Labarai

NNPC na iya talaucewa idan har bai ƙara farashin fetur ba – Fadar Shugaban ƙasa

NNPC na iya talaucewa idan har bai ƙara farashin fetur ba – Fadar Shugaban ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan Dabarun Sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ya ce, kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya amince cewa ya na fama da matsalar kuɗi wanda hakan ya sa ba zai iya ci gaba da bayar da tallafin man fetur ba. Mista Onanugu, mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru ga Shugaba Bola Tinubu, ya bayyana hakan a cikin wani saƙon da ya wallafa a ranar Talata a shafin ɗ. Ya ce idan hukumar ta NNPC ta ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin man fetur, kamfanin zai iya shiga…
Read More
Gwamnatin Ogun ta rufe wasu kamfanonin Chana saboda rashin tsafta

Gwamnatin Ogun ta rufe wasu kamfanonin Chana saboda rashin tsafta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Ogun, ta rufe wasu kamfanonin ƙasar Chana guda biyu bisa zarginsu da gudanar da ayyuka a gurɓatattun muhalli da kuma zubar da shara ba bisa ƙa'ida ba. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara na musamman kuma Manajan darakta na OGWAMA, Abayomi Hunye ya fitar a ranar Lahadi. Kamfanonin da abin ya shafa su ne – Yibao Industrial Limited, wanda ke ƙauyen Bara da ke kan titin Sagamu – Abeokuta da kuma Ronchang Industrial Park, ɗaura da farfajiyar Julius Berger, a kan titin Legas zuwa Ibadan. A cewar…
Read More
Ana ci gaba da jimamin rasuwar Wakilin Manhaja na Gombe, Mohammed Ali

Ana ci gaba da jimamin rasuwar Wakilin Manhaja na Gombe, Mohammed Ali

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe Ana ci gaba da jimamin rasuwar Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Gombe, Malam Muhammed Ali, wanda ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya. Marigayin, wanda ya rasu yana da shekara 70 a ranar Talata, 27 ga Agusta, 2024, ya bar matar aure ɗaya da ’ya’ya takwas. Muhammed Ali, tsohon ɗan jarida ne wanda ya shafe tsawon shekarunsa yana aikin jarida. Haifaffen garin Jos ne a jihar Filato, asalin Kanuri daga garin Dikwa a jihar Borno. An haife shi a ranar 10 ga watan Janairu, shekarar 1955. Marigayin ya halarci Makarantar Firamare ta Nur-Ud-Deen…
Read More
Ƙasurgumin ɗan daban da ya addabi Kano ya mutu

Ƙasurgumin ɗan daban da ya addabi Kano ya mutu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar ƙasurgumin ɗan daban nan da ya addabi jihar, Abba Burakita. Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin. Burakita, dai ya yi ƙaurin suna wajen harkar daba, fashi da makami, ƙwace, sara-suka da sauran miyagun laifuka. Kiyawa ya ce “ɗan daban da muka kama, kuma dama muna nemansa a bisa zargin laifukan fashi da makami da jagorantar harkar daba; Abba Burakita, ya rasu,” in ji shi. Idan ba a manta ba Burakita…
Read More
Harin Mafa: Gwamnatin Yobe ta yi jana’izar mutane 34

Harin Mafa: Gwamnatin Yobe ta yi jana’izar mutane 34

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami’an gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Idi Barde-Gubana, sun gudanar da sallar jana’izar mutane 34 da aka kashe a wani hari da wasu ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai ranar Lahadi. Mataimakin gwamnan wanda ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa, ya ce gwamnatin jihar za ta haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya wajen samar da rundunar soji a yankin domin daƙile afkuwar lamarin. Ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta tabbatar da ganin an kula da mutanen da suka rasa matsugunansu da kuma waɗanda suka…
Read More
Shugabar ƙaramar Hukumar Jere a Borno ta yaba da cigaban da Zulum ya kawo a fanni daban-daban

