Labarai

Babu wa’adi ga amfani da tsofaffin takardun kuɗi a Nijeriya – CBN

Daga BELLO A. BABAJI Babban bankin Nijeriya, CBN ya yi kira ga al'umma game da batun da ke yawo na cewa tsofaffin takardun nairori na N200, N500 da N1,000 za su daina amfani nan da ƙarshen shekarar 2024. Cikin wata takarda da Daraktar hulɗa da jama'a na bankin, Sidi Ali Hakama ta fitar a ranar Alhamis, bankin ya ce babu ƙamshin gaskiya game da labarin don haka ya ke kira ga al'umma su ƙaurace wa labarin. Bankin ya kuma ce hukuncin da Kotun Ƙoli ta yi na watan 29 ga watan Nuwamban, 2023, ya nuna cewa za a cigaba da…
Read More
‘Yan sanda sun janye jami’an su daga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

‘Yan sanda sun janye jami’an su daga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano

Daga USMAN KAROFI Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa za ta bi umarnin kotu da ta hana ta shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2024. Cikin wani saƙon bidiyo da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya fitar a ranar Juma’a, rundunar ta ce duk da haka, za ta tabbatar da tsaron rayuka a faɗin jihar. “Muna bin umarnin kotu da ta hana mu shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano. Duk da haka, za mu ci gaba da aiwatar da nauyinmu na kare rayuka da…
Read More

Wasu takardun kuɗi za su daina aiki kafin ƙarshen shekara – Majalisar Wakilai

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilai ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fara janye tsoffin takardun kuɗi na N200, N500, da N1,000 kafin wa’adin ranar 31 ga Disamba, 2024. A zaman majalisar na ranar Alhamis, ƴan majalisar sun nemi CBN ya ƙara adadin da ya ke fitarwa na sabbin kuɗaɗe don tabbatar da sauyin kuɗi ya gudana ba tare da matsala ba. Wannan ƙudiri ya biyo bayan ƙudirin gaggawa da Ɗan Majalisa, Afam Ogene ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan rashin isasshen wayar da kan jama’a game da wa’adin da ke tafe. Ogene ya lura cewa…
Read More

Hatsarin jirgin Fatakwal ya rutsa da ma’aikacin NNPCL

Daga BELLO A. BABAJI Wata helikwafta a Fatakwal da ke Jihar Ribas ta yi hatsari wanda ya rutsa da ɗaya daga cikin jami'an kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL. Kakakin kamfanin, Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa, helikwaftar wadda kamfanin East Wind Aviation ke gudanar da ita ta kasance ta na aiki ne da NNPCL a lokacin da lamarin ya faru. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:22 na safe a wani yanki na taruka da ke Fatakwal lokacin da jirgin ya tashi daga sansanin sojoji don zuwa tashar mai ta FPSO – NUIMS ANTAN. Aƙalla mutane takwas ne…
Read More

An soke tafiyar Shettima zuwa taron Samoa sakamakon tsaiko da jirginsa ya samu

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ba zai samu halartar taron ƙasashen masu tattalin arziƙi (Commonwealth Heads) ba da za a yi Samoa, kamar yadda aka tsara. Ofishin shugaban ƙasa ya sanar hakan jim-kaɗan bayan wani abu ya yi karo da jirginsa a wani filin jiragen sama na New York da ke Amurka wanda hakan ya sa aka soke zuwan Shettima taron. A saboda haka ne aka samar da wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Ministan Kula da Muhalli, Balarabe Lawal wadda za ta wakilci Nijeriya a taron, kamar yadda wata sanarwa da Mai taimaka wa shugaban ƙasa, Bayo…
Read More

Babbar Kotun Kano ta bai wa KANSIEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi

