Labarai

Mota mai amfani da gas ta yi bindiga a Edo

Mota mai amfani da gas ta yi bindiga a Edo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu mutane uku sun samu raunuka daban-daban a wata fashewa da wata mota mai amfani da iskar gas ta ‘CNG’ ta yi a gidan man NIPCO da ke Unguwar Eyean a hanyar Benin zuwa Auchi a ƙaramar Hukumar Uhunmwonde a Jihar Edo. Kamfanin Dillancin Labaran iƙna ya ruwaito cewa, ya naƙalto daga shafin Blueprint cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar Alhamis a gidan mai na NIPCO a lokacin da wata mota ƙirar CNG Audi ke cike da iskar gas. An kuma tattaro cewa fashewar ta samo asali ne sakamakon wasu na'urorin sauya…
Read More

Kwanaki 377 da Amurka ke goyon bayan kisan kiyashin Isra’ila akan Falasɗinawa

Daga BELLO A. BABAJI Duk da kashe-kashe da ɗaiɗaita al'umma da dukiyoyi da Isra'ila ke yi akan mutanen Gaza da wasu sassan ƙasar Palestine, hatta hanyoyin shigar da abinci da magunguna ga ƴan Palestine ya zama abin dakatarwa wanda hakan na faruwa ne bisa goyon bayan Amurka, kamar yadda Ambasadan Palestine a Nijeriya, Abdullah Abu Shawesh ya bayyana. "Duniya ta ga hotunan marasa lafiya da waɗanda ke gudun hijira sun fake a kusa da asibitin Al-Aqsa da ƙona su da rai. Mata da yara suna shan wahala tare da tsananin ƙona da su ke fuskanta. Babu wata hanya da gaggawa…
Read More
Shaharren ɗan fim ɗin nan  Olabiyi ya mutu

Shaharren ɗan fim ɗin nan Olabiyi ya mutu

Daga USMAN KAROFI Fitaccen ɗan wasan Nollywood, Ayobami Mudashir Olabiyi, wanda aka fi sani da ‘Bobo B,’ ya rasu. Marigayin ya rasu ne a Ibadan, Jihar Oyo, bayan fama da rashin lafiya na ɗan wani lokaci. An ce an tsara fitowar shi a wani shirin fim da za a yi a Jihar Oyo a watan da ya gabata, amma bai samu damar halarta ba saboda yanayin lafiyarsa. Olabiyi ya kwanta asibitin koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH), Jihar Oyo, inda daga bisani ya rasu a ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024. A cikin wata sanarwa, Akinola ta ce, “Muna baƙin cikin…
Read More
Sanwo Olu ya bayyana Naira  85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Legas

Sanwo Olu ya bayyana Naira 85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Legas

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta fara biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi na N85,000. Sanwo-Olu ya bayyana wannan a daren Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, a shirin da aka yi wa take "One on One with Babajide Sanwo-Olu.” Yayin da aka ambaci batun mafi ƙarancin albashi, gwamnan ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku cewa mafi ƙarancin albashi a Legas, wanda muka tattauna tare da ƙungiyarmu, ya zama N85,000 daga yau. “Ba gasa muke yi ba, don haka ba zan ce muna biyan fiye da…
Read More

Mun dakatar da fafutikar neman tsige Ganduje daga shugabancin APC – Matasan Arewa ta Tsakiya

Daga IBRAHIM HAMISU Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa ta Tsakiya ta ce ta dakatar da fafutukar da ta ke yi ta neman a tsige Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga matsayinsa na shugabancin jam'iyyar APC. Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Hon. Abdullahi Sale Zazzaga ne ya bayyana hakan a wata hira da DCL Hausa ta yi da shi a ranar Laraba. Zazzaga ya ce manyansu ne su ka ja hankalinsu kan su dakatar wannan fafutuka musamman saboda taron kwamatin zartarwa na jam'iyyar da ke ƙaratowa. Zazzaga ya ce, "Komai da ka gani ana yi ne bisa dalili. Siyaysar da mu ke, mu na yi…
Read More

