Labarai

CAF ta ci tarar Libya, ta ba wa Nijeriya maki uku a wasan neman gurbin AFCON

CAF ta ci tarar Libya, ta ba wa Nijeriya maki uku a wasan neman gurbin AFCON

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta baiwa Nijeriya maki uku da ƙwallaye uku bayan rashin nasarar da aka samu kan wasan zagaye na huɗu na gasar cancantar shiga AFCON 2025 da aka shirya tsakanin Nijeriya da Libiya a ranar 15 ga Oktoba a Benina. A hukuncin da ta yanke ranar Asabar, wanda shugaban hukumar, Ousmane Kane ya sanya wa hannu, hukumar ta yanke hukunci kamar haka: 1) An same hukumar ƙwallon ƙafa ta Libiya da karya dokar 31 na gasar cin kofin Afrika tare da dokoki na 82 da 151 na Kundin hukuncin CAF. 2) An ayyana wasan No.…
Read More

Zaɓen ƙananan hukumomi: Mazauna Kano sun kiyaye dokar taƙaita zirga-zirga

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake cigaba da gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi, al'umma a Kano suna ƙoƙarin kiyaye dokar taƙaita zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka don tabbatar da an kammala su cikin lumana. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan da Babbar Kotun kasar jihar ta bai wa Hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaɓen tare da rushe yunƙurin wasu jam'iyyu na dakatar da shi. Mai Shari'a, Sanusi Ma'aji wanda shi ya yi hukunci kan batun, ya ce KANSIEC ta na da damar gudanar da zaɓe a baki ɗaya ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano. Da farko…
Read More
Ana ta Allah wadai da kuma kiran tsagaita wuta bayan Isra’ila ta kai hari Iran

Ana ta Allah wadai da kuma kiran tsagaita wuta bayan Isra’ila ta kai hari Iran

Daga USMAN KAROFI A ranar Asabar, sojojin Isra'ila sun kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Iran da ke yankuna kamar Ilam, Khuzestan, da Tehran, inda aka auna wurare kusan 20 a cikin sa’o’i kadan. Iran ta tabbatar da mutuwar sojojinta biyu, tare da bayyana cewa harin ya haifar da ƙaramin ɓarna kawai. Wannan harin ya zama wani babban ci mataki a tsakanin rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu. Kakakin sojin Isra'ila, Daniel Hagari, ya ce Isra'ila ta kammala wannan aikin nata kuma ta shirya kare kanta idan Iran ta mayar da martani. A nasa ɓangaren, Hedikwatar Tsaron Sama ta Iran…
Read More
Dalilan da suka sa Matawalle ya tsira da kujerarsa duk da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

Dalilan da suka sa Matawalle ya tsira da kujerarsa duk da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci

An bayyana dalilan da suka sa Shugaba Bola Tinubu ya sauke ministoci biyar, amma ya bar Ministan Tsaro Bello Matawalle, duk da zarge-zargen goyon bayan 'yan bindiga da ake masa. Ministocin da aka cire sun haɗa da Uju-Ken Ohanenye (harkokin mata), Lola Ade-John (yawon buɗe ido), Prof. Tahir Mamman (Ilimi), Dr Jamila Bio Ibrahim (matasa), da Abdullahi Gwarzo (gidaje). Mai ba shugaban ƙasa shawara, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sauya ministocin ya biyo bayan yadda jama’a ke kallon yadda suka yi aiki da kuma bayanai kan tasirinsu. Wata majiya daga APC ta ce rashin tasiri a siyasarsu a jahohin da…
Read More

