Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya miƙa sunayen sababbin ministoci ga Majalisar Dattijai

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattijai ta karɓi sabbin sunayen ministoci bakwai da da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana su a ranar Laraba don tantancewa. Shugaba Tinubu ya aika da saƙon ne ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio wanda aka karanta shi a zaman Majalisar na ranar Alhamis. Sunayen ministocin sune kamar haka; Dakta Nantawe Yilwatda, Ministan Jin-ƙai da Rage Talauci; Muhammadu Maigari Dingyaɗi, Ministan Ƙwadago da Ɗaukar aiki; Bianca Odinaka Odumegu-Ojukwu, Ƙaramar Ministar Harkokin Waje; Dakta Jumoke Oduwole, Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Ci-gaba; Idi Muktar Maiha, Ministan Ci-gaban Kiwo; Rt Hon. Yusuf Abdullahi Ata, Ƙaramin Ministan Gine-gine; da kuma…
Read More

Saƙon Sakatare-Janar na MƊD a ranar bikin Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2024

Daga BELLO A. BABAJI Duniya ce ta gina Majalisar Ɗinkin Duniya domin hidimta wa al’ummar duniya. Tun daga 1945, ya zama an tsara wasu ƙasashe da za su samar da mafita da haɗin-kai don magance matsalolin duniya da samar da zaman lafiya. Mafitar da za ta kawo sassaucin tashe-tashen hankula, da kuma gina hanyoyin da za su wanzar da zaman lafiya. Ba wani abu ba ne mafita illa kawar da fatara, da zaburar da ci-gaba mai ɗorewa, da tsayawa wajen ganin an taimaki masu rauni. Mafitar da ke bada agajin ceton rai ga mutanen da ke rayuwa a yankunan da…
Read More
Gwamnatin Katsina ta buƙaci asibitoci masu zaman kansu su sabunta rajista

Gwamnatin Katsina ta buƙaci asibitoci masu zaman kansu su sabunta rajista

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Gwamnatin Jihar Katsina ta buƙaci dukkan asibitoci masu zaman kansu da ke aiki a jihar su tabbatar su cika ƙa'idojin da doka ta shinfiɗa ta hanyar sabunta rajistarsu. Haka kuma an buƙacie su da su tabbatar suna da kayan aiki na zamani,ma'aikata masu ƙwarewa da kayan aikin jinya masu inganci. Kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya bayyana haka tare da gargaɗin cewa cibiyoyin da suka kasa bin wannan doka za a ɗauki matakan rufe su nan take . Yace dokar Edict No.5 na shekara 1999 wadda ta tsara ƙa'idojin gudanar da cibiyoyin lafiya…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin gyaran ilimi a jihar

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin gyaran ilimi a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ganin yadda ake ta samun yawaitar faɗuwar jarabawar kammala karatun sakandare gwamnan Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da kwamitin da zai duba matsalolin da ke tattare da harkan ilimi tare da gano bakin zaren. Da yake ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnan jihar, sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba faskari ya bayyana dalilin kafa wannan kwamiti da yace ƙalubalen da ake fuskanta a ɓangaren ilimi ya sa aka kafa kwamitin. Yace gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin domin gina ginshiƙin ilimi mai ɗorewar ga makomar jihar Katsina. Sakataren gwamnatin ya ƙara da cewa kwamitin zai mayar da…
Read More

Sarki Sanusi zai naɗa Ali Muktar a matsayin sabon Sa’in Kano

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a 25 ga watan Oktoba, 2024 ne Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai naɗa sabon Sa'in Kano. Za a gudanar da taron naɗin ne a Masallacin gidan Sarki da ke Kofar Kudu a Kano, da misalin ƙarfe 9 na safe. Arc. Ali Muktar, shi ne wanda za a bai wa Sarautar Sa'in kuma Hakimin Makoɗa. Cikin wata takarda da Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmed ya aika masa, ya taya shi murna game samun matsayin, ya na mai kira a gare shi da ya sanar da ƴanuwa da abokan arziƙi don su taya…
Read More

