Labarai

Fulanin asali ba sa aikata ta’addanci — Sarkin Zazzau

Fulanin asali ba sa aikata ta’addanci — Sarkin Zazzau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce da zaman lafiya aka fi sanin Fulani a Nijeriya ba da ayyukan ta’addanci ba. Sarkin ya yi wannan jawabi ne a wajen wani bikin al’adu da ƙungiyar bunƙasa al’adu ta Fulani (FUDECO) ta shirya a ranar Asabar. Bamalli, ya bayyana cewa Fulani na asali ba sa ɗaukar AK-47 don cutar da mutane. A cewarsa, abin da ya dace shi ne, Bafulatani ya riƙe sanda da gatari don kula da dabbobinsa. Ya kuma yi kira ga Fulani da su ci gaba da alfahari da al’adunsu da ɗabi’unsu. Ya…
Read More
Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Rauda ta bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma – Isa Safiyanu

Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Rauda ta bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma – Isa Safiyanu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Rauda dake Rangaza da Daraktan makarantar, Imam Muhammad Yakub ya kafa da cewa tana taimakawa domin bada gudunmawa a inganta harkar lafiya a cikin al'umma. Malam Isa Safiyanu Umar mai kula da hada-hadar kuɗi na Kwalejin kimiyyar Lafiya da Fasaha  ta Rauda ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a madadin darakta janar na makarantun Rauda Imam Muhammad Yakub. Ya ce daga manufar kafa makarantar shine don taimakawa al'umma don matso da tarbiyyar yara kusa kan gina su akan samun horo akan  ilimin kula…
Read More
Zanga-zanga: Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen mutum 76 da za ta gurfanar gaban kotu

Zanga-zanga: Gwamnatin Tarayya ta bayyana sunayen mutum 76 da za ta gurfanar gaban kotu

An kama masu zanga-zanga guda 76 a Abuja, Kaduna, Gombe, Jos, Katsina, da Kano, yayin zanga-zangar da aka gudanar daga ranar 1 zuwa 10 ga Agusta, 2024, a sassa daban-daban na ƙasar. Zanga-zangar ta samo asali ne daga matsalar tattalin arziki mai tsanani, wanda ya sa ‘yan Najeriya da dama suka hau tituna don nuna damuwarsu. A wannan lokacin, an ruwaito cewa jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa, sun kama wasu, kuma a wasu lokuta sun harbi masu zanga-zangar. A cikin wata tuhuma mai lamba FHC/ABJ/CS/503/2024, mai ɗauke da kwanan wata 27 ga Satumba, kuma da wakilinmu ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da tsarin ƙin karɓar tsabar kuɗi a hanyar Abuja-Keffi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ƙaddamar da tsarin ƙin karɓar tsabar kuɗi (cashless tolling system) a babbar hanyar Abuja zuwa Keffi. Ministan Ayyuka, Sanata Umaho ya bayyana hakan a ranar Alhamis a lokacin da ya ke ƙaddamar da naɗa kwamitin aikin da kuma ninka hanyar Keffi zuwa Akwanga zuwa Makurdi. Ya ce tsarin, wani shiri ne ƙarƙashin shirin samar da ci-gaba a manyan titina don samar da sufuri mai sauƙi da inganci acikin al'umma. Ministan ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarinsa na farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya tare da fatan kwamitin…
Read More

Shettima ya buƙaci ƴan kasuwa su yi amfani da damar kasuwancin zamani don bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga manyan ƴan kasuwa da su ya amfani da damammaki wajen zuba hannun-jari a ɓangarorin daban-daban don bunƙasa harkar tattali a Nijeriya. Ya ce akwai buƙatar a sanya hannu a ƙananan masana'antu, noma, harkar tattali na zamani, ingantayya da makamantansu. Wata takarda daga Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harakokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha, ta ce harkar zuba hannun-jari na ƙasashen waje da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tsara, ya samu ƙaruwa a ranar Alhamis bayan da ƴan kasuwa da dama daga ƙasar Sweden suka ƙudiri aniyar zuba…
Read More

