Labarai

Fashewar tankar mai: Mutane 181 sun mutu, 80 na kwance a asibiti, Gwamnan Jigawa ya faɗa wa Tinubu

Fashewar tankar mai: Mutane 181 sun mutu, 80 na kwance a asibiti, Gwamnan Jigawa ya faɗa wa Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana cewa kimanin mutane 181 ne suka mutu sakamakon fashewar wata tankar mai da ta afku a jihar a makon jiya. Ya ce yayin da mutane 80 ke kwance a asibitoci, jimillar iyalai 210 ne abin ya rutsa da su a ranar 15 ga Oktoba. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata. Wata motar dakon mai daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe, ta fashe a Majia, dake ƙaramar hukumar Taura a jihar Jigawa. Da yake…
Read More
Matatar Ɗangote ta fara sayar da mai ga ‘yan kasuwa kai tsaye

Matatar Ɗangote ta fara sayar da mai ga ‘yan kasuwa kai tsaye

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Matatar man Ɗangote ta fara samar da man fetur ga wasu ‘yan kasuwar mai kaitsaye ba tare da neman wani kamfanin man fetur na ƙasa ba. An tattaro cewa, yayin da ƙarin ‘yan kasuwar man ke ƙara zage damtse wajen siyan kayayyakin kaitsaye daga masana’antar, wasu kuma na shigo da kayayyakin, domin ɗaruruwan miliyoyin litar man fetur da ake shigowa da su ya kamata su shiga gabar ruwan Nijeriya nan da makonni biyu. Ku tuna cewa jaridar ta ruwaito a ranar Litinin cewa aƙalla jiragen ruwa huɗu ɗauke da man fetur da aka shigo…
Read More
Zargin kwartanci: Hisbah na neman Kwamishinan Jigawa ruwa a jallo

Zargin kwartanci: Hisbah na neman Kwamishinan Jigawa ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta ayyana Kwamishinan Harkoki na Musamman na Jihar Jigawa da aka dakatar, Auwal ɗanladi Sankara, a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo. Shugaban Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne, ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi tsammanin Sankara zai amsa kiran fa hukumar ta yi masa, amma ya ƙi. Saboda rashin halartar kiran, Hisbah ta ayyana shi a matsayin wanda ta ke nema. Daurawa, ya ce hukumar ta bayar da belin Kwamishinan ne bisa wasu sharuɗa. “Aikinmu a Hisbah shi ne yin sulhu. Idan sulhu ya…
Read More
Gwamnatin Nasarawa za ta fara tantance ‘yan fanshon jihar

Gwamnatin Nasarawa za ta fara tantance ‘yan fanshon jihar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu haka hukuma dake kula da harkokin ‘yan fansho a Jihar Nasarawa wato Nasarawa State Pension Bureau a Turance dake birnin Lafiya babbar fadar jihar ta kammala dukkanin shirye-shirye don fara tantace da biyan sama da ‘yan fansho a jihar 1000 wasu basussukan su bayan gwamnatin jihar ta sake ware kimanin zuzuruntun kuɗi sama da biliyan 1 don raba wa ‘yan fanshon ɗin waɗanda suka cancanta a ba su a rabon kuɗin na bana. Babban darakta janar na hukumar Alhaji Suleiman Musa Nagogo ne ya sanar da haka a lokacin da yake tattaunaws…
Read More
An kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai a Yobe

An kama ’yar shekara 54 kan safarar makamai a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan sanda sun kama wata mata mai shekeru 54 kan zargin ta da fasaƙwaurin harsashi guda 350 a Jihar Yobe. Rundunar ’yan sandan jihar na zargin matar ne safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba daga garin Buni Yadi zuwa Damaturu. Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce dubun matar ta cika ne a Damaturu bayan  samun bayanan sirri a kan ayyukanta. “An kama wata mota ƙirar Golf 3 kuma bayan bincike an gano harsasai guda 350 samfurin 7.62ɗ39mm a ɓoye a cikin kayan wadda ake zargin. “A halin yanzu ana yi mata tambayoyi domin…
Read More
Farouk Lawan da ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyar a gidan yari

