Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta aika masu zanga-zangar matsin rayuwa gidan kaso na Kuje

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta aika masu zanga-zangar matsin rayuwa gidan kaso na Kuje

Wasu daga cikin masu zanga-zangar mastin rayuwa da aka gudanar a watan da ya wuce an tura su gidan kaso na Kuje. Mai shari'a Emeka Nwite na babbar kotun da ke Abuja ya yanke wannan hukuncin bayan da aka tuhume da cin amanar ƙasa. Mai shari'an ya bayyana zai fara sauraren belin su ranar 11 ga watan Satumba 2024. Wannan ya biyo bayan zargin su da ake da cin amanar ƙasa da ƙoƙarin tada zaune tsaye. Mutum goma da su ka bayyana gaban kotu sun haɗa da Micheal Adaramoye wanda a ka fi sani da Lenin, Adeyemi Abayomi, Suleiman Yakubu,…
Read More

‘Yan sanda na neman ɗan ƙasar Birtaniya ruwa a jallo bisa zargin kitsa kifar da gwamnatin Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar ƴan sanda ta shelanta neman wani ɗan Burtaniya mai suna Andrew Wynne kan zarginsa da kitsa kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. An gano cewa rundunar ta gudanar da wani bincike kan yadda wasu ƴan ƙasashen waje suka kitsa kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Nijeriya. Mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya faɗi haka a hedikwatar rundunar da ke Abuja inda ya ce ɗan Burtaniyan ya karɓi hayar waje ne a 'Labor House' da ke Abuja inda a nan ya ke ayyukansa na zamba cikin aminci yayin da ya fakewa da sunan gudanar da harkokin…
Read More
Motocin yaƙi da ‘yan ta’adda suka ƙona an bar su ne lokacin da suka lalace – Hedikwatar Tsaro

Motocin yaƙi da ‘yan ta’adda suka ƙona an bar su ne lokacin da suka lalace – Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar tsaro ta fito ta bayyana cewa motocin yaƙi da 'yan ta'adda su ka ƙona a wani faifan bidiyo dama sun lalace ne. Wannan ya fito a wani bayani da daraktan yaɗa labarai na tsaro Manjo Janar Edward Buba a ranar Litinin. Buba ya ce, ma'aikatan "Operation Hadarin Kaji" a ranar 29 ga Agusta a yayin da suke wani sintiri a ƙauyen Kwashabawa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara. Ya bayyana motocin sun lalace ne a wannan hanyar saboda faɗawa da su kai cikin taɓo. Buba ya cigaba da faɗa cewa sannan wani faifan bidiyo da ke yawo yana…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N30 a harkar tsaro cikin shekara ɗaya

Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N30 a harkar tsaro cikin shekara ɗaya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin Gwamna Dikko Raɗɗa ta kashe Naira biliyan 30 a cikin shekara ɗaya da watanni uku kan harkar tsaro. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Dr Nasir Mu'azu Ɗanmusa ne ya faɗi haka a taron masu ruwa da tsaki na shiyyar Funtuwa da Gwamna Raɗɗa ya jagoranta. Kwamishinan ya bayyana cewa, a duk wata gwamnatin jihar na bai wa ƙananan hukumomin da rashin tsaro ya shafa Naira Miliyan uku, domin sayen man fetur na sintiri. Ya yi cikakken bayani akan halin da suka sami jihar akan matsalar ta'addanci da ƙokarin da gwamnatin…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina

Da Ɗumi-Ɗumi: Gobara ta tashi a gidan gwamnatin Katsina

Wata gobara ta kama a wani sashen gidan gwamnatin Jihar Katsina. Sashen da ya kama inda gwamnan jihar ke ganin manyan baƙi na musamman. Rahoton da Manhaja ta samu ya nuna cewa, gwamnan jihar Dikko yana Funtua ziyarar aiki a lokacin da lamarin ya faru. Har yanzu ba a san dalilin da ya sa wutar ta kama ba, kawo yanzu a na ta ƙokarin ganin cewa a kashe ta. Sauran bayanai na zuwa…
Read More

