21
Oct
Daga USMAN KAROFI Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta bayyana cewa babu wani muƙaddashin babban hafsan sojojin Ƙasa (COAS) da aka naɗa, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa. A cewar wata sanarwa da ta fitar, an bayyana cewa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja yana kan hutun shekara, kuma babu wani sabon naɗe-naɗe a cikin rundunar. Sanarwar ta kara da cewa dukkan hafsoshin soji suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Manjo Janar Abdulsalami Bagudu Ibrahim, wanda yake babban hafsan tsare-tsare da shirye-shirye na sojojin ƙasa, yana ba da rahotanni na yau da kullum ga babban hafsan sojojin ƙasa, yayin…
