Labarai

Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa Sarkin Gobir

Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa Sarkin Gobir

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta yi Allah-wadai da sace-sacen mutane da azabtarwa da kuma kisan gilla da aka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa a ƙaramar Hukumar Sabon Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Bawa. Sakataren ƙungiyar ta MACBAN na ƙasa, Malam Bello Aliyu-Gotomo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Aliyu-Gotomo ya ce, kisan da aka yi wa basaraken ba wai kawai ya tayar da hankali ba ne, illa dai yana nuni da irin ta'asar da masu aikata ta'addancin suka aikata. A cewarsa, babu hujjar ayyukan waɗannan ƙungiyoyin masu kisan kai.…
Read More
Tsofaffi na buƙatar tallafin gaggawa a Nijeriya – NSCC

Tsofaffi na buƙatar tallafin gaggawa a Nijeriya – NSCC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugabar ƙungiyar Kula da Tsofoffi ta ƙasa (NSCC), Dokta Emem Omokaro, ta buƙaci masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa hanyoyin da tsare-tsare don tabbatar da adalci ga tsofaffi ƙasar nan. Omokaro, ta yi wannan kiran a ranar Larabar da ta gabata a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya yi kira da a haɗa kai don tabbatar da adalci ga tsofaffi. Taron masu ruwa da tsaki da aka yi wa laƙabi da ‘Elder Justice’, cibiyar ce ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar kare haƙƙoƙin Dan Adam ta ƙasa da kuma Majalisar bada…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai duba rikicin sayar wa matatun gida ɗanyen mai

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin da zai duba rikicin sayar wa matatun gida ɗanyen mai

Ƙaramin ministan man fetur na ƙasa, Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti da zai duba rikicin siyar da ɗanyen mai ga matatar Ɗangote da sauran matatu na cikin gida. Lokpobiri ya bayyana cewa kwamitin zai duba rashin jituwar da ke afkuwa tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar. Ya umarci kwamitin wadda babban sakataren ma'aikatar ke jagoranta da su kawo rahoton binciken su daga nan zuwa ranar Litinin da Talata. Ministan ya jaddada cewa dole ne masu ruwa da tsaki su tabbatar sun bi dokar mai PIA ta ƙasa da ta shafi siyar da ɗanyen mai…
Read More

Napoli ta cire Osimhen daga cikin ƴan wasanta na Serie A, ta bai wa Lukaku lamba 9

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta cire Victor Osimhen acikin jadawalin ƴan wasanta da ke fafatawa a gasar Serie A ta ƙasar Italiya bayan samun tseko da aka yi a ƙoƙarin ficerwarsa daga ƙungiyar. Ƙungiyoyin Chelsea da Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya ne suka so sayen sa wanda hakan bai yiwu ba sakamakon rufe kasuwar hada-hadar ƴan wasa da aka yi a jiya. Tuni dai Napoli ta sayi ɗan wasa Rumelu Lukaku don ya maye gurbin Osimhen da tunanin zai koma Chelsea. A yanzu haka dai Osimhen na halin tsaka mai wuya sakamakon jefar da shi da…
Read More

Mata ta rasa ranta yayin da ƴaƴanta biyu suka raunata bayan ruftawar ginin a Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani mummunan al'amari ya faru a unguwar Makwarari da ke jihar Kano bayan ruftawar wani ginin sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankin. Al'amarin yayi sanadiyyar mutuwar matar gidan, Balaraba Tijjani mai shekaru 35 yayin da ƴaƴanta guda biyu, Abdulnasir ɗan shekara 11 da Abdallah mai shekaru 13 suka samu raunuka. An fara ruwan ne a ranar Alhamis inda ya cigaba har zuwa safiyar ranar Juma'a wanda hakan ya sabbaba rushewar gidan. Baya ga haka ne maƙofta suka garzaya da su asibiti don ba su kulawa inda a nan ne mahaifiyar ta rasa ran…
Read More