‘Yan sandan Kanada sun kama ƴar Nijeriyar da ta yi barazanar saka wa Yarabawa guba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan sanda a jihar Toronto da ke ƙasar Kanada sun kama wata ƴar Nijeriya mai suna Amaka Sonnberger da ke zaune a ƙasar wacce ta yi barazanar sanya guba wa al'ummar Yarbawa da Benin. An kama matar ne mai shekaru 46 a ranar Lahadi bayan bincike da aka gudanar kan saƙon da ta yaɗa a yanar gizo a ranar 25 ga watan Agusta wanda ke ɗauke da barazana ga wasu keɓaɓɓun mutane a Nijeriya. Ƴan sandan sun gabatar da matar ne a kotu a ranar 2 ga watan Satumba inda ake tuhumar ta da laifin furta…
Read More

Likitoci sun koma bakin aiki bayan yajin aikin gargaɗi

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar likitocin Nijeriya (NARD), ta umarci mambobinta su dawo bakin aiki bayan shafe mako guda ana yajin aikin gargaɗi. An fara yajin aikin ne don nuna damuwa kan sace wata likita mai suna Dakta Ganiyat Popoola da aka yi watanni takwas da suka gabata. Duka da cewa sun koma bakin aiki, ƙungiyar ta ce za su yi nazari kan ƙoƙarin gwamnatin tarayya wajen amsa buƙatunsu acikin makonni uku. Dakta Popoola wata likita ce da ke aiki a Asibitin Ido na Ƙasa da ke Kaduna wacce aka yi garkuwa da ita tare da mijinta da wani ɗan…
Read More

Yau za a fara shari’ar masu zanga-zanga a wasu manyan jihohin Arewa

Daga BELLO A. BABAJI A yau ne ake fara shari'ar masu zanga-zanga a jihohin Abuja, Kano, Kaduna da Borno, inji Mataimakin Sufeton ƴan sanda (DIG) ɓangaren Leƙen Asiri, Dasuƙi Galadanchi. Mataimakin Sufeton ya faɗi haka ne a yayin taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) inda ya ce mutane 126 da aka kama za a gurfanar da su gaban kotu waɗanda ake zargin su da ɗaga tutar ƙasar Rasha da ke nuna buƙatar sauya Gwamanti a lokacin zanga-zangar wacce ta canja salo zuwa tashin-tashina da mace-macce gami da satar dukiyoyin ƙasa da ta al'umma. Lauyan kare ƴancin Ɗan-adam Femi Falana tare…
Read More

An yi wa Tinubu da shugabannin Afrika shimfiɗar fuska a Chana

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Litinin ne ƙasar Chana ta buɗe ƙofar ƙarfafa alaƙa tsakaninta da shugabannin ƙasashen Afirka don bunƙasa ayyukan ci gaba a Nahiyar Afirka a wani taron da aka yi wa laƙabi da Chan-Africa. A makon nan ne ƙasar wani rahoton gidan jarida na ƙasar Beijing ya ce taron haɗin-gwiwa na China-Africa zai zama babban fagen harkokin difulomasiyya tun lokacin annobar COVID-19 wanda ake tsammanin wakilci da dama daga ƙasashe daban-daban. Ƙasar Chana ta aika da dubunan ma'aikata zuwa Afirka don gina manyan ayyukanta musamman a ɓangaren albarkatun ƙasashen. Yawaitar adadin kuɗaɗen aro da Chana ka…
Read More
Yadda ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona a Neja da Kebbi

Yadda ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona a Neja da Kebbi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ambaliyar ruwa ta lalata amfanin gona a ƙaramar Hukumar Argungu da sauran yankunan da abin ya shafa a jihohin Kebbi da Neja. Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar Raya Wutar Lantarki ta ƙasa (N-HYPPADEC), Nura Wakili ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, yayin da yake jajantawa manoman da iftila'in ya shafa. Hukumar ta ce tana kallon lamarin a matsayin wani gagarumin koma baya ga ƙoƙarin da al'ummar ƙasar ke yi na samar da ɗorewa da tabbatar da abinci. Sanarwar ta ce, Manajan Daraktan Hukumar, Abubakar Yelwa, ya nuna matuƙar…
Read More