Labarai

Sojoji sun hallaka ‘yan fashin daji biyu da suka zo ɗaukar kuɗin fansa

Sojoji sun hallaka ‘yan fashin daji biyu da suka zo ɗaukar kuɗin fansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sojoji sun harbe 'yan fashin daji guda biyu har lahira a yayin da suka yi yunƙurin karɓar kuɗin fansa na Naira 1.5 na mutane 4 da suka yi garkuwa da su a ƙauyen Mai-Iddo dake ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna. Daily Trust ta rawaito cewa rahotanni sun bayyana cewa mutanen da aka yi garkuwa da su sun haɗa maza 3 da ƙaramin yaro ɗaya da aka sace su makon da ya gabata. Wani shugaban al'umma a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust. Ya ce, an kashe 'yan fashin dajin…
Read More
An naushe wani mutum wajen rabon faɗa ya mutu a Adamawa

An naushe wani mutum wajen rabon faɗa ya mutu a Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani mai suna Markus Dali mazaunin Sina Kwande a ƙaramar hukumar Michika a jihar Adamawa ya rasa ransa yayin da ya ke ƙoƙarin rabon faɗa tsakanin wasu mutane biyu. Lamarin ya faru ne a ranar 30 ga watan Agusta lokacin da Dali ya shiga tsakanin Barka Yama da Aleɗ Z. Tari domin ya raba su faɗa. Daily Trust ta tattaro cewa Barka ya kawo naushi sai ya samu Dali wanda hakan ya sa ya faɗi sumamme, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibiti. An kama wanda ake zargin mai shekaru 32, Barka,…
Read More
Dole ne Arewa ta shirya yiwuwar rabuwa, inji Farfesa Lugga

Dole ne Arewa ta shirya yiwuwar rabuwa, inji Farfesa Lugga

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Farfesa Sani Abubakar Lugga, Wazirin Katsina na 5, ya yi kira ga yankin Arewa da su haɗa kai su shirya don cin gashin kansu, kamar takwarorinsu na Kudu. Da yake jawabi a wajen taron wayar da kan al’umma da ƙungiyar haɗin kan Arewa CNG ta shirya a Katsina, Lugga ya jaddada buƙatar ‘yan Arewa su jajirce wajen yiyuwar ɓallewa daga Nijeriya, tare da yin la’akari da kiraye-kirayen ɓallewa daga Kudu. Lugga ya koka da rashin haɗin kai a tsakanin ‘yan Arewa wajen kare ‘yancinsu, inda ya kwatanta hakan da yadda ƙungiyoyi irin su ‘yan…
Read More
JAMB ta bada sharuɗɗan ɗaukar ɗalibai masu ’yan ƙasa da shekaru 18

JAMB ta bada sharuɗɗan ɗaukar ɗalibai masu ’yan ƙasa da shekaru 18

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta JAMB ta ce manyan makarantu za su iya ɗaukar ɗalibai ‘yan shekara 16 a zangon karatu na shekarar 2024/2025 “muddin ƙa’idojin da hukumar ta gindaya sun dace da ɗaliban, amma ba za a iya karɓar ɗalibai ba sai saboda shekaru." A wata takardar da hukumar ta fitar ga cibiyoyi a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, wanda wakilinmu ya samu, hukumar ta buƙaci manyan makarantun da su yi girbi daga tsarin shigar da su na ‘Central Admission Processing System (CAPS), tare da aikewa da jerin…
Read More
PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwarta don bai wa gwamnoni yin matsaya kan Damagum

PDP ta ɗage taron kwamitin zartarwarta don bai wa gwamnoni yin matsaya kan Damagum

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar PDP za ta ɗage taronta na Kwamitin Zartarwa na ƙasa da aka shirya gudanarwa tun da farko a ranar 24 ga watan Oktoba domin bai wa gwamnoni damar cimma matsaya kan hanyoyin siyasa don sauƙaƙa ficewar shugaban riƙo na ƙasa Umar Damagum daga jam'iyyar. Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP na NWC da dama, waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana a kan batun, sun bayyana cewa za a jinkirta taron kwamitin ne saboda gwamnonin da ke ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin na baya-bayan nan da kuma ba da lokaci…
Read More
Wike: Gwamnonin Kudu maso Kudu sun yi barazanar ficewa daga ƙungiyar gwamnoni