Shugaban JIBWIS na Katsina ya buƙaci mahukunta su kyautata wa mabiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatul-bidi'a Wa Iƙamatus-Sunnah (JIBWIS) na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, ya yi kira shugabanni a dukkan matakai su guji barnatar da dukiyar al'umma kuma su riƙa kyautata wa waɗanda su ke shugabanta. Sheikh Yakubu Musa ya faɗi hakan ne ta wata kafar sadarwa ta ƙungiyar, inda ya ce a wannan lokaci na halin matsin rayuwa, wajibi ne shugabanni a madafun iko da ƴan majalisu da masu wadata su fito da arziƙin da Allah ya basu su tallafa wa mabuƙata. "Ka je kasuwanninmu ko asibitoci ka ga yadda mutane suka tagayyara…
Read More

KILAF ta yi haɗin gwiwa da Gidan Buɗe Ido na Ƙasa a gagarumin bajekolin Kano

Daga BELLO A. BABAJI Tawagar ƙungiyar finafinan Afirka da na yarukan Kano da bukukuwansu (KILAF) ta karɓi baƙoncin wakilan Gidan Buɗe Ido na Ƙasa (NGA) don tattauana batutuwan haɗin-gwiwar da suka alƙanta su. Cikin wata sanarwa da shugaban KILAF, Mista Abdulkareem Mohammed ya fitar, ya ce tattaunawar ta cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu wanda ya gudana ne la'akari da gagarumin taron KILAF da za a yi a daga ranar 25 zuwa 30 ga watan Nuwamba, 2024 a Kano. Shugaban ya ce kawo yanzu KILAF da NGA sum cimma matsayar inganta harkokin al'adu da wasu sana'o'in hannu da al'umma suka dogara…
Read More
Gwamna Lawal ya ba ƙungiyar tsoffin sakatarorin dindindin na Zamfara motar bas

Gwamna Lawal ya ba ƙungiyar tsoffin sakatarorin dindindin na Zamfara motar bas

Daga USMAN KAROFI Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya sanar da cewa Gwamna Dauda Lawal ya ba da gudunmawar motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 ga Ƙungiyar tsoffin sakatarorin dindindin na Zamfara. Idris ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce gwamnan ya cika alƙawarin da ya yi wa ƙungiyar a taron shekara-shekara na bara. A cewar sa, an miƙa motar ga shugabannin ƙungiyar a fadar gwamnati da ke Gusau. Ya ƙara da cewa, “Tun a taron bara, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin samar wa ƙungiyar motar…
Read More
NDLEA ta kama wani mutum ɗauke da hodar ibilis a Katsina

NDLEA ta kama wani mutum ɗauke da hodar ibilis a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar hana sha da fatauci ƙwayoyi NDLEA ta kama wani mutum ɗauke da hodar ibilis mai nauyin 0.642 a kan hanyar Kano zuwa Kankia. Kwamandan hukumar a Katsina Muhammad Aminu Abubakar ya bayyana wa manema labarai haka a ofishin hukumar. Ya ce wanda ake zargi da aikata laifin, ya faɗawa jami'an hukumar cewa yana kan hanyar sa ta zuwa jamhuriyar Nijar. Kwamandan ya ƙara da cewa hukumar na nan na faɗaɗa bincike akan mai laifin da zaran an kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu. Ya yi gargaɗi cewa zai yi amfani da…
Read More
Falana ya umarci Bobrisky ya janye kalaman ɓatanci, ya nemi afuwa cikin awanni

Falana ya umarci Bobrisky ya janye kalaman ɓatanci, ya nemi afuwa cikin awanni

Ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam kuma lauya, Femi Falana, tare da ɗansa Folarin, wanda aka fi sani da Falz, sun nemi Bobrisky ya janye zarge-zargen ɓatanci da ya yi musu, tare da neman gafara cikin sa’o’i 12. Wannan kira ya zo ne a ranar Laraba, bayan wani sautin murya da ke yawo a yanar gizo, inda aka ce fitaccen mai sanya kayan mata, Idris Okuneye (Bobrisky), ya yi zarge-zargen kan su. A tuna cewa, a cikin makon da ya gabata mai sharhi na kafofin watsa labarai, Martin Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya fitar cewa Bobrisky ya…
Read More