25
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta shirya kafa Cibiyar Tsaron Makarantu a Hedkwatar Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) a Kano. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, a lokacin taron wayar da kan jama’a na yini ɗaya kan aiwatar da shirin Tsaron Makarantu. Taron mai taken “Fahimtar Asalin Tsaron Makarantu” an yi shi ne don ƙara fahimtar muhimmancin tsaro a makarantu. A wata sanarwa da Ibrahim Idris Abdullahi, jami’in hulda da jama’a na Hukumar Tsaron Fararen Hula…