Wike: Gwamnonin Kudu maso Kudu sun yi barazanar ficewa daga ƙungiyar gwamnoni

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Gwamnonin yankin Kudu maso Kudu na Nijeriya sun yi barazanar ficewa daga ƙungiyar Gwamnonin Tarayyar Nijeriya (NGF) har ma da ta Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa (NEC) bisa nuna takaicinta dangane da gazawar ƙungiyar ta yi wajen kare muradun 'ya'yanta, musamman ma Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas daga zargin tozartawar Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan da Fubara ya gada, Nyesom Wike. Gwamnonin na Kudu maso Kudu sun nuna matuƙar takaicinsu bisa famkama da nuna isa da suke zargin Wike ya na yi wa gwamnonin PDP, har da shi Gwamna Fubara, don haka…
Read More
Har yanzu kamfanin NNPC ne kaɗai ke sayen fetur daga matatar Ɗangote

Har yanzu kamfanin NNPC ne kaɗai ke sayen fetur daga matatar Ɗangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Har yanzu Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ne kaɗai ke riƙe da ragamar sayen man fetur daga matatar mai na Dangote duk da umurnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a baya-bayan nan na sakar wa sauran ’yan kasuwar mara wajen sayen mai kai tsaye daga matatar. ‘Yan kasuwar man fetur sun bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa, NNPC zai ci gaba da zama shi kaɗai ke sayen mai daga matatar ta Lekki har sai an ƙulla wata sabuwar yarjejeniya da matatar mai ta Dangote. Sai dai ba su bayyana lokacin da yarjejeniyar tsakanin…
Read More
Sarkin Machina ya yaba da salon jagorancin Shettima na ƙarfafa hukumar NEDC

Sarkin Machina ya yaba da salon jagorancin Shettima na ƙarfafa hukumar NEDC

Daga GAMBO ISA Mai Machina, Alhaji Dr. Bashir Albashir Bukar OON, LONN, kuma Sarkin Machina na 77 a jihar Yobe ya yaba da nasarorin da shiyyar Arewa maso Gabas ta samu tun lokacin da aka ƙirƙiro Yobe daga tsohuwar jihar Borno a 1991 zuwa yau. Mai Machina ya bayyana hakan yayin zantawarsa da jaridun Blueprint a Abuja. Sarkin ya yaba da ci gaban da aka samu a fannin shirye-shiryen noma, gina hanyoyin sadarwa da ke kawo shawarwarin jagoranci ga jama'ar yankin Arewa maso Gabas. Mai Machina ya kuma yaba wa, mai girma Gwamna Mai Mala Buni (Chiroman Gujba) da irin…
Read More
Shugaban ƙungiyar masu Keke-Napep na Yobe ya yaba wa Gwamna Buni kan bunƙasa noma

Shugaban ƙungiyar masu Keke-Napep na Yobe ya yaba wa Gwamna Buni kan bunƙasa noma

Daga GAMBO ISA Shugaban ƙungiyar Masu Keke-Napep, Alhaji Umaru Barau a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridun Blueprint a Abuja ya yaba da ɗimbin nasarorin da mai girma gwamnan jihar Yobe ya samu da kuma salon jagorancin Chiroman Gujba a fannin noma, tsarin kula da lafiya a duk faɗin jihar da ƙananan hukumomi 17. Umaru Barau ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni akan himma wajen bunƙasa noma, ƙarfafawa ‘yan ƙasa da masu ƙaramin ƙarfi da kuma mambobin ƙungiyarsa, inda ya buƙaci mambobinsa da su ci gaba da marawa gwamnati baya domin samar da romon dimokuraɗiyya…
Read More
Gaza: Amurka na goyon bayan Isra’ila duk da ƙaruwar kisan ƙare dangi – Abu Shawesh

Gaza: Amurka na goyon bayan Isra’ila duk da ƙaruwar kisan ƙare dangi – Abu Shawesh

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rikicin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai wani matsayi mai matuƙar tada hankali, inda aka kashe Falasɗinawa sama da 42,227, yayin da wasu 98,464 suka jikkata, waɗanda galibinsu mata ns da ƙananan yara, ya zuwa ranar 15 ga watan Oktoba. Halin da ake ciki ya yi muni, inda dubbai suka maƙale a arewacin Gaza, kuma suna fuskantar hare-haren bama-bamai ba dare, ba rana. A cikin wata sanarwar manema labarai, jakadan ofishin jakadancin Falasɗinu a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya yi kira da a shiga tsakani, yana mai jaddada cewa "abu…
Read More