23
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilai ta gayyaci Ministan Abuja, Nyesom Wike da Darakta-Janar na Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Oluwatosin Ajayi da Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Peter Opara da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan harkar tsaro don daidaita matsalolin tsaro a Abuja. Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan gabatar da wani ƙudiri na muhimmacin kula da garuruwa da Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Toro ta Jihar Bauchi, Haruna Dabo ya gabatar a zaman Majalisar na ranar Talata. Dabo ya gabatar da ƙudirin ne jim-kaɗan bayan garkuwa da kuma kashe mai taimaka masa, Ni'ima Sulaiman da wasu ƴan bindiga suka yi…
