20
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), ta ce ta na shirin gudanar da bincike game matsalar ɗaukewar lantarki da ake samu a ƴan kwanakin nan daga rumbun lantarkin Nijeriya. Ta ce dalilin yin hakan shine don gano ainihin musabbabin abin da ke haifar da faruwar lamarin akai-akai. NERC ta bayyana hakan ne ta shafinta na X a ranar Asabar inda ta ce za a yi hakan ne don samar da mafita ta dindindin game da al'amarin. Hukumar ta kuma ce za ta sanar da rana da lokaci da za a yi zama game batun…
