Labarai

Kotu ta tsige shugaban hukumar zaɓe ta Kano bayan gano alaƙarsa da wata jami’yya

Daga BELLO A. BABAJI Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tsige Farfesa Sani Malumfashi daga muƙaminsa na shugaban hukumar zaɓe ta jihar, KANSIEC sakamakon alaƙarsa da wata jami'yya. Mai Shari'a Simon Amobeda ya gabatar da hukuncin a ranar Talata bayan da Aminu Aliyu Tiga da jami'yyar APC reshen jihar suka shigar da ƙara akan sa. Da farko dai, APC ta ƙalubalanci hukuncin da hukumar zaɓen ta yi na sanya Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin shiga takarar shugaban ƙaramar hukuma da Naira miliyan 5 ga kujerar kansila a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe.
Read More
Ƙarya ku ke, babu mai suna Ibrahim da Yahaya a masu taimaka min –  Sanata Ashiru ga NDLEA

Ƙarya ku ke, babu mai suna Ibrahim da Yahaya a masu taimaka min – Sanata Ashiru ga NDLEA

Sanata Oyelola Ashiru ya musanta zargin da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta yi masa, tana cewa an kama shi da kwayoyi masu haɗari. NDLEA ta bayyana cewa an kai samame gidan Sanata Ashiru dake Ilorin, Jihar Kwara, kuma an samu miyagun ƙwayoyi a gidan. Wannan zargi ya biyo bayan bayanin da Sanata Ashiru ya yi a zauren majalisa na cewa hukumar NDLEA tana amsar cin hanci. Sai dai wata sanarwa da mai taimaka masa na harkokin majalisa, Olaitan Adeyanju, ya fitar ya ce zargin ƙarya ne. "Abin kamar shirme, domin hukumar NDLEA sai bayan Sanata Ashiru…
Read More
Shugaban ƙasar Kamaru ya bayyana bayan raɗe-raɗin mutuwa

Shugaban ƙasar Kamaru ya bayyana bayan raɗe-raɗin mutuwa

Shugaban ƙasar Kamaru mai shekaru 91, Paul Biya, an gan shi a bainar jama’a a karon farko bayan makonni shida da ake raɗe-raɗin mutuwarsa. Ɓatan sa daga idon jama'a ya haifar da jita-jitar rashin lafiyarsa, har ma wasu suka yi tunanin ya rasu. Amma a ranar Litinin da rana, gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ya nuna faifan bidiyon isowar shugaban a filin jirgin saman birnin Yaoundé daga wani jirgi da ya taso daga Switzerland. Gwamnatin ta haramta wa kafafen yaɗa labarai tattauna lafiyar Biya — wanda ya yi mulki tun daga shekarar 1982, ta na mai bayyana hakan a matsayin…
Read More
Gwamnatin Jigawa za ta ƙaddamar da shirin ɓunkasa ilimi

Gwamnatin Jigawa za ta ƙaddamar da shirin ɓunkasa ilimi

Daga ABUBAKAR M TAHEER Gwamnatin Jihar Jigawa za ta fara gudanar da shirin Citizen Leads Initiative nan ba da jimawa ba domin bunƙasa harkokin ilimi da koyarwa a jihar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata zantawa da ƙwararriyar mai bawa gwamna shawara kan harkokin ilimi Dakta Hauwa Mustapha Ɓaɓura ta Jihar Jigawa kan halin da jihar take ciki na taɓarbarewar harkokin ilimi. Gwamnatin jihar za ta gayyaci sarakuna,yan kasuwa,malamai da masu riƙe da madafun iko domin ciyar da fannin ilimi a jihar. Shirin Citizen Lead initiative zai kasance wata hanya ta musamman da dukkan ɓangarorin al'ummar daga ciki da wajen…
Read More
Malaman firamare 17,000 su ka sami horo a Katsina

Malaman firamare 17,000 su ka sami horo a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Malaman makarantun firamare 17000 su ka samu horo daban daban akan sanin makaman aiki da yadda zasu inganta koyarwa a jihar. Shugaban hukumar ilimin firamare na bai ɗaya (SUBEB) Dakta Kabir Magaji ya bayyana haka a taro da yayi da sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomi 34 da ke Jihar Katsina. Ya ce hukumar ta na bada horaswar ne ga malamai domin su san sabbin dabaru na koyarwa ta yadda su ma za su tafi da zamani. Dakta Magaji ya tabbatar da cewa su ma sauran malaman da ba su sami halartar horon da su shirya…
Read More
Gwamna Namadi ya rantsar da ‘yan kwamitin da za su binciki hatsarin Majiya

Gwamna Namadi ya rantsar da ‘yan kwamitin da za su binciki hatsarin Majiya

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa da ke Arewacin Nijeriya ya ƙaddamar da kwamitin da zai binciki musabbabin aukuwar gobarar da ta yi sanadin rasa rayukan al,umma a ƙauyen Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura. Kuma kwamitin shine zai Kula da rabawa al,ummar ƙauyen na Majiya tallafin da jama,a da gwamnatin Jigawa ta kafa sakamakon haɗarin motar mai da ya haifar da mutuwar mutane kimanin 180 a ƙauyen na Majiya da ke ƙaramar hukumar Taura. Gwamna Namadi ya rantsar da kwamitin mai mutane 25 yau a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse a ƙarƙashin…
Read More

Kamfanin Ɗangote zai janye ƙarar biliyan N100 da ya shigar akan NNPCL da AA Rano da wasu

Daga BELLO A. BABAJI Rukunin Kamfanin Ɗangote ya ce zai janye ƙarar Naira biliyan 100 da ya shigar kan Hukumar Kula da Tace Albarkatun Man fetur ta Ƙasa (NMDPRA) na bada lasisin shigo da mai ga Kamfanonin man fetur na NNPCL, Matrix, AA Rano da wasu guda huɗu duk da cewa akwai matatar gida da ke samar da tataccen fetur. Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a daren ranar Litinin, ya ce ƙarar da suka shigar a ranar 6 ga watan Satumba, 2024 ta ƙunshi tsohon batu wanda a yanzu ababen da ke faruwa sun sha ƙarfin ƙarar. Kakakin…
Read More

Zamfara: Magoya bayan Hon. Kabiru Classic sun saya masa takardar takarar shugaban ƙaramar hukuma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Magoya bayan Kabiru Yahaya Classic, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne daga Jihar Zamfara, sun haɗa hannu wajen saya masa takardar tsaya wa takarar kujerar shugaban ƙaramar hukumar Talata Mafara. Rahotonni sun bayyana cewa, a makon da ya gabata ne aka gudanar da wani taron gaggawa a gidan tsohon ɗan majalisar tsakanin jagorori da magoya bayansa daga mazaɓu 11 na ƙaramar hukumar, wanda ya samu halartar mutane da dama. An shirya taron ne don tattauna muhimman batutuwa da suka shafi jami'yyar PDP a Talata Mafara musamman saboda yadda Hon. Classic ya nuna damuwa kan…
Read More

Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin rufe makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwmnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya bayar da umarnin a rufe dukkanin makarantun koyon aikin kiwon lafiya masu zaman kansu da ke jihar. Gwamnatin jihar ta kuma soke lasisin makarantun bayan wani bincike da ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar ta gudanar game da yadda makarantun ke tafiyar da ayyukansu. Mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya, Umar Mammada ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta Katsina, a ranar Litinin. Ya ce, a ƴan shekarun nan jihar ta samu ƙaruwar cibiyoyi masu…
Read More