Osimhen ya cigaba da kasancewa ɗan wasan Napoli bayan rufe kasuwar hada-hadar ʼyan wasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yunƙurin ficewa daga Napoli zuwa Chelsea na Victor Osimhen ya samu cikas yayin da aka rufe kasuwar hada-hadar ƴan wasa. Hakan na zuwa ne bayan da ƙungiyoyin biyu suka gaza cimma matsaya game da ɗan wasan. Haka zalika, zuwansa ƙungiyar Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya zai yi wuya bayan da ta sayi Ivan Toni na Brentford a ranar da aka rufe hada-hadar. Don haka, Osimhen zai cigaba da zama a Napoli a halin tsaka mai wuya saboda ƙungiyar ta sayi Rumelu Lukaku inda ta ɗauki lambar ɗan Nijeriyan ta bai wa sabon ɗan wasan. Rahotonni sun bayyana…
Read More

An yi kutse a shafin Hisbar Kano na Facebook, an watsa hotunan batsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu masu datsa a yanar gizo sun datsi shafin facebook na hukumar Hisba ta Kano inda su ke saka ababen da suka shafi batsa wanda hakan ya haifar da cecekuce. Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da faruwa al'amarin inda ya ce su na ƙoƙarin shawo kan matsalar wacce tsawon kwana uku kenan da farawarta. Ya ce, ɓangaren harkar yanar gizo na hukumar na cigaba da ƙoƙari wajen ganin shafin ya dawo aiki yadda aka saba. Ya kuma yi kira ga al'umma su taimaka wajen ganin an samu gyarar ta hanyar aika rahoto…
Read More
Janar Lagbaja ya yi kira a bada kyakkyawan haɗin kai ga gwamnati da hukumomin tsaro

Janar Lagbaja ya yi kira a bada kyakkyawan haɗin kai ga gwamnati da hukumomin tsaro

Shugaban hafsan sojojin Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yi kira ga ƴan ƙasa nagari da su taimaka wajen ganin Nijeriya ta samo tsaro domin zaman lafiya. Yayi wannan kiran ne a yayin rufe taron Hafsan Sojojin Nijeriya na tsakiya da ƙarshen shekara wanda a ka gudanar a babban birnin Jihar Akwa-Ibom, Uyo. Lagbaja ya bayyana cewa rundunar soji na ƙoƙari sosai wajen ganin sun sami haɗaka mai ƙarfi da sauran hukumomin tsaro da ke ƙasar. Taron ya ba kwamandojin yaƙi damar ganawa da junansu domin tattaunawa da kuma bada shawara domin ganin sun inganta yanayin ayyukansu a faɗin ƙasar.
Read More

Ba ki da ƴancin tsare mu – masu zanga-zanga ga G wamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan zanga-zangar tsadar rayuwa da aka tsare sun ƙalubalanci hukuncin da kotu ta bayar na kama su tare da tsare su yayin da suka ce gwamnatin tarayya ba ta da ƴancin yi mu su hakan. Cikin ƙarar da masu zanga-zangar suka shigar, an samu batun da ke ƙalubalantar hukuncin da kotu ta yi a ranar 22 ga watan Agusta ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a, Emeka Nwite wanda ya umarci Sufeton ƴan sanda ya tsare su na kwana 60 har zuwa lokacin kammala bincike akan su. Mutum 49 ne suka shigar da ƙarar a ranar 26 ga watan…
Read More

NUJ reshen Abuja ta jajenta rasuwar ma’aikacin Blueprint

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƴan jarida reshen Abuja, tayi alhinin rashin wani babban ɗan jarida, Mista John Oba wanda ya rasa ransa bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita. Wata takarda da ƙungiyar ta fitar, tace Oba ɗan jarida ne da yayi aiki da gidajen Leadership da Blueprint a lokuta mabanbanta cikin jajircewa da bajinta da ya nuna a harkar aikin jarida. Da dama daga cikin ƴan jarida sun koka game da rashin nasa inda ya kasance abin koyi a gare su. Ƙungiyar ta ce mamaci ya kasance mai ƙoƙari sosai inda ya taka rawar…
Read More