Labarai

Yayin da ‘yan Nijeriya ke jiran dawowar Shugaba Tinubu,  Shettima ya lula Sweden

Yayin da ‘yan Nijeriya ke jiran dawowar Shugaba Tinubu, Shettima ya lula Sweden

Daga USMAN KAROFI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ana sa ran zai tashi daga Abuja a ranar Laraba zuwa Sweden a ziyarar kwanaki biyu don wakiltar Najeriya a tattaunawar Ƙasa da ƙasa. Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Ƙasa, ya bayyana a wata sanarwa cewa ziyarar ta kasance ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. “Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa zai dawo gida a ranar Asabar. Yayin da yake Sweden, zai gudanar da tattaunawar Ƙasa da ƙasa tare da manyan jami’an gwamnati, ciki har da ganawa da Amarya Victoria ta Sweden da Firayim Ministan Sweden,” in…
Read More

Yanzu-yanzu: Jagororin NLC da TUC na ganawa da Gwamnatin Tarayya kan tashin farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Jagororin ƙungiyoyin ƙwadago da na kasuwanci (NLC da TUC) na ganawa da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin sakataren gwamnatin kan sabon ƙarin da aka yi wa litar fetur a Nijeriya. Ana gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Sakataren gwamnatin ƙasar, Sanata George Akume wanda musamman don ƙalubalen da hakan ke yi ga al'ummar ƙasa aka shirya shi. Cikin mahalarta zaman akwai; Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu da Ministan Tattali, Wale Edun da kuma Ministar Ƙwadago, Nkeiruka Onyejeocha. Sauran sun haɗa da; Ministan Labarai, Mohammed Idris da ƙaramin Ministan Man…
Read More
‘Yan Majalisa sun nemi a yi gaggawar janye ƙarin kuɗin fetur da gas

‘Yan Majalisa sun nemi a yi gaggawar janye ƙarin kuɗin fetur da gas

Daga USMAN KAROFI Majalisar Wakilai ta fara duba batun ƙarin farashin man fetur da gas a ƙasar nan. Wannan ya biyo bayan ƙudurin da Aliyu Madaki ya gabatar, tare da goyon bayan mambobi 111 na majalisar, inda suka buƙaci a gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da gas ɗin girki. ‘Yan majalisar sun bayyana damuwarsu cewa ƙarin farashin yana jefa ‘yan Nijeriya cikin ƙunci, tare da barazanar rashin aikin yi. Haka kuma, Majalisar ta nemi Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) da ma’aikatar albarkatun man fetur su ƙara ƙarfin tace man fetur a cikin gida, tare da yin kira ga…
Read More

CAF ta sake magantuwa kan badaƙalar wasan Nijeriya da Libiya

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) ta bada sabon umarni game da wasan neman gurbin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka ta 2025 tsakanin Libiya da Nijeriya. A baya ne dai aka bar tawagar Super Eagles a wulaƙance a lokacin da suka je ƙasar Libiya don buga wasan ba tare da marabtar su irin yadda ake yi wa baƙi ba. A ranar Talata ne CAF ta sanar da cewa, ba za a buga wasan ba kamar yadda aka tsara shi inda tace za ta miƙa lamarin ga ofisoshin ƙwararru na hukumar don ji da lamarin. Tun da…
Read More
Dikko Raɗɗa ya raba Naira biliyan uku ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Dikko Raɗɗa ya raba Naira biliyan uku ga waɗanda ambaliyar ruwa ya shafa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mutane 1,067 da ambaliyar ruwan sama ya shafa a jihar Katsina suka amfana da tallafin kuɗi fiye da biliyan uku daga gwamnatin tarayya. Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a wajan bikin bada taimakon kuɗi ga mutanen da ambaliyar ruwan sama ya shafa a Katsina. Ya sanar da cewa mutum 1,067 kwamitin da gwamnati ta kafa ƙarƙashin mataimakin gwamna suka tantance. Malam Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa mutum 439 da gidajen su suka rushe gaba ɗaya suka sami Naira 600.000,sai kuma waɗanda wasu sassan gidajen su ya rushe suka sami Naira 300.000. Haka gwamnatin…
Read More
Mutum 94 sun ƙone Ƙurmus, 50 sun samu munanan raunuka bayan faɗuwar tankar mai a Jigawa

