05
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo da kuma gwamnan Jihar Borno sun zo katsina ta'aziyar Marigayiya Dada Musa Yar'adua. Da yake jawabi da iyalan marigayiyar, tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya bayyana rasuwar Hajiya Dada Musa Yar'adua a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya . Yace shi a wajan marigayiyar uwa ce gare shi ganin yadda ya ke da kusanci ga ya'yan ta da tun yana da ƙurucciya su ke tare . Ya ƙara da cewa wani abinda ba zai taɓa mantawa da shi ba shine yadda marigayiya Dada…
