Labarai

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin tantance kwasa-kwasai a cibiyoyin koyar da kiwon lafiya

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin tantance kwasa-kwasai a cibiyoyin koyar da kiwon lafiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta kafa kwamiti da zai binciki cibiyoyin koyar da kiwon lafiya domin gano kwasa-kwasai da ake koyarwa ba tare da izini ba. Da yake jawabi bayan ya ƙaddamar da kwamitin, mataimakin gwamnan jihar Faruk Lawal Joɓe yace wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan ƙorafe ƙorafe da al'ummar jihar suka yi ne akan tsarin koyarwa na cibiyoyin. "Saboda ƙorafe ƙorafe da juma'a su kai tayi akan irin kwasa-kwasai da cibiyoyin koyar da kiwon lafiya suka yi gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa wannan kwamiti domin a sami daidaito da buƙatun al'ummar…
Read More
Kada a jefa rayuwar Shettima cikin haɗari, yana buƙatar sabon jirgi – Kakakin Majalisar Borno

Kada a jefa rayuwar Shettima cikin haɗari, yana buƙatar sabon jirgi – Kakakin Majalisar Borno

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, ya bayyana damuwa kan rayuwar Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, yana cikin haɗari saboda matsaloli da jirgin mataimakin shugaban ƙasan ke fuskanta. Lawan ya yi wannan magana ne bayan da Shettima ya soke tafiyarsa zuwa taron Ƙolin Commonwealth a Samoa, sakamakon wani abu da ya bugi jirgin nasa a filin jirgin JFK a birnin New York, Amurka. Lawan ya bayyana cewa jirgin da ake amfani da shi wajen wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na fama da matsaloli, kuma hakan na iya jefa rayuwar Mataimakin Shugaban Ƙasa cikin haɗari. Ya yi kira…
Read More

TCN ya yi ƙarin haske game da ɗaukewar lantarki a Arewa

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce yana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA) don gyara tashar lantarkin Shiroro-Kaduna wanda ya haddasa raguwar wuta a jihohin Kaduna, Kano da ma wasu manyan biranen Arewa. Cikin wata takarda da Janar-Manaja na hulɗa da jama'a na TCN, Ndidi Mbah ya fitar, ya ce kamfanin na aiki tuƙuru wajen ganin dawo da raba isasshen lantarki duk da ƙalubalen tsaro da yankin ke fuskanta. Rahotonni sun bayyana cewa, wutar yankin ta samu tsaiko ne sakamakon lalata ta da ƴan ta'adda…
Read More

KANSIEC ta bai wa sababbin ciyamomin Kano shaidar shiga ofis

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe ta Kano, KANSIEC ta damƙa wa sabbin ciyamomin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar shaidar kama aiki bayan kwana ɗaya da kammala zaɓe. Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi shi ya jagoranci taron bada shaidar a yayin tabbatar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin, ya na mai kira a gare su tare da kansiloli da su cika ayyukansu yadda ake buƙata don amfanin yankunansu. Rahotonni sun bayyana cewa, nan ba da jimawa ba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da su a gidan gwamnatin jihar. Jam'iyyar NNPP ce ta lashe kujerun duka ciyamomi 44 na jihar…
Read More

Zaɓen ƙananan hukumomi: NNPP ta lashe duka kujerun ciyamomi da kansiloli a Kano

Daga BELLO A. BABAJI An sanar da jam'iyya mai mulki a Jihar Kano, NNPP a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaɓen duka ciyamomi 44 na ƙananan hukumomin jihar da duka kujerun kansiloli 484 da aka kammala a yau. Shugaban Hukumar zaɓe ta jihar (KANSIEC), Farfesa Sani Lawal Malumfashi ya sanar da hakan wa manema labarai a hedikwatar KANSIEC a birnin Kano. Farfesa Malumfashi ya bayyana zaɓen a matsayin wanda aka yi shi cikin lumana wanda ke tattare da gaskiya da adalci inda ya ce babu kujera ɗaya da sauran jam'iyyu 18 da suka fafafa suka samu. Duk da yunƙurin…
Read More

