ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar wa manema labarai a inda ƙungiyar ta nuna fushinta kan zargin Wike da shirya maƙarƙashiya wajen yin amfani da kusancinsa ga allƙalin da zai yin hukunci kan ƙararsu da Fubara game da kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar a ranar Litinin. Alabraba…
Read More

Gwanjon jirgi Tinubu ya saya, ba sabo ba – Fadar shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce mai gidansa, Shugaba Bola Tinubu bai sayi sabon jirgi mai tashin angulu ba, a madadin haka, wanda aka yi gwanjonsa ne ya saya. Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata hira da gidan talabijin na 'channels', inda ya ce jirgin ba na Shugaba Tinubu bane, amma kadara ce ta ƴan Nijeriya. Ya ce akwai jiragen da ke cikin mummunan yanayi da ba za a iya aiki da su ba wa Shugaba Tinubu saboda tsufa da suka yi da kuma tsadar kula da su da ake yi,…
Read More