Labarai

NASENI ta bada tallafin miliyan N70.5 ga injiniyoyi mata shida

NASENI ta bada tallafin miliyan N70.5 ga injiniyoyi mata shida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar kula da Kayayyakin Kimiyya da Injiniya ta ƙasa NASENI ta hannun kwamitin shugaban ƙasa kan canjin fasaha ta PICTT ta ba da tallafin Naira miliyan 70.5 ga injiniyoyi mata shida. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na NASENI, Olusegun Ayeoyenikan, ya fitar ranar Laraba a Abuja. Mista Ayeoyenikan ya ce an bayar da tallafin ne ga mutane shida da suka yi nasara a ƙarƙashin shirin Deɓeloping Engineering Leaders through Her (DELT-Her), tare da gabatar da shawarwarin da aka ƙaddamar a matsayin wani ɓangare na shirin NASENI na Delta-2.…
Read More
Gwamna Nasir ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 6.4 kan biliyan N7.23 a Argungu

Gwamna Nasir ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kilomita 6.4 kan biliyan N7.23 a Argungu

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi  Gwamnan Jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya ƙaddamar da aikin tagwayen hanyoyi mai tsawon kimanin kilomita  6.4 a kan titin tsohuwar Bypass dake garin Argungu. Da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar da aikin ranar Talatar da ta gabata, Maigirma Gwamna Malam Nasir Idris ya bayyana cewa wannan yana ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe da kuma wani ƙoƙari da wannan gwamnati take yi wajen raya ƙauyuka da birane a faɗin jihar. Ya bayyana cewa aikin hanyar ya haɗa da gina magudanun ruwa da kuma kwalbatoci da kuma sanya…
Read More
NDLEA ta kama ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 115.22 da mutane 149 da ke mu’amula da ƙwayoyi

NDLEA ta kama ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 115.22 da mutane 149 da ke mu’amula da ƙwayoyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar NDLEA reshen jihar Ebonyi ta bayyana cewa ta kama haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 115.226 sannan ta kuma kama mutum 149 da suke da alaƙa da safarar muggan ƙwayoyi a cikin watanni uku a jihar. Shugaban hukumar Peter Ogar ya sanar da haka yayin hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ranar Laraba a garin Abakaliki. Ogar ya ce Jami’an hukumar sun yi wannan kamen daga watan Yuli zuwa Satumba a 2024. Ya ce a tsakanin wannan lokacin hukumar ta kama mutum 82 inda a ciki akwai maza 64 da mata 18 da…
Read More
An tsinci gawarwaki 12 da ake tunani na ‘yan bindiga ne a Abuja

An tsinci gawarwaki 12 da ake tunani na ‘yan bindiga ne a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kauyen Tokulo da ke ƙaramar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja sun shiga ruɗu sakamakon tsintar gawarwaki guda 12 da aka yi a garin da ake tunanin 'yan bindiga ne. Kansilan mazaɓar Igu a yankin, Jerry Alkali ya shaida wa Daily Trust cewa mutane ne suka kira shi da misalin ƙarfe 2 zuwa 3 na daren Litinin, cewa suna ta jin harbe-harbe. Ya ce, "ranar babu wanda ya iya barci. Da safiya da mutane suka fara zuwa tafiya zuwa gona suka fara ganin gawarwaki a wata hanyar tafiya ƙaramar hukumar Kagarko da ke…
Read More
Boko Haram ta fille kan mutum huɗu a Borno

Boko Haram ta fille kan mutum huɗu a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Al’ummar yankin Ngoshe a ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno sun shiga zullumi bayan ƙungiyar Boko Haram ta fille kan wasu mutum huɗu da ta yi garkuwa da su a yankin. Bayan Boko Haram ta saki bidiyon fille kan mutanen — maza biyu da mata biyu — al’ummar Ngoshe sun shaida mana cewa waɗanda aka kashen suna daga cikin mutane bakwai, maza biyu da mata biyar da mayaƙan ƙungiyar suka yi awon gaba da su a yankin a makon da ya gabata. A cikin bidiyon an ji wani shugaban ƙungiyar yana cewa sun yi…
Read More
Gwamnatin Nijeriya za ta raba wa talakawa miliyan 20 tallafin kuɗi

Gwamnatin Nijeriya za ta raba wa talakawa miliyan 20 tallafin kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta ce tana shirin raba wa talakawan ƙasar guda miliyan 20 tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin rayuwa. Ministan kuɗi da tattalin arziki na Nijeriya, Wale Edun ne ya bayyana haka a lokacin babban taron tattalin arzikin ƙasar karo na 30 a Abuja, babban birnin ƙasar. Mista Edun ya ce gwamnatin za ta yi amfani da ribar da ta samu a watanni shidan farko na shekarar 2024 wajen raba tallafin, domin inganta rayuwar talakawan ƙasar da ke fama da matsin rayuwa. A jawabinsa na bikin zagayowar ranar 'yancin kai na 1 ga…
Read More
Babu wani yunƙuri da ake na tsige ni —  Akpabio

Babu wani yunƙuri da ake na tsige ni —  Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio, ya ce rahotannin da ke nuni da cewa hukumar tsaro ta DSS ta karɓe ikon majalisar don hana wani shirin tsige shi ba gaskiya ba ne. Rahotannin sun ce jami’an tsaro sun mamaye dukkan ƙofofin shiga ginin majalisar a ranar Laraba. TheCable ta rawaito cewa da ya ke magana a zauren majalisar dattijai, Akpabio ya ƙaryata rahotannin a matsayin “labaran ƙanzon kurege”. Shugaban na majalisar dattijai cikin raha ya ce masu yaɗa wannan labari na iya neman samun kuɗaɗen shiga daga yawan yaɗuwar labarin a shafukansu na yanar gizo.…
Read More
Ranar masu taɓin hankali: Dokta Paul Agbo ya buƙaci a riƙa kula da ma’aikata 

Ranar masu taɓin hankali: Dokta Paul Agbo ya buƙaci a riƙa kula da ma’aikata 

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yayin da duniya baki ɗaya suke gudanar da bukukuwan bikin ranar masu taɓin hankali wato World Mental Health Day a Turance na 2024, Dr. Paul Agbo wanda shi ne shugaban sashin kula da masu taɓin hankalin na Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Lafiya babban birnin jihar Nasarawa ya buƙaci ƙarin albashi wa ma'aikata a duka matakai don ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya yi kiran ne jim kaɗan bayan wani zagaye na musamman don tunawa da ranar ta masu taɓin hankalin wanda sashin ta shirya ta gudanar a…
Read More
Muna bai wa harkar tsaro kulawa ta musamman a Fagge – Abdullahi Gwarzo

Muna bai wa harkar tsaro kulawa ta musamman a Fagge – Abdullahi Gwarzo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD rahim a Kano Jami'in riƙo kuma daraktan mulki na ƙaramar Hukumar Fagge, Kwamared Abdullahi Gwarzo ya bayyana cewa kula da harkar tsaro na da mutuƙar muhimmanci a rayuwa "wanda idan babu tsaron ba zaman lafiya idan ba zaman lafiya ba mulki kuma babu al'umma." Ya ce don haka ne ma suka bai wa harkar tsaro kulawa dpn haka abinda ya soma shine ganawa da masu ruwa da tsaki kan tsaro na ƙaramar hukumar don samun rahoto na halin da ake ciki a kowane lungu da saƙo da abinda ya kamata a yi hakan tasa suka ɗauki mataki…
Read More