Mutum 94 sun ƙone Ƙurmus, 50 sun samu munanan raunuka bayan faɗuwar tankar mai a Jigawa

Daga ABUBAKAR M TAHEER A jiya Talata da misalin sha ɗaya na dare wata tanka ɗauke da man fetur da ta taso daga Kano zuwa Nguru ta faɗi a kusa da Khajida University Majia. Cikin wata sanarwar gaggawa da jami'an hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sanda ta Jihar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adam ya fitar da safiyar yau, ya bayyana yadda lamarin ya afku. Bayan faɗuwar tankar ke da wuya man ya rinƙa kwarara magudanan ruwa wanda al'ummar garin su ka fito domin kwasar man fetur ɗin, nan take wuta ta kama inda nan take nutum 94 sun ƙone…
Read More

PDP ta dawo da Damagum da wasu jigogin jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake samu rikici acikin babbar jam'iyyar adawa a Nijeriya (PDP), ƙungiyar gwamnonin jami'yyar ta ƙudiri aniyar haɗe kan mambobinta tare da kawar da duk wata saɓani da ake samu a tsakanin su. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Abdulƙadir Bala Muhammad ya bayyana hakan, inda ya ce ya soke dakatarwar da aka yi wa wasu daga cikin ƴaƴan jam'iyyar. Gwamna Bala ya faɗi hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar jim-kaɗan bayan kammala wani taron gaggawa da mambobin PDP a Abuja. Kawo yanzu ana samun raɗeraɗin cewa ba a kai ga warware matsalolin…
Read More

Ku faɗaɗa harkokinku ta hanyar inganta sana’o’in matasa – Shettima ga manyan ƴan kasuwa

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga sabbin daraktocin hukumar zuba hannun-jari ta ƙasa, NSIA da su faɗaɗa guraben zuba hannun-jari don taimaka wa ɓangarorin harkar tattali a Nijeriya. A lokacin da ya ke ganawa da daraktocin a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Shettima ya zayyano ababen da gwamnatin tarayya ta shirya bai wa hukumar don bunƙasa ayyukanta musamman ta fuskar ƙarfi a ɓangaren kuɗi. Ya kuma nuna buƙatar NSIA ta bada tallafi ga harakar tattali a ɓangaren harkar noma da inganta shi, ya na mai kira a gare su da su ɗore…
Read More
NFC ta ƙara nuna aniyarta wajen inganta tsaro na bidiyo da sauti a Nijeriya

NFC ta ƙara nuna aniyarta wajen inganta tsaro na bidiyo da sauti a Nijeriya

Daga USMAN KAROFI NFC ta sake jaddada aniyarta wajen inganta tsaro na zamani da yaƙi da asarar bayanan ƙididdiga a taron shirin ilimi da haɗin gwiwa na Ƙasa da Ƙasa (TNB) na hukumar musayar ilimi ta Jamus (DAAD) da aka gudanar a birnin Berlin. Dr. Ali Nuhu, Manajan Daraktan hukumar NFC, ya gabatar da takarda mai taken "Asarar bayanai da haɗin gwiwar NFC da gwamnatin Jamus da hukumominta," inda ya ja hankalin mahalarta taron tare da gabatar da muhimman shirye-shiryen haɗin gwiwa da NFC ke gudanarwa, ciki har da dabaru na zamani da ake aiwatarwa don kare bayanan kididdiga na…
Read More
Gyaran rumbun lantarki na ƙasa ya kusa kammala – Hukumar TCN

Gyaran rumbun lantarki na ƙasa ya kusa kammala – Hukumar TCN

Daga USMAN KAROFI Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa gyaran rumbun lantarki wanda ya faɗi a ranar Litinin yana ci gaba kuma ya kusan kammala. A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Manajan hulɗa da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya bayyana cewa babban rumbun lantarki na ƙasa ya fuskanci matsala a ranar Litinin, 14 ga Oktoba, 2024 da misalin ƙarfe 6:48 na yamma. “Sanarwar ta ce duk da cewa an fara dawo da tsarin wutar nan take, tare da tashar wutar lantarki ta Azura, an samu ci gaba wajen dawo da tsarin wutar da misalin…
Read More