26
Oct
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar man Dangote ta fara dakon ɗanyen mai daga kamfanin mai na ƙasa NNPCL, ƙarƙashin yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a naira, kamar yadda jami’an matatar man da gwamnatin tarayya suka tabbatar a ranar Talata. An tattaro cewa an fara jigilar ɗanyen man zuwa matatar a cikin makonni uku da suka gabata lokacin da gwamnati ta fara sayar da ɗanyen man ga matatun ƙasar a cikin kuɗin ƙasar. Wata majiya mai cikakken bayani game da cinikin ɗanyen mai a cikin gida ta shaida wa manema labarai cewa, matatar ta na jiran karɓar ƙarin ɗanyen man fetur…
