19
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Alamu sun nuna cewa shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC ka iya dakatar da taron ƙaddamarwa na babban kwamitin Zartarwa na Ƙasa, NEC zuwa 2025. An samu wasu bayanai daga Sakatariyar APC kan cewa ayyuka da suka yi wa Shugaba Tinubu yawa da rashin kasancewar sa a ƙasa su ne dalilan da suka sa za a ɗage zaman. Wata majiya ta ce, saboda Shugaba Tinubu ba ya ƙasa ya sa aka dage zaman a karon farko wanda aka tsara yin sa tun a watan Satumban da ya gabata. Duk da cewa ba a samu…
