Labarai

Tinubu ya naɗa Ministan Kiwon Dabbobi bayan sallamar wasu biyar

Tinubu ya naɗa Ministan Kiwon Dabbobi bayan sallamar wasu biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Tinubu ya naɗa Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi, makonnni kaɗan bayan ya karɓi rahoton Kwamitin Shugaban ƙasa kan kafa ma’aikatar. Shugaban ƙasar ya kuma sanar da naɗi Idi Mukhtar Maiha a matsayin ministan sabuwar ma’aikatar. Naɗin ministan kula bunƙasa kiwon dabbobin na cikin jerin sabbin ministoci bakwai da shugaban ƙasar ya naɗa bayan sallamar wasu ministoci daga gwmanatinsa. Sabbin ministocin nasa sun haɗa da maza huɗu da mata uku, ciki har da Ambasada Bianca, matar tsohon madugun neman kafa ƙasar Biafra, Marigayi Odumegwu Ojukwu, a matsayin ƙaramar Ministar Harkokin Waje. Mace ta biyu ita…
Read More
Fitowata daga kurkuku sabon babi ne a rayuwata – Faruk Lawan

Fitowata daga kurkuku sabon babi ne a rayuwata – Faruk Lawan

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Dan Majalisar Wakilai, Hon. Farouk Lawan ya shaƙi iskar ’yanci daga gidan yari na Kuje bayan ya kammala zamansa, inda ya bayyana ficewar a matsayin wani sabon babi a rayuwarsa. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Adamu Duza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce: “Eh, an sake shi ne bayan ya kammala zaman da aka tanke masa.” A cikin wata sanarwa da ya fitar, Lawan ya gode wa Allah da samun kansa, wanda ya ce, ya zama farkon wani sabon babi a rayuwarsa. Ya ce, “na gode wa Allah Ta’ala. Alhamdulillah. Alhamdulillah. Alhamdulillah.…
Read More
Mafi ƙarancin albashi: Gwamnan Kebbi ya amince da biyan N75,000 ga ma’aikata

Mafi ƙarancin albashi: Gwamnan Kebbi ya amince da biyan N75,000 ga ma’aikata

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu ya bi sahun waɗansu daga cikin gwamnoni da suka amince da biyan mafi ƙarancin albashi ka da ya kasa Naira 70,000 ga ma'aikatan jihohinsu tare da ƙananan hukumomi. Ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan na jihar Kebbi ya amince da biyan Naira 75,000 ga ma'aikatan jiha da ƙananan hukumomi zuwa malamai, inda ya umarci kwamishinan kuɗi da babban akawun kuɗi na jihar da su tabbatar da an biya sabon mafi ƙarancin albashin a cikin kwanaki biyu daga Laraba zuwa yau Juma'a.  Gwamnan ya bayyana cewa ya…
Read More
Hukumar alhazai ta Kebbi ta nemi maniyyata su fara adashin gata

Hukumar alhazai ta Kebbi ta nemi maniyyata su fara adashin gata

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi Hukumar jin daɗin Alhazzai ta Kebbi ta yi kira ga maniyyata aikin hajji na shekarar 2025 mai zuwa da su soma kai kuɗin ajiya na adashin gata da aƙalla kada ya yi ƙasa da Naira milliyan shida a matsayin kuɗin ajiya na farko. Haka-zalika kuma ana sa ran kowane maniyyaci zai biya sauran ragowar kuɗin kujerarsa daga nan zuwa watan Nuwamba mai zuwa da za su iya kai naira miliyan biyu da dubu ɗari huɗu. Da ya ke bayani, shugaban hukumar jin dadin alhazan Alhaji Musa Yaro (Enabo) ya ce wannan shi zai bai wa…
Read More
Uwargidan gwamnan Kebbi ta ƙaddamar da cibiyar maganin ciwon tari a Argungu 

Uwargidan gwamnan Kebbi ta ƙaddamar da cibiyar maganin ciwon tari a Argungu 

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Uwargidan gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir ta buɗe wata cibiya don bayar da maganin ciwon tarin TB kyauta a garin Argungu. Da ta ke buɗe cibiyar a wani sashe na babbar asibitin garin Argungu, Hajiya Zainab Nasir ta bayyana cewa yanzu an samo maganin ciwon tarin TB mai inganci ba kamar irin waɗanda cutar ke bijirewa ba. Ana rasa rayuka da dama sanadiyyar ciwon da ake iya magancewa saboda halin ko-oho da mutanen da ke ɗauke da cututtukan ke nunawa wanda da sun dage da shan magani za su iya warkewa. Ta ƙara da…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan Injiniya Gilima