Yadda shari’a ta zama wasan kwaikwayo bayan rashin sanin inda wanda aka tsare ya ke

DAGA BELLO A. BABAJI An samu wani abin mamaki a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bayan da aka nemi babban ma'aikacin kamfanin Binance Holding Limited, Tigran Gambaryan ba a gan shi ba bayan an tsare shi na zaman dakon shari'a wadda aka shirya yi a yau Juma'a. Rahotanni sun bayyana cewa, Mai Shari'a Emeka Nwite na kotun ya ayyana ranar 18 ga watan Oktoba don gurfanar da kamfanin da ma'aikacin kan badaƙalar wasu kuɗaɗe da hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta shigar. A lokacin da aka shirya tsaf don sauraren ƙarar ne, sai aka…
Read More

Kiwon Kaji: Gidauniyar BATN ta tallafa wa mata 200 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gidauniyar 'British American Tobacco Nigeria Foundation', BATN tare da haɗin-gwiwar Ma'aikatar Noma da Samar da Abinci ta Tarayya da Ma'aikatar Noma da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Zamfara, sun bai wa mata 200 da jariran kajin turawa don inganta shirin kiwon kaji a jihar. A lokacin da ya ke magana a wajen ƙaddamar da rabon kajin a Gusau, babban Manajan BATN, Oludare Odusanya ya ce, gidauniyar ta zaɓo mata 200 ne daga dukkan ƙananan hukumomi 14 dake jihar don su ci gajiyar tallafin. Ya ce kowacce mace za ta karɓi kaji guda 20, buhun abincinsu na…
Read More
Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kwamitoci shida domin aiwatar da manufofin ci gaban Jihar Zamfara

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kwamitoci shida domin aiwatar da manufofin ci gaban Jihar Zamfara

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da gudanar da ayyukan ofisoshin gwamnati bisa ƙa'idojin ingantaccen shugabanci. A ranar Alhamis, Gwamna Lawal ya ƙaddamar da kwamitoci guda shida da aka kafa domin aiwatar da manufofin ci gaban jihar a ɗakin majalisar gidan gwamnati da ke Gusau. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa kwamitocin da aka kafa sun haɗa da: Kwamitin raya al'umma, kwamitin yaƙi da Shaye-shaye, Kwamitin dokar ƙasa da filaye, kwamitin tsare-tsaren ci gaban Zamfara. Sauran kwamitocin sun haɗa da…
Read More

Ɗalibai sun ƙone gidan shugaban makaranta kan zaftare N23m a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI Wasu fusatattun ɗalibai da ke makarantar Kwalejin kiwon lafiya ta Jega a Jihar Kebbi sun ƙona gidan Shugaban Kwalejin, Haruna Sa'idu Sauwa da farfasa motarsa. Ɗaliban sun fara zanga-zangar ne bayan samun batun zargin hukumar gudanarwa ta makarantar na karɓe wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira miliyan 23 daga hannun ɗalibai 250 da ke shirin kammala karatu. Wata majiya ta ce lamarin ya samo asali ne daga wata sabuwar tsangaya da aka ƙirƙiro (Public health) wadda da farko an dangana ta ne da wani sashi da kuma Ƙungiyar Lafiyar Al'umma ta Ƙasa. Kwalejin ta…
Read More

Shugaba Tinubu na kewaya Abuja cikin dare don sanin halin matsin da al’umma ke ciki – Sanata Kalu

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da al'umma ke fuskantar tsadar rayuwa a ƙasar, Sanata Orji Kalu ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sane da halin matsin da ake fama da shi a ƙasar kasancewar ya kan kewaya cikin dare don gani da idonsa tare da ɗaukar matakan daidaita al'amuran taɓarɓarewar harkar tattali. Hauhawar farashi ya ƙaru da kaso 32.7 a watan Satumba, 2024 kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa, NBS ta bayyana. Tun lokacin da aka cire tallafin man fetur da rugujewar darajar Naira ne kayayyaki suka ta yin tashin gwaoron zabi. Sanata Kalu ya ce ba sabon abu…
Read More