Labarai

Wike ya roƙi ’yan Nijeriya su riƙa biyan haraji don raya ƙasa

Wike ya roƙi ’yan Nijeriya su riƙa biyan haraji don raya ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su biya haraji, yana mai cewa gwamnati a kowane mataki na buƙatar samun kuɗi domin samar da ayyukan yi ga ’yan Nijeriya. Wike ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Abuja, a wajen babban taron kasuwanci da zuba jari na Abuja wanda kamfanin 'Abuja Inɓestment Company Limited' ya shirya. Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya ce taken taron shi ne; ‘Haɓaka Zuba Jari Ta hanyar Haɗin kai’, ya dace da yunƙurin Gwamnatin Tarayya na tura ikon haɗin gwiwa don samar da damar…
Read More
Hajjin 2025: An buƙaci maniyyatan Edo su fara adashin gata da miliyan N8.4

Hajjin 2025: An buƙaci maniyyatan Edo su fara adashin gata da miliyan N8.4

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Edo, ta umurci dukkan maniyyata aikin Hajjin shekarar 2025 da su yi ajiyar farko ta Naira Miliyan 8.4, har zuwa lokacin da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) za ta fitar da sanarwar ƙarshe. Shugaban hukumar Ibrahim Oyarekhua ne ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata yayin ganawa da manema labarai a Benin. Ya jaddada buƙatar samun kuɗaɗen ajiya da wuri, yana mai nuni da canjin manufofin Saudiyya na baya-bayan nan da ke buƙatar a biya aƙalla watanni biyu kafin ranar Arafat. Oyarekhua ya ci gaba da…
Read More
Ranar Abinci Ta Duniya: Monoma  matan Zamfara sun yi bajekolin kayan noma

Ranar Abinci Ta Duniya: Monoma  matan Zamfara sun yi bajekolin kayan noma

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Kungiyar Mata Manoma ‘Nigerian Association of women in Agriculture’ (NAWIA), reshen Jihar Zamfara tare da haɗin gwiwa da ofishin matar gwamnan jihar, Hajiya Huriyya Dauda, sun gudanar da bikin Ranar Abinci ta Duniya, inda suka bajekolin hajarsu na amfani gona da kowacce ƙaramar hukuma ke nomawa a ranar Laraba da ta gabata.  A jawabin ta uwar gidan gwamna, Dauda Lawal, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa, Majalisar ɗinkin Duniya ta ayyana ranar Abinci ta Duniya tana mai jaddada cewa, matan Jihar Zamfara ba a bar su a baya ba wajen nuna ma duniya amfanin…
Read More
‘Yan siyasa ne ke haifar da ƙaruwar shaye-shaye ga matasa – Kawu Sumaila

‘Yan siyasa ne ke haifar da ƙaruwar shaye-shaye ga matasa – Kawu Sumaila

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kawu Sumaila, Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, ya ce wasu 'yan siyasa da bai fadi sunayensu ba na haddasa yawaitar amfani da miyagun kwayoyi a kasar nan. Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sumaila ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a zauren majalisar dattawa, yayin da ya ke ba da gudunmuwa a muhawara kan ƙudirin dokar da ke neman kafa cibiyar ƙasa ta wayar da kan jama'a game da amfani da ƙwayoyi da kuma gyaran hali. Sanata Rufai Hanga wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya, shi ne ya gabatar da ƙudirin.…
Read More
Allah bai halicci Nijeriya don shiga mummunan hali ba – Obasanjo

Allah bai halicci Nijeriya don shiga mummunan hali ba – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce ba yin Allah ba ne Nijeriya ta yi fama da matsalar tattalin arziki, yana mai cewa kasar na da albarkatu masu yawa. Tsohon shugaban na Nijeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 40 na Archdiocese na Abuja a Abuja a ranar Lahadi, 13 ga Oktoba. Obasanjo ya jaddada cewa Nijeriya na da duk abin da take bukata don ci gaba. “Kamar yadda Allah ya halicci sauran al’ummai, ya ba su albarkatu, haka nan kuma ya albarkaci Nijeriya da albarkatu…
Read More
Waɗanda suka kashe Hanifa a Kano sun nemi kotu ta soke hukuncin kisa a kan su