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan Injiniya Gilima

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Raya Birane ta jihar Kaduna (KASUPDA), ƙarƙashin Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa wani gida mai shekaru 22 mallakin Injiniya Yahya Gilima, wani fitaccen Injiniyan gine-gine a jihar. Wannan gida da aka rusa kammalallen gida ne da ke lamba 11, Titin Yahya Imam da ke Malali a Kaduna, wanda Injiniya Gilima ya mallaka tun a shekarar 2002, inda aka fara aikin ginawa nan take, sannan aka kammala a shekarar 2003. Sai dai kuma a ranar Juma’a, kwatsam sai suka wayi gari an liƙa masu wata sanarwa a jikin bangon…
Read More
An ƙaddamar da Manhajar WikiHausa a birnin Kano

An ƙaddamar da Manhajar WikiHausa a birnin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ranar Asabar da ta gabata, an ƙaddamar da babbar Manhajar nan ta Hausa mai suna WikiHausa da take ƙunshe da rayuwar Bahaushe a harshen Hausa. Isah Uba Chamo wanda shi ne shugaban Manhajar kuma shi ne ya samar da ita, ya bayyana cewa an ƙirƙiri Manhajar ne domin ta samar da ingantaccen ilimi a yanar Gizo. Ya ce aƙalla shekara 6 da kafa wikiHausa, amma ya ce da ya yawa wasu ba su san shi ne ya kirƙire ta ba, wasu sun ɗauka 'yan ƙasar waje ne suka yi ta. Ya kara da cewa"…
Read More
Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin sabon albashi na N70.000 a Katsina

Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin sabon albashi na N70.000 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince da kafa kwamitin da zai tsara yada gwamnati zata fara biyan ma'aikatan jihar sabon tsarin albashi. Wata takardar sanarwa daga ofishin mataimakin gwamna ɗauke da sa hannun Hassan Abubakar Ɗayyabu na nuna cewa sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba faskari zai kasance shugaban kwamitin. Sauran mambobin kwamitin sun haɗa shugaban ma'aikatan jihar da Kwamishinonin kasafin kuɗi da na ma'aikatar kudi da kuma na ƙananan hukumomi da masarautu. Akwai kuma babban akawun kuɗi na jihar da shugaban hukumar tattara haraji na jihar da daraktoci masu binciken kuɗi na jiha dana ƙananan hukumomi.…
Read More
Ministan tsaro ya ziyarci Zamfara, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Lawal wajen yaƙi da ‘yan bindiga

Ministan tsaro ya ziyarci Zamfara, ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Lawal wajen yaƙi da ‘yan bindiga

zDaga USMAN KAROFI Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan jajircewarsa da goyon baya ga ayyukan soji a Jihar Zamfara. A ranar Alhamis, ministan ya ziyarci fadar gwamnatin Zamfara da hedikwatar Rmrundunar haɗin gwiwa ta Arewa Maso Yamma, (Operation Fansar Yamma) da ke Gusau. Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa ziyarar tana da nufin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jiha da ma'aikatar tsaro. Sanarwar ta ƙara da cewa ministan ya tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a matsayin ci gaba daga ziyarar da gwamnonin Lawal na Zamfara da…
Read More
Ƙungiyar AFAN ta nisanta kanta daga wani shirin bashi ga manoma

Ƙungiyar AFAN ta nisanta kanta daga wani shirin bashi ga manoma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙungiyar manoma ta Nijeriya (AFAN) ta nisanta kanta daga wani shirin ba da rance ga manoma wanda ake tallatawa a kafafen sada zumunta na zamani. Shafin yanar gizon da ke tallata bashin yana ikirarin cewa Ma'aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar manoma ta Nijeriya (AFAN) da bankunan raya masana'antu su ke ɗaukar nauyin bashin. Har ila yau shafin yayi ikirarin cewa duk manomin da ya shiga shafin zai samu rancen Naira 550,000 don bunƙasa nomansa. Amma wata sanarwa daga shugaban AFAN na Jihar Katsina, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ta…
Read More