Labarai

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’adua

Daga Umar Garba a Katsina Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Hajiya Dada, mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Umaru Musa Yar'adua. A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, shugaba Tinubu ya nuna alhininsa bisa rasuwar dattijuwar mai shekara 102 a duniya. Tinubu ya kuma miƙa saƙon ta'aziyya ga Sanata Abdulaziz Yar’Adua da ɗimbin iyalan marigayiyar da ma al'ummar jihar Katsina baki ɗaya. Hajiya Dada, mahaifiyar marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar’adua, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Shehu Musa Yar'adua da kuma Sanatan Katsina ta tsakiya, Abdul'aziz…
Read More

Osimhen ya amince da ficewa daga Napoli a matsayin ɗan wasan aro

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan wasan Super Eagles da ke ƙungiyar Napoli ta ƙasar Italiya, Victor Osimhen ya amince da koma wa ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya a matsayin ɗan wasan aro. Fabrizio Romano, wanda ƙwararren ɗan jaridar harkar ƙwallon ƙafa ne ya ruwaito a shafinsa na X da facebook inda ya ce hakan na zuwa ne bayan da wakilan Galatasaray suka tattauna da Osimhen a safiyar ranar Litinin. Adadin da Napoli ta sanya akan ɗan wasan da farko ya kai Euro miliyan 130 wanda daga baya ya nemi kuɗin ya dawo Euro 75, amma hakan bai sa ƙungiyar ta sallama…
Read More
Zanga-zanga a Abuja saboda ƙarancin fetur

Zanga-zanga a Abuja saboda ƙarancin fetur

Wasu masu zanga-zanga sun fito a jiya Litinin a babban birnin tarayya Abuja suna masu kira da a kori shugaban kamfanin NNPCL Mele Kyari a dalilin wahalar mai da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Zanga-zangar na zuwa ne daidai lokacin da kamfanin ke sanar da barazanar rashin kuɗi da ke damun shi. Wanda a sanadiyar haka ne, kamfanin ya ce harkokin shigo da man fetur na samun cikas. Babban lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana ya bayyana cewa wannan matsin rayuwar ya ta'azzara domin ko titi ka fita za ka kula ba ababen hawa sosai…
Read More

Mahaifiyar tsohon Shugaban Ƙasa Yar’adua, Hajiya Dada ta rasu, za a yi jana’iza gobe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Allah ya yi wa mahaifiyar tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Dada, rasuwa da yammacin nan na Litinin, 2 ga Satumba, 2024. Ta rasu da yammacin nan a gidanta da ke unguwar Yar'adua cikin birnin Katsina. Cikin manyan ƴaƴanta dai akwai tsohon Babban Hafsan Sojojin Nijeriya kuma Mataimakin Shugaban Gwambatin Mulkin Soja a lokacin tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Olusegun Obasanjo, Marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua da tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Malam Umaru Musa Yar'adua da Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua. Za a yi jana'izarta gobe Talata da ƙarfe 1:30 na rana a gidanta…
Read More

Nazari: Babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya don inganta ci gaba

Daga MARYAM RABI'U Taron Majalisar Ɗinkin Duniya na nan gaba wani lamari ne mai ban sha'awa wanda ya jawo hankalin shugabannin duniya, sanannun masana, da masu fafutuka don tunkarar wasu manyan ƙalubale na zamaninmu. Taron wanda ake yi a shalkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya dake Birnin New York na Ƙasar Amurka na da nufin ba da damar samar da hanyoyin da za a iya aiwatar da su, wadanda ke inganta makomar duniya mai ɗorewa, daidaito da kuma lumana. Ta hanyar tattara muryoyi daban-daban, taron ya na haɓaka cikakkiyar magana kan sarrafa sarƙaƙiya na duniyarmu da ke ƙara samar da haɗin-kai. A wannan shekara,…
Read More
Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin da zai binciko tashin gobara a gidan gwamnatin Katsina

Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin da zai binciko tashin gobara a gidan gwamnatin Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina ya kafa kwamitin da zai gaggauta bincikar dalilin tashin gobara a wani sashe na gidan gwamnatin jihar a Katsina. Gobarar da ta tashi a sanyin safiyar Litinin, ta lalata ƙaramin ɗakin taro da ke kusa da ofishin Gwamnan jihar. Sai dai jami'an kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jiha sun yi ƙokari wajen daƙile wutar kada ta bazu zuwa sassan gidan gwamnatin. A cikin wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Yar'adua, daraktan yaɗa labaran ofishin sakataren gwamnatin jihar ya sanya wa hannu, ta ce an ɗora wa kwamitin alhakin gano dalilin tashin…
Read More

COPAN ta yi tir da yunƙurin kifar da gwamnatin Tinubu da ɗan Birtaniya ya yi

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ƴan kishin Ƙasa ta COPAN ƙarƙashin jagorancin Barista Uchenna Odielli ta yi alla-wadai da yunƙurin da wani ɗan Burtaniya mai suna Andrew Wynne Povich da aka sani da Free Povey ya yi na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Bayan zurfin bincike da ƴan sanda suka yi, sun shelanta neman sa ruwa a jallo kan ɗaukar nauyin wasu mutane a Nijeriya don nakasa ƙasar ta hanyar haddasa tashin-tashina, zanga-zanga da makamantansu. Cikin wata takarda da COPAN ta fitar a ranar Litinin, ta ce duk wani yunƙuri na kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin da aka kafa daga…
Read More

Ministan Labarai ya wakilci Tinubu a taron ƙasashen Afirka da Indonesiya a Bali

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Labarai da Haɗin-kan Ƙasa, Idris Mohammed zai wakilci Shugaba Bola Tinubu a matsayin jagoran tawagar Nijeriya a taron ƙasar Indonesiya na Afirka karo na biyu wanda za a yi a Bali daga ranar 1 zuwa uku ga watan Satumba, 2024. Mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabi'u Ibrahim cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce za a yi taron ne don ƙarfafa ayyukan da Indonesiya ke son cimmawa zuwa shekarar 2045 da kuma na Afirka a 2063. Ya ce, akwai kyakkyawar fahimta da alaƙa mai ƙarfi a tsakanin Nijeriya da Indonesiya…
Read More

Sojoji sun kashe shahararren ɗan ta’adda da mutanensa a Kaduna

Daga BELLO A BABAJI Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) ɓangaren jami'ai na musamman sun yi nasarar kashe sanannen ɗan ta'adda mai suna Mustapha Abdullahi da wasu mambobin tawagarsa guda biyar a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna. Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, AVM Edward Gabkwet acikin wata sanarwa da ya fitar yace, an tura jami'an ne daga rundunar kariya ta 413. Ya ce, an samu nasarar ne sakamakon wani rahoton sirri da suka samu a ranar 31 ga watan Agusta kan cewa an ga ɗan ta'addan da tawagarsa a yankin dajin Sabon Gida, kan hanyar Sabon Birni.…
Read More

‘Yan ta’adda sun kashe mutane tare da ƙone gidaje da shaguna a Yobe, inji ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Wasu ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi tare da ƙone wasu shaguna da gidaje a ƙauyen Mafa da ke ƙaramar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe. Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana hakan a Damaturu, babban birnin jihar, a ranar Litinin inda ya ce kawo yanzu ba su tabbatar da adadin rayukan da aka rasa ba. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 4 na yamma a ranar Lahadi inda wasu mutane biyu daga cikin mazauna yankin suka sanar da rundunar ƴan sandan. Shaidun…
Read More