Labarai

Ɗangote ya janye ƙarar biliyoyin Naira 100 kan wasu manyan kamfanonin mai

Ɗangote ya janye ƙarar biliyoyin Naira 100 kan wasu manyan kamfanonin mai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani al’amari mai ban mamaki, rukunin kamfanin mai na Ɗangote ya ce zai janye ƙarar da ta kai Naira Biliyan 100 da Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ke yi kan bayar da lasisin shigo da man fetur ga Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), kamfanin Man Fetur na Matriɗ, AA Rano, da wasu kamfanoni huɗu duk da samar da albarkatun mai a cikin gida. A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar a yammacin ranar Litinin, ya ce ƙarar da aka shigar a babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta fara gyaran babban titin Abuja zuwa Kano cikin gaggawa

Gwamnatin Tarayya ta fara gyaran babban titin Abuja zuwa Kano cikin gaggawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Ayyuka,  Nweze David Umahi, ya ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna. Da yake jawabi a wajen taron, Ministan ya bayyana cewa aikin titin ya kasu kashi uku: Abuja zuwa Kaduna (Sashe na ɗaya), Kaduna zuwA Zariya (Sashe na biyu) da Zariya zuwa Kano (Sashe na uku). Sashen Zaria zuwa Kano, an kammala shi sosai da sauran kimanin kilomita 17 kuma kwanan nan an faɗaɗa shi da kimanin kilomita 5.3 zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Kano tare da fitulu masu amfani da hasken rana. Kamfanin BUA ne ke kula da wannan.…
Read More
Boko Haram za ta iya amfani da yaran da ba sa zuwa makaranta – Obasanjo

Boko Haram za ta iya amfani da yaran da ba sa zuwa makaranta – Obasanjo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta a ƙasar, na da matuƙar haɗari ga al'ummar ƙasar nan gaba. Ya ce, sama da yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya za su iya tsunduma cikin ayyuka Boko Haram da ’yan bindiga cikin shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa. Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a Bauchi ranar Lahadi a wurin bikin Aaddamar da wasu zaɓaɓɓun ayyuka da Gwamna Bala Mohammed ya aiwatar. "Bankin Duniya ya ce muna da yara sama da miliyan 20 da ya kamata…
Read More
Ya gano maɗaurin aurensa ne mahaifin ’ya’yansa

Ya gano maɗaurin aurensa ne mahaifin ’ya’yansa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani mutum ya shiga cikin ɗimuwa bayan ya gano cewa fasto da ya ɗaura aurensa, shi ne mahaifin ’ya’yansa biyu. Wani labari mai ban mamaki, wanda ya faru a Zimbabwe, ya bayyana yadda aka umarci wani fasto daga cocin End Time Messages a Chiredzi, da ya ɗauri nauyin wasu yara. Binciken DNA ya nuna cewa, Fasto ɓhetu shi ne mahaifin ’ya’ya biyu da Eunice Mururi ta haifa bayan aurensu da Farai Hatirarami. Bayan gaskiya ta bayyana, auren Mururi da Hatirarami ya rushe. Yanzu haka dai Mururi ya maka Fasto ɓhetu ƙara kotu, inda yake neman fastom…
Read More
Duk da kashe maƙudan kuɗi babban layin lantarkin Nijeriya ya katse sau 105 a shekaru 10

Duk da kashe maƙudan kuɗi babban layin lantarkin Nijeriya ya katse sau 105 a shekaru 10

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da ɗimbin jarin da aka zuba a ɓangaren wutar lantarki, babban layin lantarkin Nijeriya ya katse kusan sau 105 a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Tinubu da magabacinsa, Muhammadu Buhari. Wani bincike da aka gudanar a ranar Lahadi ya nuna cewa Nijeriya ta samu kusan lamuni 10 da darajarsu ta kai dala biliyan 4.36 daga Bankin Duniya a cikin shekaru goma da suka gabata domin tunkarar manyan ƙalubale a ɓangaren wutar lantarki. Duk da cewa ba dukkanin lamuni 10 na Bankin Duniya aka biya gaba ɗaya ba, Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomin ƙasa da ƙasa sun…
Read More
’Yan sanda na binciken ɓacewar ɗan NYSC, Yahaya Faruk, a Ribas

’Yan sanda na binciken ɓacewar ɗan NYSC, Yahaya Faruk, a Ribas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar 'Yan Sandan Jihar Ribas na gudanar da bincike gadan-gadan kan ɓacewar Yahaya Faruk, wani mai yi wa ƙasa hidima (NYSC) da aka tura zuwa makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Ikuru a jihar ta Ribas kuma ya ɓace tun ranar 14 ga Oktoba, 2024. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ta Ribas, SP Grace lringe – Koko ya sanya wa hannu a ranar Laraba a Fatakwal ta ce, a ranar 15 ga Oktoba, 2024, shugaban makarantar Community Secondary School, Ikuru Town, Anderson Awaji Ogbana, ya kai wa rundunar rahoto, inda…
Read More
Yadda na ƙwace filin kamfanin Julius Berger – Wike

Yadda na ƙwace filin kamfanin Julius Berger – Wike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ya soke takardar shaidar mallakar fili na wasu filaye da aka ware wa katafaren gine-gine na Jamus, Julius Berger, a gundumar Katampe da ke Abuja. Ministan ya yi wannan jawabi ne a ranar Litinin a wurin bikin ƙaddamar da tsarin gina rukunin gidajen alƙalai 40 a babban birnin ƙasar. Taron ya samu halartar babban jojin Nijeriya (CJN), mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun; da shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem; da sauran manyan baki. Wike ya ce kashi 70 na kuɗaɗen aikin…
Read More
Kotu ta mayar wa Ali Musa kujerar takarar shugabancin Kumbotso a Kano

Kotu ta mayar wa Ali Musa kujerar takarar shugabancin Kumbotso a Kano

Daga RABI'U SANUSI Ana tsaka da yanke hukunci a babbar kotun jiha mai lamba huɗu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Usman Na Abba sai jam'iyyar NNPP ta mazabar Ɗan Maliki da ke cikin ƙaramar hukumar kumbotso ta fitar da sanarwar ta kori Hon Ali Musa hard worker daga jam'iyyar NNPP. Kotun kuma ta tabbatar da Hon Ali Musa Ɗan Maliki a matsayin halastaccen ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar kumbotso ƙarƙashin tutar jam'iyyar NNPP. Tun a baya dai majiyar mu ta ruwaito cewar, jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya janye sunan Ali Musa hard worker a matsayin ɗan…
Read More

Tinubu ne ya yanke shawarar cire tallafin fetur, ba mu muka sa shi ba – IMF

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kuɗi ta Ƙasa-da-ƙasa (IMF), ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya so cire tallafin man fetur a Nijeriya, ba wai su suka ba shi shawara ba. Daraktan Shiyyar Afirka na hukumar, Abebe Selassie ya bayyana hakan a ranar Juma'a, a yayin zaman IMF da Bankin Duniya da ke gudana a birnin Washington DC dake Amurka. Ya ce, aikinsu ya taƙaitu ne a tattauanawa akai-akai da ƙasashe, kamar yadda suka yi da Japan da Ingila. A ranar farko da Shugaba Tinubu ke shiga ofishi a shekarar 2023, ya sanar da cewa ya cire tallafin fetur…
Read More