06
Sep
Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Majalisar Zartaswa ta ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Nijeriya ta yanke shawarar rusa tsarin shugabannin ƙungiyar reshen jihar Oyo. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Abuja mai ɗauke da sa hannun shugaban RTEAN na ƙasa Alhaji Musa Muhammed Maitakobi da babban sakataren ƙungiyar na ƙasa Comr. Yusuf Ibrahim Adeniyi. Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Bayan shawarwarin da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar 29 ga watan Agusta, 2024, a hedikwatar hukumar ta ƙasa, muna so mu isar…