Waɗanda suka kashe Hanifa a Kano sun nemi kotu ta soke hukuncin kisa a kan su

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu mutum biyu da aka samu da laifin yin garkuwa da kisan Hanifa Abubakar ‘yar shekara biyar, Abdulmalik Muhammad Tanko da Hashimu Isyaku, sun shigar da kara kotu inda suke ɗalubalantar hukuncin kisa a kotun ɗaukaka ɗara da ke Kano. Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga watan Yuli, 2022, wata babbar kotun jihar Kano ɗarɗashin jagorancin mai shari’a Usman Mallam Na’abba ta yanke wa mutanen biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shari’ar. Sannan kuma an yanke musu hukuncin shekaru biyar da huɗu kowannensu bisa laifin haɗa baki, domin dukkansu sun…
Read More
Gwamnatin Nijar ta sauya wa titina suna masu ɗauke da sunayen Faransawa

Gwamnatin Nijar ta sauya wa titina suna masu ɗauke da sunayen Faransawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta sauya sunayen tituna da duk wasu abubuwa da ke ɗauke da sunayen Faransa, a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na yanke duk wata hulɗa tsakaninta da tsohuwar gijiyarta. Mai magana da yawun gwamnatin sojin Col Maj Abdurrahman Amadu ne ya sanar da hakan, tare da kare matakin da cewa ya zama wajibi domin maye gurbin sunayen da gwarazan jamhuriyar ta Nijar. Manjo Abdurrahman Amadu ya ce yawancin sunayen da aka sanya wa manyan titunan birnin Yamai, babu abin da suke tunawa ‘yanƙasar face baƙar wuyar da suka…
Read More
Ko za a kore ni daga APC ba zan daina faɗar gaskiya ba – Ndume

Ko za a kore ni daga APC ba zan daina faɗar gaskiya ba – Ndume

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani ƙusa a Jam'iyyar APC mai mulkin Nijeriya kuma ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam'iyyar. Sanata Ali Ndume ya ce: "Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya ma shugaban ƙasa don a kawo gyara". Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran jam'iyyarsa ta APC ya ɓaci,…
Read More
Sabbin tsare-tsaren Sa’adatu Liman yana inganta ilimi a Jami’ar Jihar Nasarawa, inji Akaro Mainoma

Sabbin tsare-tsaren Sa’adatu Liman yana inganta ilimi a Jami’ar Jihar Nasarawa, inji Akaro Mainoma

Daga JOHN D. WADA a Lafiya An yaba wa Shugabar Babbar Jami’ar Jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Liman dangane da tabbatar da daurewar al’adun jami’ar  tun da ta hau ragamar mulkin kawo yanzu. Tsohon Shugaban Jami’ar Farfesa Mohammed Akaro Mainoma ne ya bayyana haka a jawabinsa a wajen wani taron gabatar da lacca na musamman wato Inaugural lecture a Turance wadda jami’ar ke yi a wata-wata da aka gudanar a babban ɗakin taron jami’ar a mako da ake ciki. Farfesa Mohammed Akaro Mainoma ya ce dole a yaba wa Farfesa Sa’adatu Hassan Liman idan aka yi la’akari da yadda kawo yanzu…
Read More
Ƙaramar Hukumar Nasarawa za ta zama abin kwatance a Jihar Kano – Ogan Boye

Ƙaramar Hukumar Nasarawa za ta zama abin kwatance a Jihar Kano – Ogan Boye

Daga RABIU SANUSI a Kano Dan takarar ƙaramar Hukumar Nasarawa dake Jihar Kano ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP, Hon. Yusuf Imam da akafi sani da 'Ogan ɓoye,  ya bayyana ƙudurinsa na ganin maido da martabar ƙaramar hukumar da yake takara kan turbar da ta dace. Ambassada Yusuf Imam ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da suke taron ƙaddamar da takara da shirin fara gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin mazaɓu 11dake faɗin ƙaramar hukumar. Ogan Boye ya tabbatar da cewa wannan takara da za su yi ba don amfanin kansu ba ne burin su yadda za su taimaki al'ummar…
Read More