Labarai

Mele Kyari ya yi gum yayin da gidajen man NNPCL suka ɗaga farashin lita zuwa N855

Daga BELLO A. BABAJI Akwai manyan alamu da ke nuna cewa kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya umarci rassansa su mayar da farashin litar mai zuwa Naira 855. A ranar Talata ne aka ga gidajen man sun sauya farashin litar mai daga N600 zuwa N855 inda wasu ke cewa an samu umarnin ƙara farashin ne ga gidajen man. Umarnin ya sanar da cewa hukumar gudanar da gidajen man ta yi kwaskwarima ne wa farashin mai a dukkan rassansa. Haka na zuwa ne kwana biyu da kamfanin ya sanar da cewa ya na fuskantar matsaloli a yayin shigo da man…
Read More

‘Yan adaidata sahu sun fara zanga-zangar tsadar man fetur a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Ɗaruruwan ƴan adaidata sahu ne suka yi cincirindo a titunan cikin garin Kano a ranar Talata inda suke nuna rashin jin daɗinsu game tashin gwaoron zabi da farashin man fetur yayi a Nijeriya. A wasu wuraren akan samu litar mai har akan N1,200 wanda har ta kai ga gidajen mai na Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL a Kano suka sauya farashinsu zuwa N904 duk lita ɗaya. Zanga-zangar, wacce aka gudanar a yankin gadar Dangi sakamakon fusata da ƴan adaidatar suka yi, ta haifar da cinkoson ababan hawa wanda har ta kai ga an shafe tsawon…
Read More
‘Yan Majalisar Dattijai sun kai ziyarar ta’aziyar Hajiya Dada a Katsina

‘Yan Majalisar Dattijai sun kai ziyarar ta’aziyar Hajiya Dada a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar dattawan Nijeriya ƙarƙashin mataimakin majalisar sanata Barau Jibrin, ya jagoranci ziyarar ta'aziya na mutuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua a Katsina. Marigayiyar Hajiya Dada Musa Yar'adua ita ce kuma mahaifiya ga marigayi Shehu Musa Yar'adua da shugaban kwamitin harkokin soja a majalisar dattijai sanata Abdulaziz Musa Yar'adua. Sanata Barau Jibrin ya yi addu'a Allah yafe mata kura kuran ta ya albarkaci abinda ta bari. Ya kuma shawarci sanata Abdulaziz Musa Yar'adua da ya ɗauki mutuwar ta a matsayin sa na musulmida babu wanda zai wuce lokacin sa. Ya bayyana Marigayiya…
Read More

Shettima, Atiku da wasu gwamnoni sun halarci jana’izar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’adua

Daga UMAR GARBA a Katsina An gudanar da sallar jan'izar Hajiya Fatima Dada, mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar Najeriya marigayi Mallam Umaru Musa 'Yar'adua kamar yadda addininin musulunci ya tanada a yau Talata. An binne marigayiyar ne a kusa da kabarin tsohon shugaban 'yar'adua a maƙabartar ɗan marna da ke cikin garin Katsina. Manyan baƙi a ciki da wajen jihar Katsina da suka haɗa da Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima; Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa; ƴan siyasa da sarakunan gargajiya da dai sauransu duk sun samu damar halartar sallar janazar. Blueprint Manhaja ta rawaito…
Read More
An yi jana’izar Hajiya Dada Musa Yar’adua

An yi jana’izar Hajiya Dada Musa Yar’adua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Dubun duba tan mutane daga ciki da wajan Jihar Katsina suka halarci jana'izar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua duk da ruwan sama da akai ta yi. Jana'izar da ta gudana a filin wasa na cikin garin Katsina kusa da gidan marigayiyar a unguwar Yar'adua da misalin ƙarfe 2.20pm na yammacin talata Sheikh Aminu Ibrahim yammawa ne ya jagoranci sallar. A cikin waɗanda suka halarci jana'izar akwai mataimakin shugaban ƙasa Kashim shattima da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa. Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan…
Read More

Ɗangote ya yaba wa Tinubu bisa umarnin cinikin mai da Naira

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yaba wa Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, bisa bayar da umarnin a riƙa cinikayyar man fetur da kuɗin Naira maimakon Dala. Ɗangote, wanda ya bayyana haka a ranar Talatar nan lokacin da ya ke ƙaddamar da fara saye da sayarwar fetur daga matatar tasa a Legas, ya ce hakan zai rage buƙatar Dala da kashi 40 cikin 100, inda hakan ke nufin farfaɗowar darajar Naira da sama ma ta daidato a kasuwar shunku. A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a harabar matatar…
Read More
NNPCL ta ƙara kuɗin mai zuwa N855 duk lita

NNPCL ta ƙara kuɗin mai zuwa N855 duk lita

Kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin man fetur. Ko wacce lita za ta koma N855 daga N615 a faɗin ƙasa. A na sa ran wannan ƙarin farashin zai yi tasiri mai yawa a kan tattalin arziki, wanda zai shafi komai tun daga farashin sufuri zuwa farashin kayayyaki a faɗin ƙasar. Zuwa yanzu Kamfanin bai bayar da wata sanarwa a hukumance ba da ya sanya wannan ƙarin.
Read More
Akwai ladan miliyan N20 ga bada bayanin inda ɗan Birtaniya ya ke – ‘Yan sandan Nijeriya

Akwai ladan miliyan N20 ga bada bayanin inda ɗan Birtaniya ya ke – ‘Yan sandan Nijeriya

Rundunar ƴan sanda ta ƙasa a ranar Litinin ta bada sanarwar ladan miliyan N20 ga duk wanda ya bada bayanai in da za sami ɗan ƙasar Birtaniya Andrew Wayne da Lucky Ehis Obiyan kan zargin ɗaukar nauyin ta'addanci a cikin Nijeriya. Wannan sanarwa na ɗauke ne a wata sanarwa ta musamman da rundunar ta fitar ga ƴan jarida a hedikwatar rundunar da ke Abuja. " Duk wanda ya gansu, ya miƙa su zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa ko kuma ya kira lambobi kamar haka "08035179870, 09133333785, 09133333786. Da yake magana da ƴan jarida, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar…
Read More
DA ƊUMI-ƊUMI: Matatar Ɗangote ta gama shirin fara sayar da fetur a gidajen mai

DA ƊUMI-ƊUMI: Matatar Ɗangote ta gama shirin fara sayar da fetur a gidajen mai

Matatar mai ta Ɗangote za ta fara siyar da mai ga gidajen mai na ƙasa. Shugaban kamfanin Ɗangote, Alh Aliko Ɗangote ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Talata. Ya cigaba da cewa fara bayar da man cikin gida zai rage yawan dogaro da man ƙasar waje da kuma rage dogaro da Dala. Ya cigaba da cewa man da matatar ta shi za ta samar sai gogayya da kowanne iri a duniya wajen inganci da kyau. Hakan zai gudana nan ba da jimawa ba da zarar kamfanin ya gama tattaunawa da kamfanin NNPC
Read More

Shugaba Tinubu ba ya ɗaukar ƙalubalen tsaro da wasa – Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya sassaci game da ƙalubalen da ake fuskanta a lamuran tsaro a Nijeriya. Shettima ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin shugabannin gidan labarai na News Agency Nigeria (NAN) a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Ya ce, akwai buƙatar haɗin-gwiwa na shiyyoyi da kuma al'ummar yankunan don warware matsalolin da taɓarɓarewar tsaro ta haifar a yankin Afirka ta Yamma. Ya kuma yi nuni da yadda hakan yayi tasiri a Nijeriya da ƙasashen da take maƙoftaka da su inda gidajen jaridu…
Read More