Labarai

Mawaƙin adabin siyasa Garba Gashuwa ya rasu

Yau Lahadi, 1 ga watan Satumba, 2024 Allah Ya yi wa shahararren mawaƙin adabi na siyasa, Alhaji Garba Gashuwa, rasuwa. Jana'iza ƙarfe 10 na safe a gidan sa da ke Sheka, a jihar Kano. Alhaji Garba wani shaƙiƙi ne ga shahararren mawaƙin nan mazaunin Kaduna, Alhaji Musa Ɗanbade. Allah ya rahamshe shi, amin.
Read More

Tinubu zai yi tankaɗe da rairaya a gwamnatinsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu na shirin yin tankaɗe da rairaya wa ma'aikatan gwamnatinsa a ƙoƙarinsa na inganta ayyukansa wa al'ummar Nijeriya. Shugaba Tinubu na samun matsi daga ciki da wajen jam'iyyarsa ta APC kan neman ya tsige wasu ministoci da ba sa ayyukansu yadda ya kamata. A shekarar da ta gabata ne Tinubu ya naɗa kwamitin karɓar rahoton ayyukan ministoci da wasu manyan jami'an gwamnatinsa ƙarƙashin jagorancin Mai bashi Shawara ta musamman kan tsara shirye-shirye, Hadiza Bala Usman. Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka bai wa muƙami na minista ko…
Read More
Gwamatin Tarayya za ta zuba jarin Dala Biliyan 4.8 a kiwon lafiya – Shettima

Gwamatin Tarayya za ta zuba jarin Dala Biliyan 4.8 a kiwon lafiya – Shettima

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na shirin zuba jari na zunzurutun kuɗi Dala Biliyan 4.8 a fannin kiwon lafiya a faɗin ƙasar.Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin da yake ƙarin haske kan sauye-sauyen da gwamnatin ta yi a fannin kiwon lafiya wanda a cewarsa, zai lashe sama da dala biliyan 4.8 wajen zuba jari duk a yunƙurin gwamnati na ganin an farfaɗo da ingancin kiwon lafiya a Nijeriya tare da magance Ƙalubalen da ya jima yana addabar ɓangaren kiwon lafiyar.Shettima ya bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da rukunin…
Read More

Minista ya umarci shugabannin sojoji su ƙaura zuwa Sakkwato don shawo kan taɓarbarewar tsaro a Arewa-maso-Yamma

Daga BELLO A. BABAJI A cigaba da ƙoƙarin shawo kan matsalolin taɓarɓarewar tsaro a Arewa-maso-Yammacin Nijeriya, ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya umarci shugaban Ma'aikatan Tsaro da wasu manyan jami'an tsaro su sauya sheƙa zuwa jihar Sakkwato. Umarnin wani ɓangare ne na faɗaɗa ayyukansu don kawo ƙarshen ta'addanci da sace-sace da ke addabar yankin. Ministan ya nuna damuwa sosai kan yadda ƴan ta'adda ke tada-zaune-tsaye musamman a jihohin Sakkwato, Zamfara, Katsina da Kebbi. Ya ce, yayin kasancewar shugabannin tsaron a Sakkwato, za su mayar da hankali wajen ayyukan ƴan ta'addar musamman kan dakatar da ayyukan shahararren ɗan ta'adda, Bello Turji…
Read More

IPC ta caccaki gwamnatin Kano kan tsare ɗan jarida bisa tuhumar ɓata suna

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Cibiyar labarai ta ƙasa-da-ƙasa (IPC) reshen jihar Legas, a ɓangarenta na kula da bada kariya ga ƴan jarida (SPJ) tayi matuƙar nuna damuwarta kan tura wani ɗan jarida da ke aiki da Pyramid a jihar Kano Muktar Ɗahiru zuwa gidan yari. An kama Ɗahiru tare da tsare shi ne sakamakon yaɗa bayanai da gwamnatin jihar ta bayyana su a matsayin laifi. SPJ yace, ƴan sanda sun kama ɗan jaridar ne a ranar 29 ga watan Agusta, 2024 kan yaɗa wani saƙo a shafinsa na Facebook. Rahoton da aka samu daga SPJ ya nuna cewa, an kai…
Read More
Sarkin Katsina zai naɗa Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina

