Labarai

NNPC da Chevron sun gano sabon rijiyar mai a Neja-Delta

NNPC da Chevron sun gano sabon rijiyar mai a Neja-Delta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanonin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, da Kamfanin Chevron sun yi wani gagarumin aikin gano sabon wurin ɗanyen mai kusa da rijiyar haƙar mai ta Meji NW-1 a yankin Neja Delta ta yamma. Yankin, wanda a ka canja kwanan nan zuwa PIA 2021, wani muhimmin yanki ne mai albarkatun mai a Nijeriya. Hakan zai kara inganta harkokin makamashi a Nijeriya da farfaɗo da tattalin arziki. Babban manajan kamfanin Chevron, Olusoga Oduselu shi ya tabbatar da haka a ranar Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024. Oduselu ya ce sun samu nasarar da haɗin gwiwar kamfanin NNPCL kan…
Read More
Nijeriya ta yi alƙawarin samar da tsarin guje wa yawan katsewar lantarki

Nijeriya ta yi alƙawarin samar da tsarin guje wa yawan katsewar lantarki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN), ya yi alƙawarin samar da tsarin ajiyar wuta don tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na su riƙa zama cikin duhu ba a duk lokacin da babban layin lantarki ya katse. Manajan Daraktan TCN, Sule Abdulaziz, ne ya bayyana wannan shirin na wata hira a gudan talbiji na Channels. Ya zargi tsofaffin ababen more rayuwa da suka kai shekaru 50 da faruwar rugujewar wutar lantarki a ƙasar. Abdulaziz ya ci gaba da cewa, “A yanzu haka muna ɓullo da wani tsari, kuma Bankin Duniya ne ke ɗaukar nauyinsa, kuma aikin zai…
Read More
Mutumin da ke yi wa ’yan sanda sojan-gona ya shiga hannu a Kano

Mutumin da ke yi wa ’yan sanda sojan-gona ya shiga hannu a Kano

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wani mutum da ke yin sojan-gona inda yake cutar al'umma. Mai magana da yawun rundunar a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. SP Abdullahi ya ce an kama mutumin bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga mazauna Fagge da Sabon Gari da Koki da kuma kwaryar birnin Kano, inda suka ce mutumin yana amfani da matsayin jami'in ɗan sanda wajen karɓar kuɗaɗe a hannunsu. "Mun kama mutumin ne mai suna Salisu Bala mai shekara 31 ranar 14 ga watan Oktoba a Kurna ƙaurters…
Read More
An kashe ɗan sanda a rikincin ’yan acaɓa a Legas

An kashe ɗan sanda a rikincin ’yan acaɓa a Legas

An kashe wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda rikicinsu da ’yan acaɓa a safiyar Asabar a yankin Agege da ke Jihar Legas. ’Yan sanda sun ɗora laifin kisan a kan wasu ’yan acaɓa da ake zargin muna da hannu a lamarin. Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba ya jagoranci tawagar ’yan sanda ne zuwa wajen da wani hatsari ya auku a mahaɗar WEMCO a yankin Agege. Rahotanni sun ce ’yan sandan sun je ne domin su cire wata motar dakon kaya da ta buge wani ɗan acaɓa, amma sauran ’yan acaɓar suka yi musu tirjiya, inda suka yi ƙoƙarin ƙone…
Read More
Yadda ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa a Sakkwato

Yadda ɗan shekara 18 ya sace ɗan makwabcinsa a Sakkwato

Rundunar ’yan sanda reshen jihar Sokoto, ta cafke wani ɗan ƙungiyar masu garkuwa da mutane, inda ta cafke babban wanda ake zargi, ɗan shekara 18, Abba Aliyu, wanda makwabci ya shigar da ƙara daga unguwar Badon Hanya a jihar Sokoto. Wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Ahmed Rufa’i ya raba wa manema labarai a jihar a ranar Asabar, ta ce a ranar 16 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 1200 na safe, Ibrahim Shehu ya kai rahoto ga sashin yaƙi da garkuwa da mutane da ke sashin binciken manyan laifuka na Sakkwato, inda ya ce ɗansa, Saidu…
Read More
Adadin fetur ɗin da ake sha ya ragu da kashi 92 a ƙarƙashin mulkin Tinubu – Rahoto