Yanzu-yanzu: Ruftawar gini ta rutsa da sama da mutane 40 a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Kimanin mutane 40 ne ruftawar wani gini ya rutsa da su a yankin Sabon Lugbe da ke Abuja. Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar. A halin yanzu al'umma na cike da alhini game da iftila'in yayin da jami'an gaggawa suka garzaya wajen da abin ya faru don bada agaji ga mutane da dukiyoyinsu. Sauran bayani zai I daga baya.
Read More

Birtaniya ta bai wa sojojin Nijeriya kyautar kayan aiki na Naira biliyan ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Birtaniya ta bai wa sojojin Nijeriya kyautar kayan aiki na zamani da adadinsu ya kai Naira biliyan ɗaya don ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin rundunar sojin ƙasar da na Nijeriya. Cikin wani saƙo da Babbar Hukumar Birtaniya ta fitar a Abuja ranar Juma'a, ta ce tallafin kayan aikin zai tai wa yaƙin da sojojin su ke yi da ƴan ta'adda a yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya. Haka kuma an bada tallafin ne a lokacin da wasu daga cikin sojojin Birtaniya ke gudana da wani karatu da musamman kan ƙwarewa a aikin soja waɗanda a halin yanzu su…
Read More
Ministan tsaro ya roƙi sojoji su kawo ƙarshen rashin tsaro

Ministan tsaro ya roƙi sojoji su kawo ƙarshen rashin tsaro

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi kira ga rundunar sojan sama ta Najeriya da ta ƙara ƙoƙari wajen mamaye sararin samaniya da kawo ƙarshen rashin tsaro a Nijeriya, musamman a yankin Arewa maso Yamma, yana cewa, “Don Allah, ku kawo ƙarshen rashin tsaro yanzu.” Da yake ziyarar hedkwatar rundunar sojan sama ta 213 Forward Operating Base a Jihar Katsina, Ministan ya bayyana cewa, “Muna tura ƙarin kayan aiki, ciki har da jiragen helikwafta na yaki da na’urorin jirgi marasa matuƙa domin ƙara inganta iya aikinku da kawar da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda. Shugaban ƙasa yana farin ciki da…
Read More
Hedikwatar tsaro ta tsare wani sojan ruwa da laifin kashe abokin aikinsa

Hedikwatar tsaro ta tsare wani sojan ruwa da laifin kashe abokin aikinsa

Daga USMAN KAROFI Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar da kama da kuma ƙwace makami tare da tsare wani jami'in sojan ruwa, LS Akila A, wanda aka tura FOB Dansadua don Operation FANSAN YAMMA, bisa zargin buɗe wuta tare da kashe abokin aikinsa na soja a wani yanayi mai tattare da shakku. Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan ayyukan watsa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya gabatar ga manema labarai a Abuja. Sanarwar ta ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin. Janar Buba ya tabbatar da cewa bayan kammala binciken, za a…
Read More
Irin rawar da Amurka ta taka wajen sakin shugaban Binance da ke tsare a Nijeriya

Irin rawar da Amurka ta taka wajen sakin shugaban Binance da ke tsare a Nijeriya

A ranar Alhamis, Amurka ta tura jirgi ɗauke da kayan jinya da jami'an sojoji guda shida domin ɗauko Tigran Gambaryan, babban jami'in kamfanin Binance Holdings Limited, daga Nijeriya. A cewar jaridar The New York Times, Gambaryan ya bar Nijeriya bayan Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar safarar kuɗaɗe da ta shigar a kansa. A baya, wannan jarida ta ruwaito cewa a ranar Laraba, Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar safarar kuɗaɗe da aka shigar a kan Gambaryan, wanda aka tsare, sakamakon matsalar lafiyarsa da kuma shiga tsakani ta diflomasiyya. An tsare Gambaryan tun watan Fabrairu sakamakon ɗaukar matakin gwamnati kan kamfanin saboda…
Read More