Za a yi zaɓen ƙananan hukumomin Kano duk da hukuncin kotu – Ɗan Majalisa

Daga BELLO A. BABAJI A kwanaki biyu da suka gabata ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin dakatar da Hukumar zaɓe ta jihar (KANSIEC) daga gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi. Kotun ta yi hakan ne bayan wani zargi da ta yi da ke alaƙanta jagororin hukumar da wata jami'yya a jihar wanda hakan ya saɓa wa dokar hukumar a mataki na jiha da ma ƙasa baki ɗaya. Duk da wannan hukunci da kotun ta yi, shirye-shirye game da zaɓen na cigaba da gudana yadda aka tsara, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Daga cikin ayyukan zaɓen akwai ɗaukar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da cibiyar sauya fasalin mota zuwa CNG a Jihar Kano

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da cibiyar sauya fasalin mota zuwa CNG a Jihar Kano

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar cibiyar sauya fasalin motoci da ababen hawa daga masu amfani da man fetur zuwa masu amfani da iskar gas na CNG a garin Gundutse dake ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano. Oluwemimo Joseph Osanipin, wanda shine Babban Darakta kuma Babban Jami’in Hukumar Kula da Kera Motoci ta Ƙasa ne ya bayyana hakan a ranar litinin yayin ƙaddamar da cibiyar, inda ya ce kafa cibiyar zai inganta sauya motoci zuwa masu amfani da CNG tare da ba da horo ga makanikai kan yadda zasu dinga yin sauyin. Ya kara da cewa, daga…
Read More
Shugaba Tinubu ya sallami wasu ministoci da naɗa wasu sababbi

Shugaba Tinubu ya sallami wasu ministoci da naɗa wasu sababbi

Fadar shugaban ƙasa ta sanar da sabon naɗe-naɗen ministoci tare da sake fasalin ma’aikatu, wanda zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da gudanar da harkokin mulki a ƙasar. Wannan sanarwar ta zo ne a watan Oktoba 2024, inda aka bayyana wasu canje-canje masu muhimmanci da suka shafi naɗe-naɗen ministoci, sauya ma’aikatu, da kuma sallamar wasu ministoci daga majalisar zartarwa. Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi, akwai haɗa ma’aikatar yawon buɗe ido da ma’aikatar al’adu ta tarayya don zama ma’aikatar al’adu, yawon buɗe Ido, da tattalin arziki na Ƙirƙire-ƙirƙire. Wannan matakin an ɗauke shi ne domin ƙara haɗa kai da…
Read More
Ku sayi fetur a kan Naira 1000 duk lita ko kuma ku sayi CNG N200 duk mita – Tinubu

Ku sayi fetur a kan Naira 1000 duk lita ko kuma ku sayi CNG N200 duk mita – Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce direbobin motocin Nijeriya yanzu za su iya siyan litar Man Fetur, wanda aka fi sani da fetur, a Naira 1,000 kowace lita. Shugaban ya kuma bayyana cewa kwatankwacin litar man fetur, wato Standard Cubic Meter na Gas (CNG), za a iya samun sa a Naira 200. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da shugabannin kamfanin Nigerian Independent Petroleum Company (NIPCO), tare da darektan kamfanin, Mista Ramesh Kasangra, a fadar gwamnati dake Abuja a ranar Talata, bisa ga wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan bayani da dabaru, Bayo…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi – Sojojin sama na Nijeriya guda biyar sun mutu sanadiyar haɗarin mota

Da Ɗumi-Ɗumi – Sojojin sama na Nijeriya guda biyar sun mutu sanadiyar haɗarin mota

Wasu jami'an rundunar sojan saman Nijeriya sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Jos zuwa Akwanga. Haɗarin ya auku a ranar 22 ga watan Oktoba yayin da jami'an ke hanyar zuwa Abuja domin halartar wani taron wasanni inda motar su tayi karo da wata babbar mota da ke tafe. Daraktan yaɗa labari na rundunar sojan saman, Air Comodore Olusola ya tabbatar da faruwan wannan lamarin, inda ya nuna irin halin baƙin ciki da rundunar ta ke ciki domin waɗannan gagaruman rashi. Olusola ya cigaba da bayyana yadda rundunar sojan za ta…
Read More