Adadin fetur ɗin da ake sha ya ragu da kashi 92 a ƙarƙashin mulkin Tinubu – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Amfani da man fetur na yau da kullum a Nijeriya ya ragu matuƙa bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. Bayanan da gidan Talabijin na Channels ya samu daga Hukumar Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), ɓangaren adadin manyan motocin da ake fitarwa, ya nuna cewa yawan amfani da mai ya ragu ya zuwa ranar 20 ga Agusta, 2024, wanda ya kai lita miliyan 4.5 a kowace rana. Yawan man fetur na yau da kullum kamar na Mayu 2023 ya kasance lita miliyan 60,000 a kowace…
Read More
Nijeriya ta fi kowace ƙasa matsalar wutar lantarki a duniya – Adesina

Nijeriya ta fi kowace ƙasa matsalar wutar lantarki a duniya – Adesina

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwunmi Adesina, ya bayyana cewa NIjeriya ce ta fi kowacce ƙasa yawan al’ummar da ke fama da rashin wutar lantarki a duniya. Adeshina ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekaru 90 na tsohon shugaban ƙasa, Janar Yakubu Gowon. Ya bayyana cewa kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 86 ne ba su da wutar lantarki, lamarin da ya sanya ƙasar ta zama kan gaba a duniya a wannan fanni. Adeshina ya kuma ƙara jaddada cewa rashin ingantaccen wutar lantarki na gurgunta harkokin kasuwanci da masana’antu a faɗin ƙasar nan. “Hukumar IMF ta…
Read More
’Yan Nijeriya sun fi samun sauƙin lantarki kan sauran ƙasashen Afirka – TCN

’Yan Nijeriya sun fi samun sauƙin lantarki kan sauran ƙasashen Afirka – TCN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamfanin Kula da Raba Wutar Lantarki a Nijeriya, wato TCN, ya bayyana cewa, duk da ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan, har yanzu farashin lantarki a Nijeriya ya fi sauƙi a kan wasu ƙasashe makwabta na Afirka. Manajan Daraktan TCN, Sule Abdulaziz, ne ya bayyana hakan a wani shiri na Sunday Politics a gidan talbiji na Channels. Ya ce, ‘yan Nijeriya na ƙara biyan kuɗin wutar lantarki saboda samar da wutar lantarki ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ‘yan ƙasar da ke rukunin Band A a yanzu suna samun wutar lantarki…
Read More
Tinubu na shirin saka harajin kashi biyar kan caca, wasanni da sadarwa

Tinubu na shirin saka harajin kashi biyar kan caca, wasanni da sadarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta gabatar da ƙudurin saka harajin kashi biyar cikin ɗari a kan ayyukan sadarwa, wasanni da caca a matsayin wani sabon ƙudiri na yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya. Wannan shawara, wacce ke ƙunshe a cikin “Dokar Harajin Nijeriya,” na da nufin sanya harajin kan ayyuka daban-daban a faɗin ƙasar. Kudirin mai taken; "ƙudirin dokar da zai daidai wasu dokoki kan haraji da kuma daidaita tsare-tsare na shari'a da suka shafi haraji da kuma kafa dokar harajin Nijeriya don samar da harajin kuɗaɗen shiga," wanda aka samu…
Read More
Duk da rashin wuta, kamfanin lantarki na Kaduna ya buƙaci a biya kuɗin wuta

Duk da rashin wuta, kamfanin lantarki na Kaduna ya buƙaci a biya kuɗin wuta

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna, KAEDCO, ya buƙaci mutane da su biya kuɗin wuta duk da tsawon lokacin da aka ɗauka babu wutar lantarki a Arewa. Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa an samu katsewar wutar lantarki a Kaduna, Katsina, Kano da Jigawa sakamakon lalacewar turakun lantarki a layin 330KV na Shiroro zuwa Kaduna da kuma matsalar layin Ugwuaji zuwa Makurɗi. Wannan lalacewar ya bar jihohin da abin ya shafa cikin duhu na tsawon kwanaki. Amma cikin wata sanarwa da babban jami'in hulɗa da jama’a na kamfanin, Abdulazeez Abdullahi, ya fitar, kamfanin ya buƙaci abokan cinikin sa da su biya…
Read More