04
Sep
Shugaban rukunin Kamfanin Ɗangote, Aliko Dangote da Shugaban gidauniyar Bill and Melinda Gates, Bill Gates na daga cikin waɗanda suka halarci taron majalisar tattalin arzikin Ƙasa (NEC) a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Shugaban majalisar, Kashim Shettima ne ya jagoranci taron a cikin zauren majalisar. Kasancewarsu a taron bazai rasa nasaba da ƙoƙarin da gidauniyar su ke yi na kawo ƙarshen cutar Polio a Nijeriya ba. Haka kuma a wajen taron akwai gwamnoni kamar su Babagana Zulum na Jihar Borno, Bala Mohammed na Bauchi, Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa, Duoye Diri na Bayelsa, Francis Nwifuru na Ebonyi, Lawan Dauda…