Farouk Lawan da ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekara biyar a gidan yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon ɗan majalisar wakilai, Farouk Lawan, wanda aka yanke wa hukunci saboda samunsa da laifin cin hanci da rashawa ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe shekaru biyar a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja. Tsohon ɗan majalisar ya wakilci Bagwai/Shannon a majalisar wakilai daga Kano a shekarun 1999 to 2015. A cikin wani jawabi da ya sanya wa hannu a ranar Talata, Lawan, ya bayyana cewa Allah ya yi masa fitowa bayan kammala wa’adin da kotu ta ɗibar masa tare da miƙa godiyarsa ga Allah bisa samun damar buɗe sabon shafi a…
Read More
Ribar Naira biliyan ɗaya gwamnati ta samu daga NAGIS kawo yanzu – Gwamna Sule

Ribar Naira biliyan ɗaya gwamnati ta samu daga NAGIS kawo yanzu – Gwamna Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya  Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya ce kawo yanzu tun da ya hau karagar mulki a matsayin gwamnan jihar daga shekarar 2019 zuwa 2024 da ake ciki gwamnatinsa ta ci ribar sama da zunzurutun kuɗi har Naira biliyan 1 daga hukumar nan dake tattara bayyanan filaye da sauran kaddarorin al’ummar jihar wadda ake kira Nasarawa Geographic Information System NAGIS a Turance. Gwamnan ya sanar da haka ne a jawabinsa a wajen bikin sake buɗe babban ofishin hukumar ta NAGIS wadda ya ci wuta sakamakon wani gobara da ya auku kwanakin baya a babban…
Read More
Muna amfana da kyawawan ayyuka daga jagoranmu Rabiu Kwankwaso – Bombay Gama

Muna amfana da kyawawan ayyuka daga jagoranmu Rabiu Kwankwaso – Bombay Gama

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jagoran Kwankwasiyya na mazaɓar Gama a ƙaramar Hukumar Nassarawa, Hon. Muhammad Adamu da aka fi sani da Bombay Gama ya bayyana cewa suna matuƙar murna da alfahari da zagayowar ranar haihuwar jagoransu na Kwankwasiyya na duniya, babban jagoran NNPP Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso bisa cikarsa shekaru 68 da haihuwa. Ya ce sun gode wa Allah da ya ba su dama suke biyayya ga tsarin tafiyar siyasa ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da har yau ɗin nan basa nadama akan hakan saboda ɗorasu da yake yi akan Gwadabe na daidai da aƙida ta kyakkyawar siyasa…
Read More
Ɗan takarar Kansila a Fagge ya yaba da gudunmawar da Gwamna Abba ya ba ‘yan kasuwar Kantin Kwari

Ɗan takarar Kansila a Fagge ya yaba da gudunmawar da Gwamna Abba ya ba ‘yan kasuwar Kantin Kwari

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Ɗan takarar Kansila a mazaɓar Fagge C  dake ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Sanusi Sharif Kantoma ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tallafin kuɗi da ya  bai wa 'yan kasuwar Kantin Kwari sakamakon gobara da suka yi. Ya ce ziyarar tausayawa da alhini da jaje da tallafin da gwamnan ya yi ga 'yan kasuwar ya nuna irin tausayi da kulawa da yake ga al'ummar sa duk lokacinsa wani abu ya samesu. Ɗan takarar Kansilan na mazaɓar Fagge C a ƙarƙashin jam'iyyar NNPP ya yabawa al'ummar ƙaramar hukumar bisa goyon baya ga…
Read More
Sama da gine-gine 500 ne suka ruguje a Nijeriya – NIA

Sama da gine-gine 500 ne suka ruguje a Nijeriya – NIA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Cibiyar Nazarin Gine-gine ta Nijeriya (NIA) a ranar Juma'a ta ce, sama da gine-gine 500 ne suka ruguje a ƙasar bana. Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da shugaban hukuma ta NIA, Arc Adeniyi Mobilaji ya bayyana cewa, rushewar gine-gine da ake cigaba da samu a ƙasar da ma duniya bakiɗaya ya yi ƙamari. Duk da haka suna nuna buƙatar tsauraran ƙa'idojin gini da aiwatar da su don hana wannan barazanar cigaba da hauhawa. Sun bayyana hakan ne a yayin taron masu zanen gine-gine na 2024 da aka gudanar a Abakaliki, babban birnin jihar…
Read More