Daga RABI'U SANUSI Wata babbar kotu mai lamba 15 dake Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Sunusi Ado Ma'aji ta bai wa hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaben ƙananan hukumomi a gobe asabar. Mai shari'a Sunusi Ado Ma'aji ya bayyana cewa Hukumar zaɓen Kano tana da damar gudanar da wannan zaɓen nata bisa yadda take da hurumi. A ɓangarensa lauyan hukumar zaben ta KANSIEC da suka shigar da ƙara bisa yadda kotun tarayya dake Kano ta katange su da gudanar da zaɓen Barr. Lurwan Umar (SAN) ya ce wannan hukunci ya yi daɗi na babbar kotun ta Kano. Barr.…
Read More

MƊD za ta tallafa wa Nijeriya wajen cimma burin SDG

Daga BELLO A. BABAJI Ko’odinetan Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Fall, ya jaddada ƙudirin ƙungiyar na tallafa wa ƙasar wajen cimma muradun ci-gaba mai ɗorewa (SDGs). Fall ya bada tabbacin hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, a wani taron manema labarai na bikin cika shekaru 79 na ranar Majalisar Ɗinkin Duniya. Ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar muhimmanci, inda ya ce ƙungiyar ba za ta cimma muradun ƙarni ba idan Nijeriya ba ta cimma hakan ba. "A cikin ƙasa da shekaru biyar, dole ne mu cimma Ajandar 2030, taron ƙoli na gaba da babban sakamako", inji…
Read More

Kisan kiyashi ake yi a Gaza, ba yaƙi ba – Ofishin jakadancin Palestine

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake cigaba da tada zaune-tsaye tsakanin ƙasashen Gabas-ta-Tsakiya musamman a yankin Gaza na ƙasar Palestine inda a nan ne aka fi zubar da jinanen bayin Allah, lamarin ya yi ƙamari a Arewacin jihar inda aka fi ɗaiɗaita mutane da garuruwansu. Wani abin takaicin shine yadda mutane ke ta mutuwa a kan titina saboda tsananin wahala ta yunwa da rashin matsuguni. Cikin wata takarda da Jakadan Palestine a Nijeriya, Abdallah Abu Shawesh ya fitar, ya ce yayin da aka cika kwanaki 384, Amurka da Isra'ila na kisan kiyashi wa al'ummarsu, ya bayyana yadda adadin ke…
Read More
‘Yan bindiga sun sa harajin miliyan N11 kafin girbi ga manoman Neja

‘Yan bindiga sun sa harajin miliyan N11 kafin girbi ga manoman Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun saka harajin Naira miliyan 11 a ƙauyukan ƙaramar Hukumar Mariga ta jihar Neja kafin su ba su damar girbe amfanin gonakinsu. Manoman da harajin ya shafa da suka haɗa da: Dusai da Holobo da Sabon-Wuri da Hunyo da Meba da Farin-Ruwa da Kubashi da Mazame da Kakihun da Mai-kanwa da kuma Kuimo a Unguwar Gulbin Boka da ke gundumar Mohoro, sun shaida wa Manhaja cewa sun yi yunƙurin roƙon shiga tsakani, amma hukumomin jiha ko na tarayya ba su bayar da taimako ba. Daya daga cikin manoman da ya nemi a…
Read More
Tsadar iskar gas ya tilasta wa Gwamnatin Tarayya ɗaukar tsattsauran mataki kan NNPCL

Tsadar iskar gas ya tilasta wa Gwamnatin Tarayya ɗaukar tsattsauran mataki kan NNPCL

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na Nijeriya (Na iskar gas), Ekperikpe Ekpo, ya ba wa kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL, da masu harkar iskar gas(LPG) umarnin dakatar da fitar da shi zuwa ƙasashen ƙetare daga 1 ga watan Nuwamba. Mista Ekpo ya ba da wannan umarni ne a ranar Talata a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja. Wannan mataki na zuwa ne domin magance hauhawar farashin iskar gas da ‘yan Nijeriya suka fara fuskanta. A cikin jawabin da mai magana da yawunsa ya yi, Louis Ibah, ya ce ministan ya…
Read More