Shugabar ƙaramar Hukumar Jere a Borno ta yaba da cigaban da Zulum ya kawo a fanni daban-daban

Daga GAMBO ISA Shugabar ƙaramar Hukumar Jere ta jihar Borno, Hajiya Inna Galadima, ta yaba wa gwamnan jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, kan ci gaban da yake samarwa a jihar. Da take magana a wata hira da manema labarai, ta zayyana wasu nasarorin da gwamnan ya samu a fannin raya walwalar ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa da dai sauransu. Hajiya Galadima ta zayyano wasu nasarori da suka haɗa da: Bunƙasa ababen more rayuwa da tsare-tsare na jama'a kamar gina gidaje, samar da manyan motoci da tituna a ƙaramar hukumar Jere da kuma cikin ƙananan hukumomi 27…
Read More
Gwamnonin Arewa sun karɓi rahoton tsaro, sun sha alwashin yaƙi da ta’addanci

Gwamnonin Arewa sun karɓi rahoton tsaro, sun sha alwashin yaƙi da ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A wani gagarumin yunƙuri na magance matsalar rashin tsaro da ke addabar Arewacin Nijeriya, Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jaddada damuwar hadin kan gwamnonin yankin na magance matsalar. Gwamna Yahaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar cikakken rahoto daga gamayyar ƙungiyoyin Arewa CNG, wanda kwamitin ƙwararru kan rashin tsaro a arewacin Nijeriya ya shirya. Rahoton dai na ɗaya daga cikin muhimman sakamakon taron da aka kammala kwanan nan a Abuja, da nufin samar da mafita mai ɗorewa kan ƙalubalen tsaro a yankin.…
Read More

Tsadar fetur: Sai an yi haƙuri an jure matakan da muke ɗauka – Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan ƙarin farashin man fetur inda ya gabatar da jawabi wa ƴan Nijeriya alhali ya na ƙasar Chana. Tinubu ya ce hakan da ma wasu gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi na daga cikin salon haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya, ya na mai cewa su na bin hanyoyin da suka dace wajen cimma hakan. Mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya hakaito inda shugaban ƙasar ya ke cewa, "mene ne ɓangaren ƙamarin da zai kai mu wajen, idan ba za mu iya jure wa tsauraran matakan da za su buɗe hanya wa…
Read More

Masu katin ɗan ƙasa kaɗai za a sayar wa buhun shinkafa N40,000 – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce Ma'aikata masu katin shaidar ɗan ƙasa ne kaɗai za su amfana yayin da ta shirya fara sayar da ton 30,000 na shinkafa. Ministan Albarkatun Noma, Abubakar Kyari a lokacin ƙaddamar da tsarin ya ce an yi haka ne don a toshe ƙofar yin ha'inci ga masu saya da kuma taimakawa wajen rage farashin kayan abinci a Nijeriya. Kyari, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya ce kowane ma'aikaci damar sayan buhu ɗaya kadai aka ba shi. Sannan, za a sayer da kowane buhu ɗaya mai nauyin 50kg akan N40,000 kamar yadda aka sanar…
Read More

Yanayin kasuwa ke juya farashin man fetur – NNPCL

Daga BELLO A BABAJI Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce yanayin hada-hadar kasuwar duniya na da tasiri wajen sauye-sauyen farashin man fetur wanda ya na tafiya ne da juyawar kasuwanni kamar yadda dokar masana'antar man fetur, PIA ta tabbatar. Mataimakin shugaban Hukumar Tace Ɗanyen Man fetur na NNPCL, Adedapo Segun ya yi bayanin dalilin ƙarancin man fetur acikin al'umma, ya na mai cewa nan da ƴan kwanaki matsalar za ta kau inda tuni wasu gidajen mai suka fara sayerwa. Ya ce , sakin-layi na 205 na PIA wanda shi ya bada damar samar da NNPCL, ya ce ana…
Read More