Gwamnatin Katsina ta ƙaddamar da kwamitin aiwatar da N70,000 Mafi ƙarancin albashi a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta ɗauki matakin ƙarshe na aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar ta hanyar ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa mai ƙarfi. Mataimakin gwamnan jihar, Faruk Lawal joɓe wanda ya wakilci Gwamna Dikko Raɗɗa, ya ƙaddamar da kwamitin ne a Gidan Gwamnatin jihar, a ranar Juma'a. Kwamitin, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari ke shugabanta, an ba shi wa’adin makonni uku don ya miƙa cikakken rahotonsa kan tsarin aiwatar da sabon albashin. Aikin kwamitin ya haɗa da dukkan rukunan mai'aikatan gwamnatin jihar, ƙananan hukumomi, da hukumomin…
Read More

‘Yan Legas miliyan 8.67 ke fama da hawa jini – Gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Legas ta ce akwai kimanin mutane miliyan 8.67 mazauna jihar ne ke rayuwa da hawan jini, yayin da ta ke shirin ƙaddamar da shirin gwajin cutar na kyauta a faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana hakan wa manema labarai a ranar Juma'a a lokacin da ya ke sanar da batun shirin gwajin cutukan hawan jini da na suga da za a yi kyauta a jihar. Kwamishinan ya ce akwai aƙalla mutane miliyan 3.48 da ke fama da cutar yawan ƙiba da kuma wasu miliyan 1.78 da ke fama da cutar…
Read More

Bayan shekaru tara, Jonathan ya yi tsokaci game da faɗuwarsa a zaɓen 2015

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi tsokaci game da faɗuwarsa zaɓen shekarar 2015, inda ya bayyana hakan a matsayin lokaci mai tsanani ga harkar siyasarsa. Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana irin yadda zuciyarsa ta kaɗu a lokacin da ji sakamakon zaɓen kasancewar ya na ji kamar baki ɗaya duniyar na ƙin sa ne. Jonathan ya faɗi hakan ne a Abuja yayin Lekcar tunawa da Raymond Dokpesi wanda Hukumar gudanarwa ta Daar Communications ta shirya tare da haɗin-gwiwar Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Ƙasa. Jonathan ya tsaya takarar shugaban ƙasa ne…
Read More

Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya na son a riƙa shirya finafinan da za su janyo hankalin masu zuba jar

i Daga BELLO A. BABAJI Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), Dakta Shua'ibu Husseini ya shawarci jagororin shirya finafinai a Nijeriya su ke samar da waɗanda za su ke janyo hankalin masu zuba hannun-jari don ci-gaban masana'antar. Daraktan ya yi kiran ne a lokacin da ya ke gabatar da wani jawabi a taron ƙara wa juna sani da masana'antar Kannywood ta shirya a ranar Laraba, a Kano. Ya ce, duk da cewa masana'antar fim a Nijeriya na samun ci-gaba, akwai buƙatar ake samar da finafinai masu ma'ana da za su taimaka wajen yin nasara a kasuwancin masana'antun finafinai.…
Read More

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnatin Kano ta taƙaita zirga-zirga

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a Kano a yau, gwamnatin jihar ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 12 na daren ranar Juma'a zuwa ƙarfe 6 na yammacin Asabar don kammala shi cikin lumana. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Baba Halilu Ɗantiye ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan da aka shawarci hukumomin tsaro. Ana gudanar da zaɓen ne a gundumomi 484 na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar. An kuma ɗaga kafa ga waɗanda ke ayyuka na…
Read More
Wata kotu ta kori duka ‘yan takarar ciyamomin NNPP a Kano

Wata kotu ta kori duka ‘yan takarar ciyamomin NNPP a Kano

Daga USMAN KAROFI Babbar kotun tarayya da ke Kano ta rushe dukkan ‘yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli 44 na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar. Mai shari’a Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙarar da Injiniya Muhammad Babayo da wani ɓangare na NNPP suka shigar kan shugabancin jam'iyyar. Alƙalin kotun ya umurci hukumar zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC) da ta amince da sabon jerin sunayen ‘yan takarar da ɓangaren shugaban jam'iyyar na jiha da aka amince da shi, Dalhatu Shehu Usman, ya gabatar,…
Read More