Sarkin Katsina zai naɗa Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Nan da makwanni uku mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman zai naɗa shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar wakilai Abdullahi Aliyu sarautar Duhuman Katsina. Bayanin haka kuwa ya fito ne a wata takarda dauke da sa hannun mataimakin na musamman a harkokin yaɗa labarai na ɗan majalisar Frances Sardaunan. Me Frances ya bayyana cewa jajircewar ɗan majalisar wajan bunƙasa tattalin arziki tare da tallafawa al'ummar mazaɓarsa yasa Sarkin Katsina zai karrama shi da wannan sarauta. Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazabar musawa da matazu a Majilisar wakilai yayi karatun digiri nasa akan…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ziyarci waɗanda ambaliya ta rutsa da su tare da ba su tallafi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Asabar ne gwamanan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kai ziyarar gani-da-ido a yankunan da ambaliya ta afka mu su a ƙaramar hukumar Gummi da ke jihar. Mamakon ruwan sama da aka yi a satin da ya gabata ne yayi sanadiyyar ambaliya a wasu garuruwa na ƙaramar hukumar wacce ta salwantar da gidaje da dama. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnan ya fara ne da ziyaratar Fadar Mai martaba Sarkin Gummi, Mai Shari'a Lawal Hassan inda daga nan sai ya garzaya cikin gari domin jajentawa…
Read More

Kotu ta yi watsi da tuhumar ƴan zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Babbar kotu a Abuja ta yi watsi da ƙarar tuhumar da aka shigar kan masu zanga-zangar matsin rayuwa. Mutane 17 ne suka shigar da ƙarar inda su ke ƙalubalantar zanga-zangar gama gari da aka gabatar wacce kotun ta yi watsi da ita kasancewar ba a gabatar da waɗanda ake tuhuma ba akan lokaci. Mai Shari'a Peter Lifu yayi hukuncin kasancewar masu ƙarar mutum 17 da 26 da ke kare ta ba su bayyana ba a kotun kuma ba tare aikawa da wakilci ba a hukumance. Masu kare ƙarar sun haɗa da; ƴan ƙungiyar 'Take it Back',…
Read More

2023: Buhari bai so Tinubu ba kuma bai yarda da Osinbajo ba – Lamiɗo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya yi iƙirarin cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari bai goyi bayan yunƙurin Shugaba Tinubu ba na son zama shugaban Nijeriya kuma bai yarda da Mataimakinsa, Yemi Osinbajo ba. Ya ce, a madadin haka sai Buhari ya nemi tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan a matsayin wanda zai gaje shi. Lamiɗo yace, Tinubu shi ya ingiza kansa wajen neman shugabancin Nijeriya kuma ya yi nasara ba tare da ubangida ba. Tun kafin lokacin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC, Tinubu ya shelanta cewa, yanzu lokacinsa ne a yayin wani taro…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta sake buɗe iyakoki don harkokin kasuwanci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan Majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Badagry a jihar Legas, Mista Sesi Whingah ya tabbatar wa al'ummar yankinsa cewa nan ba da jimawa ba za a buɗe iyakokin Nijeriya don gudanar da harkokin kasuwanci a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu. A lokacin da ya ke magana a yayin wani taro na masu-ruwa-da-tsaki da matasa na yankin nasa wanda ofishinsa ya shirya, ɗan majalisar ya bayyana cewa buɗe iyakokin wani ɓangare ne na ƙoƙarin haɓaka adadin kuɗin haraji na gida da Nijeriya ke karɓa. Ya ce, tsarin ya na da muhimmanci kuma zai taimaka wajen samar da sakamako…
Read More