02
Sep
Wani tulu da aka yi imanin ya kai shekara 3,500 a duniya ya gamu da ajalinsa bayan wani ƙaramin yaro ya fasa shi a wani gidan ajiyar kayan tarihi da ke Isra'ila. Gidan tarihin na Hecht Museum ya bayyana cewa an ƙera tulun ne tsakanin shekarun 2200 zuwa 1500 kafin haihuwar Annabi Isa - kuma ta musamman ne saboda ba abin da ya same shi. A buɗe yake ba a cikin gilashi ba kuma a kusa da ƙofar shiga wurin. Masu wurin sun ce tsautsayi ne kuma ma har an sake gayyatar yaron da iyayensa domin zagayawa da su cikin…
