06
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta aika da saƙon gargaɗi ga al'umma kan mamakon ruwan sama da za a fuskanta na tsawon kwanaki biyar masu zuwa waɗanda hakan ka iya haifar da ambaliya a jihohi guda 21. Cibiyar aika Gargaɗin Ambaliya ta Ƙasa ƙarƙashin Ma'aikatar Kula da Muhalli ta bayyana haka a ranar Alhamis inda ta ce ana tsammanin hakan ya kasance daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba. Ta yi hasashen ruwan saman zai iya sa a samu ambaliya a wurare 123 cikin jihohin da aka lissafa. Ta kuma bada shawara ga al'umma da ke garuruwan kusa…
